BABI NA ARAB'IN DA UKKU.

998 227 29
                                    

https://www.wattpad.com/1110873206?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=w9A2MuNtd%2B622l0%2BjIc2ASPfh3Zd6cFPBnC7ssNginYPPoEFUrAQ6F%2BPyB%2FEL3W27mCWwkzGM1DWmbWijxOkDE%2BgKcaqC15YNh%2Bfbe6kK1ewkr6qPiO5FQd5pOlySlZh

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARAB'IN DA UKKU.

Ta bani tausayi. Amma a yadda nake hango tawa rayuwar taya zan fuskanci Mohan? Taya zan fahimtar dashi? Idan na gaya mishi zai yarda dani ko ba zai yarda dani ba? Yanzun na hango abinda Innah take nufi, yanzun na gane dalilin da yasa ta hanani zama a matsayin Mace, yanzun na Fahimci illar da take cikin rayuwar mata.

Ina kallon su kamar masu yanci. Ashe basu da yanci, ina kallon su kamar masu farin ciki ashe kowani dakika na rayuwar su hatsari ne. A haife ka a mace matsala, ka rayu a mace matsala, hawaye ne yake zuba min babu iyaka, dama tana tsoron kar wani mara imani ya min haka ne? Ashe dama can ƙaddara ta a tsare take, dama a shirya min kome nawa daki daki. Daga wannan ƙaddarar sai wata, sai wata.
"Hmm!" Naja wani iska mai zafi, sakamakon isowa wani Mahaukacin gida da zai iya cewa yana bayan gidan Mohan na can Jacader.
"Mommy ko fito" hannunta naji a samar nawa, juyawa nayi na kalle ta, kafin na bude kofar, ina takawa a hankali, sabida har zuwa lokacin gurin bai warke ba, muna shiga babban falon gidan, mutane ne. Yan gaisuwa, ana ganin Dr Zainab, suka rud'e da kuka musamman yan uwan mijinta. Dangin shi, haka ta zauna a cikin su. Zata yi kuka na matse hannunta a hankali ina murzawa. Jinjina min kai tayi alamar tayi shiru.

"Addah muje daki, ki huta" inji Benazir, gyada mata kai nayi. Na bi bayanta muka shiga cikin gidan, dagaske masu ruwa sune da kifi, domin dakin Benazir kamar irin dakin ya'yan Barber's doll ne. Kome na dakin pink da light blue ne, ban daki ta nuna min. Bayan ya shiga ta hada min ruwan wanka, shiga nayi. Na tube kayana. Bayan na zauna cikin ruwan, zafin yana ratsa jikina. Lumshe idanuna nayi ina kara sake ajiyar zuciya, domin dadin da nake ji. Musamman a gabana, domin ji nake kamar an daure ni baki daya.

Sai da na gasa kaina sannan nayi wanka da alola na fito, na samu ta ajiye min doguwar riga, dauka nayi na nufi ban daki, ina sakawa hawaye na zuba min, ina gamawa na fito nayi sallah, kusan kwana uku bana cika barci mai dadi, sai mafarkai. Haka ya tab'a min ciwo na, domin kuwa na fara jin ciwon kai da zazzaɓi, tare da nauyin kirji na. Haka na kwanta tare da kifa kirjina, akan matashin na samu barci mai daɗi.

Kwanakin da suka biyo baya, bani da lafiya sosai, domin sai da aka danganani da asibiti, inda suka maza suka gano Matsalata. Ciwon zuciya ne ya tashi, gashi babu Number wani nawa da ta sani, domin bata bincika jaka na ba.
**
Niamey.
"Yallabai yaran nan kokari kare rayuwarka da ta iyalinka suka yi akan me zasu so kashe ka? WALLAHI daga Khalil har Mohan, babu wanda yake da nufin ya cutar da kai don Allah ka saka a janye batun kashe su da zaka yi don Allah"

Kallon Alkali yayi sannan yace mishi.
"Me nene shaidan ka?"
Laptop din shi ya bude bayan ya kunna mishi daukar da yayi na manyan mutanen da suke jikin shi, take ya gamsu tare da yarda da abinda ya faɗa, lokaci guda ya bada sanarwar ta hanyar mai yaɗa labarai na fadar shugaban jamhuriyar kasar Nijar, akan an wanke su Mohan, sannan kuma an saka duk inda aka samu manyan mutanen nan a kama bayan an sake videon su.

Sannan ya sauke baki daya manyan sojojin kasar, akan za a tura da sunayen wasu. Da za a basu matsayin kuma matasa masu burin kawo cigaba. Sannan ministoci biyu da suka rasu ta jirgin sama za a kaiwa Iyalin su, gaisuwa.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now