BABI NA ARAB'IN

1K 231 27
                                    

https://www.wattpad.com/1110255281?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DdYNxkS6yN8uhfrR37h62zbfOjOm1OLDDCckdNme%2BKjEwnbGDu4mL6048YMV1h%2B07%2FeXZoIeF7Jb4dl3nS6A6LUJkIqi7ROIE9bf%2BgkMcMKV8M17P9CSRPPYeYAU9QZF

🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

BABI NA ARBA'IN.

Tsayawa nayi a gaban shi, cikin takaici ina kallon shi, zuba min ido yayi, kafin yace min.
"Ba zan miki dole ba, amma kuma yana da kyau ki fahimci suwaye a tare dake, su waye suke son amfani dake, tashi muje gida."

  Ya fada min, kasa mishi musu nayi ma mike, ashe haka ya b'atawa Malam Ansar rai yace min.
"Nagode"  juyawa nake son shi yi, amma abun mamaki Mohan ya hanani, muna fitowa ya saka ni a motar shi. Muka bar  gidan cin abincin kamar zanyi kuka haka nake bin shi.

    Baya tafiyar shi, Malam Ansar ta juya zai ya hadu da Alkali, cike da mamaki ya kalle shi. Sannan ya kasa magana, har ya fita yana kara juyawa yana duba alkali.

   *Taya mutumin nan yake kuma da Munnah?  Kamar ta B'aci sosai* shi daya yake zancen zuci, har ya shiga motar shi, wayar shi ya saka a kunne, yana me cewa.
"Yaki amsa sabida ya san zai fadi, dan haka duk rintsi ka dauko min ita idan ka sami damar haka, idan ka sake kuma na dauke ta, tabbas zan tafi da ita ne duk inda yayi min."

     Wani murmushi yayi tare da cewa.
"Kwantar da hankalinka, yanzun zaka ji ruwa mai yawa, zan baka abinda baka zata ba, yanzun zan koma diffa, idan na dawo zan kira ka."

    Kashe wayar yayi tare da sake wani murmushin gefen baki yana faɗin.
"Hmm! Ta kare maka Mohan" ya faɗa yana murmushin mugunta, a hankali ya tadda motar,tare da barin Niamey.

   Abincin ya saya tare da biyan kudin, sannan ya nufi gurin da su Mohan suka tsaya, ganin wayar Maimunari yasa shi dauka, hotonta ne a kai lokacin tana Almamoon, kura mata ido yayi zuciyar shi tana bugawa, da sauri ya kashe wayar baki daya. Abincin da bai ci ba kenan, haka kawai zuciyar shi take raya mishi wani abu akan Yarinyar,duk da ya lura bata da kwaranniya irinta sauran matan, gaskiya da ban mamaki yanayin su da yake gani a tare, abu daya da yake kara fisgan shi a kanta, kafewarta akan abu. Bayan haka baya jin akwai wani abin da ya ke yanayi daya da nashi, sai fuskar shi da kuma yana yin fatar su, sai dai tafi shi washewa kaɗan, kasancewar shi mai duhun fata sosai. Lumshe idanun shi yayi.

A da baya tunanin haka sai da wani abokin shi alkali daga tahua yazo da ya ga Maimunari ne yayi ta mamaki.
"Wodaadabe wannan yarinyar yar ka ce?" Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Eh toh kasan ban da iyali dai? Aiki ya kawo ta nan bayan nan kuma gaskiya babu wani abinda ya had'a mu sai dai ina jin ta kamar wacce ta fito jikina" ya faɗa yana murmushin jin dadi. Yau an had'a shi da d'a shi da yayi kuskuren tafiya ya bar baya da kura.

  Bayan abokin shi ya tafi ya tuna sakon da ya barwa yar uwan shi.
_Ban sani ba ko meye muka haifa! Ba zan iya duba shi ba, don Allah ku rike shi da amana, idan namiji ne ku bashi ilimin addinin musulunci, idan mace ce don Allah ki tayani boye sirrinta, dan kar hakkin mutane ya tambaye ni akanta na had'a ku da Allah."

         Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude sunyi jajjur har da ruwa sun cika.
"Ina namiji ta haifa, kuma tarihin shi zai rufe,mace kuwa tabbas soyayya zai bude tarihin ta, kuma de ƙaddara zata ratsa tsakanin. Allah kasa namiji ne. Allah kasa kar ya gado mugun halina, ya Allah kasa kar ya dauki halin da na jefa wasu iyayen."

BOROROJI....The Journey of Destiny!!!Where stories live. Discover now