PAGE 15-16

56 7 1
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

                 ✍️
       *AISHA GALADIMA*

'''Follow me on wattpad@ Ayshagaladima666
'''


1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣

______________________________
Ganin ya Mata wani kallo A daburce tace "Yaya Abbie barka da safiya" barka yace Mata kamar an Masa Dole rabewa tayi Maryam da sauri tabi Bayan nata ta rabe itama wuce warsa yayi ,Maryam da kanta ke kasa ko A batace ba sanyi taji jikinta ya dauka tun daga tafin kafarta har zuwa kirjinta gabanta ne ya Fadi ,tare da shakar daddan kamshin turaren sa ,giftawarsa yayi duk da ba Wai ya kalle ta bane kasancewar kan nata na kasa ma gefen fuskarta da gashin da ya  kwanta Mata shi kadai ya gani ta gefen idonsa , har ya fara tafiya wata zuciyar tace Masa wace waccan da bazata gaida  sa ba hoton gefen fuskarta ya Kara fado Masa arai tsaki yayi ya ci gaba da tafiyarsa ,Ganin Rahama ta shige yasa ta bi bayanta Da sallama a bakinta ta shigo kyakyawar dattijuwar dake zaune ta Amsa Mata fuskarta dauke da murmushi ,bilkisu dake rungume da Rahama na murnar ganinta ta saketa Tana kallon Maryam ,takowa Maryam din tayi ta Dan risinna Tana gaida hajjo ,cike da kulawa take karba Mata tare da yaba tarbiyar Maryam din a ranta tare da cewa"Tashi Mana 'yarnan ki zauna saman kujera" Maryam da kwarjinin hajjo ya cika Mata ido ta tashi ta Dan zauna kan kujerar a darare , ganin kallon da Bilkisu kema Maryam yasa tace "yawwa ga kawata da nake fada Miki Maryam sunanta " cewar Rahama murmushinta me Kara Mata kyau tayi kafin tace "sannu Maryam, ammah Rahama zan Miki kwace Dan Nima zamu fara kawancen ne" kusan su ukun kowa se da ya murmusa jin karfin Hali irin na bilkisun " naji ni dai in dai Maryam ce nasan miskilancinta kawai ze hadaku Dan ba magana ta cika yi ba " cewar Rahama , "duk miskilancinta takai Yaya Abie ne?"  Cewar bilkisun ,  hajjo dai na gefe Tana Jan casbinta se karema Maryam din kallo take a kaikaice jin musun nasu ze yi yawa yasa tace "me gado Wai haka zaku bar bakuwar taku ko ruwa se surutu kuke zubawa in ba ke ba Rahamu na rasa wayafi surutun a cikinku " mi bilkisu zatayi kuwa banda dariya ,itako Rahama cinno bakin ta tayi jin yadda Hajjo ta Kira sunanta , Riko hannun Maryam bilkisu tayi tare da cewa "ku tashi muje dakina in ba haka ba hajjo baza ta barmu mu tattauna ba" har sun nufi dakin Rahama ta dawo tace "yawwa Hajjo asa wasu su shigo da Kaya driver na Nan awaje Yana jira" da sauri ta wuce gudun korafin hajjo "Zaki gudun man ja'ira dama tare kuke da Kaya kika bar bawon Allah a waje kika zo Kuna surutun"cewar hajjo ,wayar ta ta dauka tare da bayar da umurnin a shigo da kayan ,suna shiga dakin akan gado Rahama da Bilkisu suka yada zango ,Maryam kujerar madubi  ta jawo ta zauna ,wayar ta ta dauka tare da bada umurnin akawo musu abun tabawa, ba jimawa kuwa aka kawo kayan ,ba yadda Rahama ba Tai da Maryam ba Akan suci ki tayi lemun kawai Tasha tace ta koshi har bilkisu se da tasa baki fafur tace ta koshi, bilkisu kam aranta Tana jinjina yanga da kuma ajin Maryam din take taji ta Kara burgeta, labarin bikin suka shiga yi da dinner din da za'ayi da daddare ," Wai Ni Kam ba masu lalle ne a garin Nan me kyau"? Cewar bilkisu,Rahama tace akwai Mana bari na Kira wata tazo ta Maki anan  tare da Maryam Dan Ranar da zanje Bata jin Dadi shiyasa batayi ba ok kawai tace da ita ,take ko ta kirata se gata tazo Jan lalle bilkisun tace Tana so ,shi aka shiga yarfa Mata ba karamin kyau yayi a farar kafarta ba se  yabawa  daga Rahama har me lallen keyi juyawa tayi ta kalli Maryam Dake murmushi tace "Wai da gaske Maryam yayi kyau ba fasa min Kai su Rahama keyi ba ?"  "Gaskiya yayi kyau sosai musamman a kafarki" cewar Maryam murmushi tayi cike da jin dadin yabon da Maryam tayi, haka kawai take jin Tana son Maryam din duk da zasu yi kusan sa'annin juna , Bayan an gama Mata aka fara ma Maryam din har tace a Mata Baki, bilkisu tace amata ja irin nata Wai ummeen su tafi son ja, ita dai Maryam murmushi kawai tayi Tana jinjina karfin halin bilkisu ,ita miye hadinta da su da har zata yi abunda suke so ammah ta kula kamar shagwaba ce tayi ma bilkisun yawa ko Kuma duk jin dadin da take ciki ne yasa haka ohho, ana gama na Maryam suka shiga yabon nata Dan shima yayi kyau ba karya, "kina da bank account ki ban account number dinki na Miki transfer kudin" cewar bilkisu eh me lallen tace Mata tare da karanto Mata account number din a take alert ya shiga wayar me lallen ,ai zubewa yarinyar tayi Tana kwararowa bilkisu godiya"nagode nagode hajiya bilkisu Allah ya Kara Miki lafiya Allah ya Kara mayar wa Abbah kujerar sa ta shugaban kasa  ya Baki miji na gari" da katar da ita bilkisun tayi ganin godiyar ba me karewa bace tare da cewa"Amin nagode Zaki iya tafiya " sallama ta musu tare da ficewa ,kallon Rahama tayi tare da cewa"Rahama 50k fa ne na Bata kamar wadda na biyawa aikin hajji shine take wanna godiyar" dariya Rahama tayi kafin tace " ai Dole tayi godiya bana tunanin an taba Bata Koda 20k ne a lalle ballantana har 50k Kinga ko Dole ta Miki godiya ,shiya sa ma na Kirata saboda ta iya aikinta " Tafa iya gaskiya Dan yayi kyau cewar bilkisun, ita dai Maryam tunda suka fara zancen kudin ta shiga mamaki ,se dayan mamakinta na jin cewa bilkisu 'yar shugaban kasa ce , ammah duk da haka  wannan zanen lallen be Kai matsayin 50k ba a ganinta almubazzaranci ne irin na masu dashi ne kawai ,talakawa nawa ne suke cikin halin kaka nikayi a kasarnan , Rahama ce ta yanke tunaninta tare da cewa "ki tashi ki je toilet ki wanke yayi fa " tashi tayi ganin dakin wayam bilkisu ta fice tun dazu  taje ta wanke din , " Allah Maryam Kinga yadda lallen Nan ya Miki kyau kuwa kamar Rani Mukherjee " cewar Rahama,harararta Maryam tayi tare da cewa "ki ci gaba da zolayata Rahama ,yawwa Rahama Ni Kam ya kuke da bilkisun Nan ?"  kallonta Rahama tayi kafin tace "'yar uncle Dina ce babban yayan su mommy Kuma shine matsayin shugaban kasar Nan a yanzu" jinjina kai Maryam tayi cike da gamsu da bayanin nata , bilkisun ce ta sake shigowa tare da cewa " ku fito muyi lunch hajjo na falo Tana jiranmu, na Riga na Mana booking din me makeup anan zata zo ta Mana " fitowa sukayi Baki dayansu
________________________

tunda ya fito Yana part dinsa kwance Yana barcinsa Kiran da munir ya dame sa da shi ne ya farkar da shi daga wayar yayi yasa a kunnensa kafin yace komai a dayan bangaren munir yace"Habah Turaki Ina ka shiga Ina ta Kiran wayarka baka daga ba "? Numfashi ya sauke a hankali ya ce "Ina bacci" munir be yi mamakin jin abunda yace ba  cewa yayi "ok dama bakinka ne suka iso na sauke su a Nan gidanmu yanzu haka suna part Dina se tambayar ka  suke"  tashi yayi akan gadon da kyau sannan yace "ok ka basu hakuri yanzu Dana shirya gani Nan tafe" ok yace tare da yanke wayar, ahankali ya zuro kafafunsa kasa tare da nufar toilet Kai tsaye after 10 minutes se gashi ya fito ,shiryawa yayi cikin wani tsadadden voile milk colour dinkin bame tazarce bane irin dinkin da gayun zamani ne ke yayi me guntuwar Riga  ,manyan turarukkansa ya dauka ya feffesa take kamshin dakin ya sauya ,cike da kasaitarsa ya fito daga part din nashi da sauri securities dinsa suka taso gai dasa sukayi tare da bude Masa mota ya shiga se da suka hau kan titi sannan ya fada ma driver inda suka nufa , ba jimawa suka iso gidansu munir a harabar gidan ya tarar dasu suna ta Arwala sallar la'asar shima yi yayi suka shiga masalacin dake cikin gidan sukayi sallar bayan fitowar su Nan yashiga gaisawa da friends din nasa da suka zo,ciki suka Kara komawa suka zazzauna ,Nan fa aka shiga zolayar munir ango can wani daga cikin friends din nasa me suna Auwal yakasai yace"Turaki yaushe zamu zo naka bikin ?" Shiru duk sukayi dakin yayi tsit dagowa yayi ya kalle su ganin kowa ya zuba Masa ido yace"soon Insha'Allah" sowa suka fara yi Dan lokutta da dama duk wani ya Masa tambaya irin haka cewa yake ba yanzu ba ,shi dai shiru yayi har sukayi su ka gama sanin ba magana ta dame sa ba yasa suka ci gaba da hirarsu da ango munir ,wayarshi ce tayi Kara ganin me Kiran nasa yasa shi dagawa tare da sallama amsashi tayi sannan yace "ummee barka da yamma ko har kun iso?" Eh tace dashi cewa yayi "ok gani Nan zuwa Ina tare da su munir ne " sallama sukayi ya yanke wayar ,Bayan ya gama kallon su yayi tare da cewa" kumin Afuwa Sadiq my Ummee tazo zanje mu gaisa na dawo ga amanar Angon Nan na Baku ku shirya min shi yadda ya kamata akwai kayan da nazo dasu zan sa a shigo da su ,su ze saka Kar ku bari yayi garaje fa" ya kare maganar Yana wata siririyar dariya ,duk dariya sauran sukayi munir ma yayi dariyar sannan yace "ai Ni ba wani garaje da zanyi malam  Dan bazan bari ma wani ya shiryani ba Ni zan shirya kaina,in sukayi delay wurin nasu Shirin se dai su tarar Dani  hall din Dan ba zan shanya sweetie na ba " me zasuyi kuwa banda wata dariyar Turaki mikewa yayi tare da cewa"to Rasa kunya nasan zaka iya ai " ficewarsa yayi Bayan sun gama sallama kamar Koda yaushe masu tsaron nashi na waje na jiransa dayansu ya ummurta da ya shiga da kayan dake booth din sa  babban akwati ne Koda ya fito shiga motoci suka yi suka tafi,munir Koda ya bude akwatin shiru yayi Yana kallon kayan ,manyan shadodi ne da yadidika turakin ya dinka Masa se wata bag dake gefe Koda ya bude wasu hadaddin wedding set ne for the couple  suit ne hade da  wedding gown sun hadu karshen haduwa sky blue "wadannan kayan zaku saka Kai da madam a wurin dinner fa" cewar Sadiq dake gefe suna kallon kayan ,ok yace tare da fitar da natan ya bayar akai Mata , aransa tunani yake shi Kam wane irin so ne Turaki ke Masa haka kusan komai ya taso na auren Nan shi yake rigansa yinsa ,Allah ya saka Masa da Alkhairi ya bashi Mata tagari da zata kula da abokin nasa , Addu'ar da ya Masa kenan a ransa  Ganin maghrib ta yi yasa suka yi sallah suna dawowa aka shiga hada Angon

Koda ya iso gidan A part din hajjo ya tarar da ummee suna zaune suna firarsu ,da sallama ya shiga tare da Zama a gefen ummee ya gaidata sannan ya juya kan hajjo cewa tayi "yanzu ka tuna Dani Bayan ka gama gaida gyatumar taka" Dan Sosa Kai yayi yace "Habah hajjota Afuwan mi kika aje min am starving " Kai kasan wani starb ai " cewar ta murmushi yayi yace "yunwa nake jifa" share shi tayi can kuma ta fara Kiran Mai gado!!! Se gata ta fito ,dama tunda ummee tazo suka fito suka gaidata suka koma Dan har make-u p artist din tazo, da murmushi ta karaso tare da rissina wa tace "Yaya Abie sannu da zuwa" yawwa yace Mata Yana murmushi shima kallon yatsunta yayi ganin tayi Jan lalle ,Jan lalle na burgeshi dama can musamman idan ummee tayi ,hajjo ce tace "ki dauko Abincin yayanki da kika zuba dazu kikace nashi  ne " tashi tayi ta nufi dinning foodflask din ta dauko tare da plate,spoon da Juice ta hado a gabansa ta aje tare da serving din sa ,tuwo ne miyar ganye da manshanu ,spoon ya dauka ya fara ci a hankali , "yawwa ummee bari na koma ciki kwalliyar za'a Mana har an farawa Rahama " cewar bilkisu ,to ummee tace Mata ta juya ,Koda ta koma har angamawa Rahama ta farawa Maryam ,jakar kayansu da Rahama tazo dasu ta bude ta fara fiddawa kowa nasa Dan har bilkisu akayi dinkin ,wow Bilkisu tace ganin kyawun da Rahamar tayi cikin ma ba'a nada mata head ba tunda Bata sa kayan ba ,nata ta dauka taba bilkisu nata ,duk sakawa sukayi kayan Masha'Allah sun zauna dab a jikinsu dama fitted gown ce,ana gamawa Maryam itama ta saka natan se da ta gama masu make up din Baki Daya sannan ta nada masu head din ,kyawon da sukayi baze misiltu ba, daukar su different pictures ta shiga yi ,Maryam ba'a karamin takure take jinta ba a cikin gown din Dan ta dameta sosai ,kasa shiru tayi ta ce "Ammah zamu saka mayafi ko?" Daga Rahamar har bilkisu kallon ta suke yi cike da mamaki ................✍️

*Aysha galadima ce*

*Novel dinnan na kudi ne*@300 Naira  *via 3118088470*
*Aisha Muhammad galadima first bank ko katin MTN to 08064933819*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 22, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NA TAKOWhere stories live. Discover now