NA TAKO PAGE 1

193 15 6
                                    

✨✨✨  *NA*
         *TAKO*✨✨✨
                    

                              

                 ✍️

           *AISHA GALADIMA*


               1️⃣



Dandazon mutane ne suke ta bullowa ta kowace kofa suna shiga cikin masalaci wasu Kuma suna tsayawa ne a harabar masalaci , kowa ka gani fuskarsa cike da annuri ba manya ba, ba yara ba
Kowa na cikin walwalarsa da annashuwa , cikin sabon Kaya  se walwali suke ko
ba'a fada ba Kai tsaye zaka iya tabbatar da wannan taron  idi ne
A can dayar hanyar shigowa kuwa wata kyakyawa yarinyace  fara tsaye tare da wata tsohuwar da taci Riga da zaninta hade da wani gilashinta afuska Wanda alamu sun nuna na kara karfin gani ne tayi tsaye Tana kallon yarinyar Tana cewa "Kinga mairo ki wuce nace Miki mu shiga cikin masalaci Mana Dan  bazan tsaya harabar  masalaci yin sallah ba wallahi ni da nasan haka Zaki min da ban matsawa sa'adatu cewar ta barki ki shirya da wuri ba dake zan tafo ,na manta da bakar kafiyarki " ta Kare maganar tare da hararar mairo ta cikin gilashinta da ke fuskarta
Yarinyar kuwa kallon tsofuwar take ranta na Kara tafarfasa kamar ta tafi ta barta a wurin take ji ammah tasan hakan bazata yiyu gare ta ba ,komi ta tuno Kuma se ta saki fuskarta tare da murmushi  ta ce " Kinga kakus nifa bacewa nayi ba zamu shiga cikin masalaci ba ammah bakiga yanzu mutane suke zuwa ba saura kusan sa'a Daya fa ayi sallar kinsan se an jira zuwan sarki da Kuma governor kafin ayi sallar Nan ,Kuma Baki son karbar sadakar kudin idan kika shiga cikin masalaci ta Yaya wani ze Baki sadakar"
Marmar ta yi da ido ta washe bakin ta irin na tsofi Tana murmushi tace "Kai shiyasa nake matukar son ki mairo duk kinfi sauran Yan uwanki  hankali wallahi kamar kinsan shiga cikin masalacin ma da nake son nayi Dan na karbo sadakar da sarki da gwamna ke bayarwa ne ammah tunda Basu zo ba da sauran lokaci bari na fara Zama anan harabar na karbi ta hannun mutane tukunna"
Shimfida sabuwar daddumar dake hannunta tayi tace "to kakus zauna Mana ,sannan Dan Allah kibar kirana mairo sunana Maryam ne ba mairo ba , tana kallon yadda tsohuwar ke hararar ta  ta gaefen ido ,sanin hali yafi sanin kama yasa da sauri Maryam ta juya ta saki murmushin me kyau tace "kakata ta kaina"  washe Baki kaka tayi kawai ta gyara zamanta ba tare da ta Kuma bi ta kan Maryam ba
Tana ta kalle kallen mutane dake ta shigowa cikin masalaci
Ita Kam Maryam kakus take ta kallo a ranta Tana mamakin son kudi irin na wannan matar duk da dama su din talakawa ne ammah mahaifinta na iya kokarinsa a kansu ammah Sam ita kakar tasu ba taki ba ma an barta taje bara ba ko a hanya ne
Karar lasifika ne ya dawo da Maryam hayyacinta tare Kuma da zaburar da kakus tayi ta Mike tsaye
"Kinga tashi mairo tashi mu shiga cikin masalacin Nan kafin a tayar da sallar nan "
"An ma tayar ki tsaya kawai muyi anan Mana"
cewar maryam
Kare maganar ta keda wuya akace "Allahu Akbar"
Maryam tada sallarta tayi ta bar kakus da ke ta fitar da ido waje kamar ta saki kuka tsabar takaicin Maryam tafiya ta fara yi kanta tsaye Tana bi ta gaban mutane dake sallah ko a jikinta
Maryam kinbi ta kanta tayi taci gaba da sallah ta
Kakus Kam ta cikin mutane taci gaba da kutsawa har se da ta dangana da masalaci se dai tab yake Babu wurin tsayawarta
Tana Nan tsaye Tana rabon idanu har aka Kare sallar  nanfa mutane suka fara fitowa daga cikin masalaci kakus gefe ta koma ammah duk da haka yadda mutane sukai yawan Nan dole se anyi matso matso ake wucewa
Nanfa wasu security sanye da kakin soja da 'yan sanda suka fara fitowa daga masalacin ,  nanfa kakus ta fara ja da baya  se dai ganin tayi kamar suna Kara kusantota numfashinta taji ya fara daukewa tayi baya kawai zata zube kasa
Wani kyakyawan dogon hannu ne fari tas ya tare kakus
Take securities suka zagaye su dago kansa yayi ya kalli security daya da sauri ya juya ya nufi wata bakar Jeep ya bude ya dauko gorar swan Daya dake gefen marfin motar ya dawo da sasarfa ya iso inda suke ya bude gorar ya mikawa ogan nasu
Karba yayi ya bude ya zuba ruwan kadan a hanunsa ya shafa a fuskar kakus, wata irin ajiyar zuciya ta sauke  ta fara bude idanunta ganin ta bude idanun nata ammah se Kara waro su waje take ya tuna da glass dinta dake dayan hanunsa a rike tada ita yayi Daga jikinsa ta zauna a dai dai sannan ya saka Mata glass din a idanunta  kallonsu ta fara yi daya bayan Daya sannnan ta sauke idanunta ga mutumin dake durkushe a gabanta se dai shima bazata iya cewa ga fuskarsa ba kasancewar ya saka facemask a fuskarsa se dai shi shadda ce a jikinsa fara tas sauran Kuma kaki
Baki na rawa tace "Dan Allah dannan kumin rai wallahi ban aikata laifin komai ba " Tana kokarin yin kuka
Gano abun da yasa ta firgita yasa ya juyo ya kalli securities din da sauri suka koma gefe daga zagayen da suka musu se dai basuyi nisa ba
Juyowa yayi ya kalli  kakus kafin a hankali yace " mama tashi please Babu abunda zasu Miki ai dama bakiyi laifin komai ba"
Dan kallon sa kakus  tayi jin hausar tasa kamar Dan koyo
Tace "to shi place din fa hardashi"
Dan murmushi ya saki Wanda idan baka kura Masa ido ba bazaka San yayi ba ma yace "Dan Allah tashi mama Kinga mutane duk sun tafi fa tashi mu Kai ki gida a wane unguwa kike"
A hankali kakus ta Mike Tana gyara mayafinta hannunsa yasa ya rike hannun kakus suka fara takawa a hankali har suka isa wurin mota har an bude mota kakus taja ta yi tsaye
Tace" bafa Ni daya nazo ba Dani da mairo ne ko a 'ina ta tsaya ita Kuma" Ta Kare maganar Tana kame Baki
Waige waige ta fara tace "lah ka ganta can bature" .....................


Aysha galadima ce✍️..................

Vote
Comment
Share

NA TAKOWhere stories live. Discover now