PAGE 11-12

32 5 2
                                    

💐 *NA*
*TAKO* 💐

👠

✍️
*AISHA GALADIMA*


'''Follow me on wattpad @Aysha galadima 666'''

'''The only one who will never fail you is Allah'''

1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

________________________________

karar Marin ba karamin girgiza Rahama yayi ba,shima kansa TJ Marin yazo Masa ne unexpected,saboda a cikin kiftawar ido da rike hannun nata yaji saukar Marin ,fizge hannunta tayi tare da ja baya ta tsaya ta fuskance sa , shikam TJ cike da mamaki yake rike da kuncinsa Yana kallonta "Ina so wannan ya Zama lokaci na karshe da zaka yi tunanin hada wanna hannun naka da nawa saboda Ni ba irin Matan da kake tunani ba ce "! Cewar Maryam da har fatar fuskarta tayi ja tsabar bacin Rai ,ba TJ da take kartawa worning din ba hatta Rahama Tunani take a ranta dama Maryam ta iya masifa har haka, ,fizgar hannunta da Maryam tayi da nufin barin wurin ya dawo da ita hayyacinta sedai taku Daya suka yi yaran TJ suka zagaye su suna muzurai se dai basu taba su ba TJ dinne ya tako ya shiga tsakiya Inda su Maryam suke "Baki ji ba" cewar TJ juyowa sukayi suna kallonshi, ba karamin kaduwa zuciyar Maryam tayi ba ganin yadda idonsa ya kada yayi ja a lokaci Daya ba,Rahama Kam har hannunta ke rawa "ke har kin Kai matsayin da zaki daga hannu ki maran saboda na rike hannunki? Shiru Maryam tayi batace komai ba se gabanta da ke faduwa ganin ya Kara kusantowa gabanta, To Ina Miki albishir da kin tabka babban kuskuren da Zaki mutu kina dana sanin shi ,se kin yi nadamar wannan Marin " Yana gama fadar haka ya juya tare da dagawa yaran nasa hannu suka bi bayansa suna masu bin su Maryam da wani mugun kallo kamar zasu cinyesu , kutt Maryam ta hade miyon da ta kasa hadewa tun fara maganarsa ,Ganin sun wuce yasa Rahama Kara damkar hannun Maryam suka nufi gidansu ,ba Wanda yace wani Abu har suka shiga gidan babban gida ne gidansu Rahama base an fada ba tunda ga farkon gidan har cikinsa gidane irin na masu hannu da shuni ,suna shiga ba kowa falon gidan Kai tsaye dakinta ta nufa da Maryam suna shiga ta mayar da kofar dakin ta rufe kafin ta kalli Maryam tace "Maryam kin San abunda kika aikata kuwa ?, Katon mutum kamar TJ Dan tasha ! Dan daba kika daga hannu kika mara a tsakar ranar Nan" Maryam dai se Kara zare idanunta tayi Tana kallon Rahama yanzu wani tsoro ya mamaye ruhinta da zuciyarta " Baki yi tunanin abunda kanje ya dawo ba " cewar Rahama ,kwallar da ta tare ita ce ta sauko a kuncinta kafin tace "habah Rahama ya kike son nayi bakiga abunda yamin bane shi?" Ganin kukan da Maryam din ta fara yasa Rahama sauke numfashi sannan ta ja hannun Maryam din suka zauna a bakin gado, tace "na gani Maryam be kyauta ba ammah fa TJ fa Maryam Dan tasha ne mutumin Nan ke da bakinki ki ka fada min haka,yanzu dai aikin gama ya Riga ya gama se dai karki Kara daga hannu ki Mari namiji kinji ko " daga Kai Maryam tayi, tashi tayi ta fita lemu da snacks ta dauko ta dawo ,da kanta ta tsiyaya lemun a cup ta mikawa Maryam ba musu kuwa ta karba Sha tayi kafin ta aje cup din tare da sauke a jiyar zuciya , kallonta Rahama tayi tace"karki damu da maganganun da yayi Insha'Allah zan ma Abbana magana a Miki iyaka da shi shine kawai" murmushi Maryam tayi tace " nagode sosai " katseta Rahama tayi da cewa "dama Maryam kin iya masifa ban sani ba ,kice na ci gaba da Jan magana akwai me tare mun ,karamin pillow din dake kan gado ta jefe ta da shi Tana dariya ,mikewa tayi tare da cewa muje mu gaida momy zan wuce ,tare suka je har bedroom din momy Maryam ta gaidata ta yaba da tarbiyar Maryam din sosai sallama ta Mata zata wuce ,wasu new hijabs da aka kawo ma momyn daga dinki ta dauki biyu ta ba Maryam da turare ,da kyar ta karba ,har Rahama na cewa mommy kin karawa icce kananzir dama bantaba ganinta da mayafi ba Tana dariya , "to ai hijab din shi yafi a musulunci dama" cewar momy fitowa sukayi maryam nama Rahama dariya ,Driver din gidansu tasa ya aje Maryam a kofar nasu gidan ba musu ko ta shiga ya ajeta
Dan Bata manta abunda tayi a yau ba ,Bayan ta koma ta nuna wa kakus kayan da aka Bata aiko tayi murna sosai, godiya kawai take zuba ma momyn kamar a gabanta ,Daren ranar Maryam ta Dade kafin bacci barawo ya saceta , mummunan mafarki da TJ tayi Koda ta tashi a tsorace take sukuku take aiwatar da komai har lokacin makarantar su ya yi, niyyarta ma bazata je ba se ga Rahama ta biyo Mata hakanan ta daure ta shirya suka tafi har lokacin tashin su yayi, yau ya sayyadi Abdallah ya kula mutumiyar tasa akwai abunda ke damunta be yi kasa agwiwa ba wurin tsayar dasu Bayan an tashi tambayarta ya shiga yi Tana cewa "bakomai" ganin kamar ba fada zata yi ba yasa ya tambayi Rahama ,kaf ta kwashe abunda ke faruwa ta fadamasa ,A take shima ransa ya baci fiye da tunaninsu ,tare da cewa Marin da Maryam tayi ta matukar burgeshi hakan shine dai dai "ku tashi muje na rakaku " yace, ba musu suka Mike gashi da mota amma a kasa yace suje Dan fatansa daya Allah ya hadasa da TJ ya koyamasa hankali har kofar gidansu Maryam ko ya Kai su, godiya suka Masa tare da shiga gidansu Maryam Baki daya ,se da suka shiga daki, Rahama ta kalli Maryam tace" Wai kin yarda da zancena da nace Miki ya sayyadi son ki yake "?
Kallonta Maryam tayi tace "ban yarda ba tausayine kawai yasa ya rako mu" to yayi Rahama tace tare da Mata sallama ta wuce nasu gidan

NA TAKOWhere stories live. Discover now