Wani Al'amari..

1K 173 15
                                    

*🐂🐂BOROROJI🫀🫀*
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
    Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

Wani Al'amari...

BABI NA TARA.

Muhammad Mamman Muhammad Nasir Aghali. Shine asalin cikakken sunan shi, kasancewar sunan shi sunan babans shi da Kakan shi na Uba, yasa aka mishi lakani da Mohan.
   Duk inda kake niman mutum me tsaye akan ra'ayin shi Mohan ya kai gurin, yana da dadin mu'amala. Ga son mutane da yawan Alkhairi, sai dai mutum ne da bai da fara'a sosai , wani hali da mohan yake dashi wanda ba kowa yake iya zama dashi ba wato murɗaɗɗan hali, duk wanda zai zauna da shi sai tayi mugun hakuri dashi, kafin wannan lamari babu me iya gane abinda yake so sai Abokin shi daya tal a duniya wato.
   Captain Khalil Ibrahim Dan Ba'are, kaf duniya bai da Amini sama da dan Ba'are, bai da abokin arziki irin Dan Ba'are shi yasan Meye Mohan yake so, shi yasan Meye baya so, gashi Allah yayi mishi farin jinin Yan mata, shi kuma baya da lokacin su.

   Sau dayawa Yan mata har kawo kansu suke gurin shi, amma haka bai tab'a burge shi ba, gashi da mugun miskilanci kamar wani Balarabe,  ga wani baiwa da Allah yayi mishi na kwarjini, duk lokacin da zai tsaya a gaban ka baka iya koda motsi. Sannan duk da haka baya cin abincin kowa sai na Dadda kakar shi na gurin Uba. Itace kawai yake cin abincin ta.  Sai na Chef Hurayyah, wata yar Kasar Libya da ya dauko ta domin cika mishi cikin shi da abincinta. Domin ta iya girki sosai, balle shi da mahaifiyar shi ta girma cikin Larabawa.
      Babban matsalar Mohan yana da damuwa amma baya iya gayawa kowa sai Dan Ba'are, TOH shima basu cika zama guri daya na, dan haka yakan zauna yayi ta rubutun shi.

       Kafin faruwan Al'amarin da ya same shi, akan ganshi yana yawan zama shi daya ko kuma yayi ta yawo a gonar shi da yake cikin gidan shi, baya cika magana dama kuma halin shine. Wani lokaci kuma zai fito afujajjan ko wanka yake zai fito yana zare idanun shi, mutum me yawan ibada da tsare hakkin Allah sai gashi an wayi gari baya Kaunar jin kiran Sallah, karshe sai dai ya koma daki ya kwanta, ko kuma a sayo mishi wani abun da zai saka shi barci.
Ranar da ya zama mafi muni a gare shi....
Biki ake tsakanin fadar shugaban kasa zuwa inda ake bikin, ko ina ka leka an cika makil, haka aka gama wannan bikin me cike da farin ciki. Kallon shi dan Ba'are yayi sannan yace mishi.
"Muje na kai ka gida" shiru yayi kamar me tunani. Can ya kalli Khalil Ibrahim Dan Ba'are.
"Kace me?"
Ya fada cikin rashin kuzari,
"Muje na kai ka gida" kurawa Dan Ba'are ido yayi, na wani lokaci kafin ya jinjina kanshi.
"Muje" ya kuma nuna mishi hanya, haka ya shiga cikin motar, a sanyayye. Koda ya shiga motar kallon waje yake,.kamar akwai abin da ya manta. Haka kawai ya fara jin kamar ana harbe harbe,. Duk da ya san karan bindiga haka bai hana shi firgita ba, har yana faɗin.
"Taka motar zasu harbe Ni"
Ya fada da karfi, abin mamaki shi dai Khalil bai ga kowa ba, haka ya tadda motar babu shiri suka bar gurin sai rike kanshi da kunnen shi yake, har suka isa gida.

Aikuwa a lokacin ne yayi karamin hauka, yayi ta fasa duk abinda ya kai hannun shi, haukacewa yayi sosai, koda aka kira likita, daukar shi aka yi zuwa asibiti, da farko yana gane kome yana magana, har yana faɗin zasu nan da bindiga ku bani bindiga na, na harbe su. Haka za ayi ta danneshi ana mishi allura.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now