AƘIDA TA CHAPTER 9

542 50 5
                                    

_*AƘIDA TA*_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

PART1
Page 9



_Asslam Alaikum warahmatullah_da _fari dai zanyi wata magana_ _tun page ɗin farko nayi bayani_, _nace ina da Jarrabawar ƙarshe_, _ina ƙoƙarin cika Alƙawari ne yasa na cigaba da kawo_ _littafin nan ɗaya ga watan October_ _nace bazan samu yin posting kullum ba_ _amma ina iya ƙoƙarina inga nayi duk dan faranta muku_ _amma wasu na ƙorafi hadda gayamin baƙar magana_ _dan bana posting kullum_ _littafin nan dai nina sa kaina_ _kuma nace free ne balle ace siya akayi nake jan rai_ _babu wanda nayiwa dole seya karanta_ kuma ban karɓi kuɗin kowa ba, _ni nake saka data in ɓata lokacina inyi typing sannan inyi posting_ _dan haka wanda baze iya haƙuri ba ze iya dena karantawa_ ba zanyi _typing kullum ba tunda ba siyarwa nayi be_
_Ni bana Wulaƙanta kowa nasan soyayya ce tasa ake karanta littafina

_
_Masoya har kullum ina sake godiya da Comments ɗinku da Addu'oinku_ _zancigaba da ƙoƙarin faranta muku Insha Allah_






Widad ya hango zaune acan ƙarshen gado kamar Mahaukaciya tuburan, rigar jikin ta iya cinyar ta, gaba ɗaya gashin kanta a hargitse, ta sunkuyar da kanta jikin ta se rawa yake tana kuka, ta rufe ko ina babu haske a ɗakin, seda ya buɗe ɗakin sannan haske ya bayyana a ɗakin.

Babban abunda ya bawa mutan gidan mamaki be wuce yadda akayi Yusuf ya mallaki mukullayen ɗakin Widad ba, alhalin su raɓar ɗakin nata ma basu isa suyi ba, balle samun mukullayen.

Da sauri ya ƙarasa gaban gadon ta yana ambaton Subhanallah,tana ɗagowa taga Yusuf ta gigice ta fara ja da baya tana girgiza kai.

Yusuf yace "Meya sameki haka? Ki kwantar da hankalin ki, Yusuf ne direban ki fa"

Girgiza masa kai tayi tana kuka tace "Ni karka kasheni"

"No ba kashe ki zanyi ba"

Ɗaga kai tayi ta kalli su Alhaji Bulama dake tsaye suna kallon su, riƙo rigar Yusuf tayi kamar zata yagata tace "Suwaye wannan? kace su fita bana son ganin su, kace su fita su bar nan" ta faɗa cikin ɗaga murya da zubda hawaye.

Yusuf ya zauna yace

"Calm down, kinga fa wancan Dad ɗinki ne Alhaji Bulama, ga Mummy, ga Ramlah ga Amal, sune baki gane ba?"

Alhaji Bulama ya tako yazo inda suke, ya miƙa hannu ze riƙo Widad.

Wata irin ƙara ta saki, ta rirrƙe Yusuf tana ɓuya a bayan sa tana girgiza kai, cikin ƙaraji take cewa
"Ni su fita, su fita su bar nan gurin, kasheni za suyi, kana kallo nima zasu kasheni, bana son ganin su ba wannan ne Daddyna ba kuma bashi ne Bulama ba"

Yusuf yace "buɗe ido ki kalle su fa, ga Daddy Bulaman nan s tsaye a gaban ki"

Girgiza kai tayi tace "bashi bane ba, na gaya maka bashi bane"
Ta rungume Yusuf gam tana ci gaba da zubar da Hawaye.

Yusuf a ransa yace "ta tabbata kenan Widad tana da taɓin hankali? In ba haka ba meze sa ta koma haka?"

Alhaji Bulama yace "Karka damu dama tana yin hakan wani lokacin, ciwonta ne ya tashi"

AƘIDA TAWhere stories live. Discover now