BABI NA SHA BAKWAI

968 166 21
                                    


https://www.wattpad.com/1099611906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=B2xbg56NQ%2Bj7itiadIMLq5S6mXv9S%2FsKyYdkh0H8PJKgwqgLqD%2Fo961ZM5LierkVHLwx3qEwMnG%2BOkvdE6rc9D1tbKk2fSwjLb0oWove1cVKshUkIo7LVOxrft0MhTCk

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....

BABI NA SHA BAKWAI.

    Kwalla ne suka cika min idanuna, na kalli Baba cikin kuka nace mata.
"Amma ko ma yayya ne dole yayi min uzuri, tunda nima mutum ne me rayuwa, taya zai dinga jifana da abinda ya fito bakin shi? Shin wannan adalci ne ko son Zuciya? Baki daya na kasa gane mishi bai da aiki sai gaya min maganar da ta fito bakin shi wallahi ki gaya mishi ya daina ko na kafta mishi rashin mutinci."

Na fada ina share kwallar da sune zubo min,
"Kayi hakuri"

Baki daya malam Ansar yaci uwar rena min hankali, dan yaga bana mishi magana ne wannan karon ya isa haka. Kuma zai ga yadda ake rashin mutunci, sai dai bai gaya min magana ba sai na rama.

Haka na share kwalla na, na cigaba da sauraron Baba, har dare yayi.

    Shigowar Mohan da su Dan Ba'are ya sani mik'ewa zaune ina kallon shi, fuskar shi a sake. Kallona yake kamar me cikakken lafiya.

  Murmushi nayi mishi tare da nuna mishi gurin zama. Kallona yake kamar yana son gano wani abu a tare dani, amma bai ce min kome ba, tunda ba magana ce yake ba. Sauka nayi tare da nufar shi na kawo shi bakin gadon ya zauna, zama nayi a kusa dashi ina me kallon kayan ciye ciyen da yake dakin na shiga mika mishi ina cewa.
"Ci karka damu Ayya naga ka rame da ba nan Anya Hammah Khalil kana kula dashi kuwa?" Wani kallon banza ya watsa mishi tare da cewa.
"Ba aiki Mohan ya dauke ni ba, dan haka dan banza idan ya dagama yaci abinci idan bai gadama ba ya zauna da yunwa banza dan iska Allah ya baka lafiya kace zaka fito da halin ka cin mutuncin ka zanyi"

        Kallon shi nayi cikin kankace idanu nace mishi.
"Wannan cin mutuncin da me yayi kama? Ka saka mara lafiya a gaba da wulakancin meye yayi maka"

         Sake hararan shi dan Ba'are yayi yana me dauke kai tare da gyara tsayuwar shi.

   Abinda ya faru kuwa ba kome bane, tun suna yara suka da wata muguwar wasa da sukewa junan su, idan mutum ya duka, dai ka sake mishi dundu a baya, shine bayan ya koma gida yana ƙoƙarin su tawo asibitin, kawai Mohan ya ganshi ya duka yana saka takalmin shi ya samu gadon bayan shi ya sakar mishi dundu sai da ya kwara amai. Kuma da ya juya ya saka fuska kamar bashi ba, shine abun yake bashi haushi yake ta zagin shi tun a mota, ya kwashe mishi albarka yakai sau dari tare da jan Allah ya isa kamar zai fasa ihu, domin dai da yaji bayan ya kame kafin ya mike tsaye kai Mohan..kwafa yayi ya kuma ce mishi.
"Dan iska mugun banxa kawai"

       "Amma ba na hana ka zagin nan ba?" Kallona yayi sannan yace min.
"Mamoon dundu yayi min a baya fa" .kamar zai fashe da kuka.
Kallon Hammah Mohan nayi,
"Me yasa kayi mishi haka? Kana son ka zama mugu ne dodo me ban tsoro?" Na mishi wani iri da hannuna ina gwalallo idanuna waje. Girgiza min kai yayi tare da kwantar da kanshi yana jin babu dad'i.
"Toh karka kuma kaji" na fada mishi ina kallon Hammah Khalil ina me Cigaba da bashi hakuri.
"Kayi hakuri"
"Shi kanan nazo na zauna kusa da kai?"
Matsa mishi nayi Baba bata ce min kome ba, sai bayan da suka gama suka fita, sannan tace min.
"Karka kuma haka babu kyau"

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now