BABI NA SITTTIN DA BIYU.

1K 203 26
                                    

https://www.wattpad.com/1115273030?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2FGBnJnXNijQUPspekfVSCvdwVvA67jfZnwBxxbrgfB3mZ707r2j51R%2BtHtXGLFFQhRnwEzTOFYN6wtlFDeefWMBEls9vr15DqQCkIJyDScb3H2il28oON918W3al4mnK
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Ana harin account ɗina fa, musamman wannan account ɗin... Wallahi 😓

BABI NA SITTIN DA BIYU.

Dan haka dole ki koyi mu'amalar irin mutanen wani lokaci ma sa masoyanka kake fada, sai ta kwab'e maka zaka Fahimci haka, sannan da gaske ne dole ki koyi hakuri, domin duk inda zaki zauna dole ki koyi hakurin nan shi yasa Allah madaukakin sarki yace masu hakuri yana tare dasu, dole ki koyi kawar da kai.(🌚🤣wallahi sai ina jin kunya idan na rubuta maganar hakurin nan 🙄domin ban da ita da rashin daraja ce zan iya fada akwai ta buhu buhu 🤨😒😏🌝🤸) mahaifiyar Mohan tana da zafi da fada, kuma irin su dole ka zama ruwan sanyi, sai a zauna lafiya. Bari na gaya miki wani abu, duk yadda aka kai da zaman aure dole ki samu positive and negative, dole cikin biyu ayi daya imma dangin miji su kauna ce ki bawa, umma miji yaki ki. idan aka yi dace kuma kika hada soyayyar dangin miji da namiji kin dace, idan kuma aka yi rashin dace uwar miji taki ki.
(Kuyi hakuri bawai babu Yaren Novel bane a labarin amma ina son ku fahimci wani abu ku mata ne! Kuma dole a gaya muku rayuwar wasu dangin mijin baka san da wanda Allah zai had'a ka dasu ba, amma yana da kyau mu fahimci kan rayuwa ba wai nace babu Sex bane a'a kawai labarin na gina shine akan wannan yanayin 🙄🤨 yan buta roro, idan aka barku da shugaban karamar hukumar wandon cinye shi zaku yi. Wallahi ba sex story bane labari ka fahimci sakon labarin shine damuwar, idan naso sai nayi labarin kamar Kwarkwarah 😂🤣 lami kenan a gaban Uban kowa ma za a karanta labarin babu jin kunya ko rufe fuska 👏🏼)

    Ba wai na gaya miki mugun hali ne ko muguntatta ba, a'a tana da fada amma tana da kirki, kowani dan adam yana da kirki yana da banzan hali, idan Allah yaso halin kirkin ya danne banzan halin ka huta idan kuma halin banzan ya danne na kirki ka banu, domin duk wanda zai fadi wani magana akan ka toh halin banzan zai fada akanka. Ba zai tab'a duba tarin alkhairirronka ba, burin shi ya fadi wancan mugun halin."

Rike hannuna tayi sosai, tare da kallona.
"Jinki Allah ba zai tab'a jarabtarki ba? Ko yayi dake ne ba zai tab'a jarabtar rayuwarki ba? Maimunari idan har namiji zai dauke ni ranar aurena bayan an daura min aure da wani yaje yayi rayuwa dani meye yafi wannan muni da jarabta? Maimunari idan har zai tafi dani bai tab'a mu'amalata ta cikin nutsuwa ba meye yafi haka cin rai?" Damke hannunta nai hawaye na wasan tsare a fuskana,  "kinsan me ya faru? Hatta rayuwar ki nice na lalata miki, domin ba zan manta ba bayan na gama tsine mishi, sai da nayi furucin da nasan shi yake dawainiya dake." Riƙe hannun juna muka yi, kwalla na zuba mana.

    " Nice na jefa ki a ƙaddara, da a lokacin ban ce wani abu nakanki ba da yau rayuwarki bata cikin matsala. Kiyi hakuri da dangin shi da kuma Mahaifiyarshi."
"Mommy ba zan koma gare shi ba, shi daya yayi aure uku bayan Bana nan? Mommy wallahi ina son Mohan, Mommy kinji zuciya tab'a kiji yadda take bugawa, Mommy Mohan wani shashine na rayuwata, amma haka yayi watsi da ni, wallahi ina son shi. Mommy ban san yadda zan gaya miki yadda nake kishin sa ba, shi din mijina ne, Mommy ki min addu'a ko zan sami sauki a zuciyata. Mommy Mohan kamar zinari ne a cikin tsakiyar taku.

   Shi din Kamar ruwa ce min a zafin sahara, kyauta ne da na samu bayan na rasa kome na, Taya ba zanyi kuka ba, amma nagode zan koyi hakuri zan kuma koyi dauke kai, amma Tabbas ba zan iya hakuri a min irin abinda aka miki ba, ba zan iya dauke kai a cutar dani ba, wallahi zan yi magana, kuma idan ka takani zan rama, sai dai idan ba zan iya ba."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now