BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.

947 217 58
                                    

https://www.wattpad.com/1106571155?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MGSTqUwhvG4fBdc8Tqj6OqYqeY7iy%2Bvg8ZVvU9exRM%2FT3GQPgpgjcFkI2rY8w%2BnUMqLJf147FJNMo%2B9%2FQjDN7znC%2BTjtiS3PBxbASme2UWXXFcEf8ltwj%2F4SXO5evwr1
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_Ina ganin Comments din ku da Vote din ku Nagode sosai, amma kuma yadda kuke son wani abun ba zai iya samu ba dole sai anyi hakuri da yadda tafiyar take! Allah yasa kuna fahimta_

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.

Hannun shi dukka biyu ya saka tare da rike Almamoon gam, yana goga mishi hancin shi kan nashi hancin, ganin yadda Almamoon ya rintsa idanun shi yasa shi kara sauke hannun shi zuwa cinyar shi.

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji yayi min tsari da wannan kazamtar." Ta fada tare da toshe bakinta.  Cikin wani irin tsana da kyamar su tace.
"Ku tashi ku bar min gidan mu na tsane ka dama ba son ka nake ba, aka sani dole kuje bana son ganinku." A hankali na mike ina kallonta a raina kuwa dad'i naji tare da kallon yadda take matsar kwallan.

          Mikewa yayi sannan yace mata.
"Lover na ne, yayi miki" kamar wacce zata yi amai ta fara yunkurin amai haka muka bar gurin ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, hannu daya riƙe da waya yana niman dan Ba'are.

"Kai Man har ka gama abinda ya kawo ka?"
"Kasan sarauniyar kyau ce da zan zauna kallonta mun gama kome saura kai da Ammin ku ji da sauarn." Ya fada tare da kashe wayar yana kallon yadda na takura a gefe guda, sai harde hannuna nake baki daya na gama kosawa na koma gida.

    Takowa yayi har gaba na, tare da d'ago kaina.
"Meke damunka?"
"Babu"
"Ka tabbatar?"
"Eh" na fada tare da gyada mishi kai kwalla na zuba min. Fuskar shi ya kai kamar zai sumbaci bakina, nayi baya da kaina.
"Toh meye matsalarka?" Ya tambaye ni a gajiye da abinda nake mishi.
"Don Allah ka mai dani gida na gaji Ni ba makaranta ba ni ba gida b..."

"Baka son zama dani ne?" Cikin wani irin sarewa na zuba mishi idanuna da suka yi jajjur.
"Ba haka nake nufi ba"
"Toh nace ba zan kai ka gida bane? Ko so kake mutane suce na maka wani abu! Kayi min shi kafin raina ya b'aci." Yana rufe baki sai ga Dan Ba'are ya iso a masifance ya bude motar ya shiga,.nima na  shiga.

    Tunda na shiga na had'a kai na da gwiwa ta, sai kuka nake.
"Meye ya same shi?" Inji dan Ba'are,ya tambaya kamar zai tsaya. Banza Mohan yayi mishi kamar baya cikin motar.

  Katse kukan nayi tare da cewa.
"Hammah Khalil zaka mai dani Maradi ko?" Na tambaye shi ina kara sake kuka,
"Eh zan mai da ka." Ya fada min yana kallona ta cikin madubi. Duk da idanun shi a lumshe yake bai hana shi dakawa dan Ba'are tsawa ba.
"Dalla can ka kalli hanya karka ja min magana, ya faɗa tare da gyara zaman shi jikin kujeran. Tare da lumshe idanun shi.

   Haka yayi ta masifa shi daya tare da fadin.
"Wallahi na rantse da Allah idan baka min shiru na sai na ga wanda zai kai ka Maradi" had'iye kukan da nayi kenan ban kuma ko tari ba har muka isa gidan.

     Muna shiga ana kawo mana abuncin daga ɓangaren Hajiya Sahiya. Ina karb'a kitchen na kai na juye abincin. Sannan na fito tare da nufar dakina na hada kayana.

      Kwalla ne ya shiga zuba min, ina had'a kayan. Har na kusan gamawa na ji motsin mutum a bayana, a hankali na mike ban juya ba. Wani irin fitar numfashi na ja, tare da sake kayan hannuna. Kwalla na kara zuba min. Hannun shi dukka biyu da ya sakalo su akan cikina, na kalla. Kwallar da suke zuba ne suka kara yawan fita tare da zuba akan hannun shi, juyar dani yayi yana mai daura kaina kan kirjin shi. Ina jin yadda zuciyar shi take bugawa very faster.

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now