PAGE 4

44 5 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

         ✍️
      *AISHA GALADIMA*


'''Ya Allah ka kawo ma kasarmu ta Nigeria zaman lafiya mai dorewa'''



         4️⃣   

-----------------------------------

A haka rayuwar ta ci gaba da kasance masu, malam salis na iya kokarin sa ganin ya inganta rayuwar iyalin nasa ,dai dai gwargwado, a wata Ranar Laraba da iyalin nasa baza su taba mantawa da ita ba Ita ce ranar da wani yaron malam salis dake ta yasa  aiki ya shigo gidan a gigice ,ya sanar musu da motar wani mutumi ta kucce Masa Yana zuwa ya kwashe malam salis yanzu haka Yana can an wuce dashi asibiti
Hankali a tashe  innah da sa'adatu suka bi bayansu Maryam lokacin suna Islamiyya ita da kannenta            
Koda suka isa har anyi admitting din  malam salis a Accident and emergency  ward be San Wanda yake kansa ba ,Innah se matsar kwallah take ,sa'adatu na tayata Kusan sa'a Daya se ga wani doctor ya fito da sauri innah ta Isa gabansa tace "Dan Nan Ya jikin salisu Yana da Rai ko"?  Tana matsar kwallah Dan Jim yayi se yace "Da sauki sosai Nan da wasu mintuna ze farfado" Yafito sa'adatu yayi da hannu yace ta same shi office ,se ganin kakus yayi ta Kara shan gabansa tace"ya zakace ta same ka nifa ,ko bakasan nice uwar salisun ba "
Kallon kakus din ya ci gaba da yi Yana mamakin tsohuwar danshi ganin ta manyanta ne yasa yake ganin Kamar be kamata ya tayar Mata da hankali ba ,
"ok" yace ku biyo bayana Dama shi Wanda ya kade malam salisu tuni ya tserewarsa
Bayan duk sun zauna ,Nan ya shiga yi musu bayanin cewa ya samu karaya ne hannu da kafa Dan haka ana bukatar 150,000 da za'ayi Masa aiki
Nan kakus ta nuna Masa Basu da wadannan kudin se dai a koma dashi gida amasa gyaran gida da ake yi
Be musa Mata ba ganin yanayin nasu kadai ma yasan Basu da wadannan kudaden Bayan an dawo da malam salisu gida ne aka Masa gyaran kafar da hannu, Maryam kanta ba karamin tashin hankali ta shiga ba ganin halin da mahaifin nata ke ciki Dan akwai shakuwa sosai a tsakaninta da shi dan shine ya zame Mata uwa da uba duk da kulawar da take samu wurin kakus lokuta da dama tafi fada ma Mahaifinta damuwarta fiye da kakus din  a haka  ya ci gaba da jinya a gida
A wanna lokacin fadar irin  abubuwan da wannan iyalin suka shiga baze misiltu ba, Dan me samo Abunda zasu ci gashi a kwance baze iya samowa ba ,abunda zasu ci ma wuya yake musu ,ganin haka sa'adatu tace zata fara kunun safe Maryam ta dinga tsaya Mata a bakin titi , Kai tsaye malam salisu yace be amince ba itama kakus  Bata so ammah sanin Basu da wata mafitar yasa ta lallashi malam salisu akan ai ba yawon talla ne zata yi ba tunda safiya ce be wuce tayi awa Daya ta dawo ba , a haka taci karfin shi har ya amince Maryam din ta fara fita duk sanda zata fita niqab take sawa mama sa'adatu taso ta hanata Innah ta taka Mata burki  Dole taja bakinta tayi shiru, in tafita kuwa har masu jira take iskowa inda take tsayawa, Bata wani jimawa take  dawo wa,da Dan abunda sa'adatu take samu suke cin abunda ya samu har 'ya'yanta su Auwalu take ma awara da alala da rana suna zuwa talla

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️©️®️®️®️®️®️
A hankali yake takawa cikin takun nasa me kama da Izzah excourt din nasa biye dashi, duk inda ya gifta bayi ne suke zubewa kasa suna bada gaisuwa  ba ya amsa musu se dai ya daga masu hannu har ya Isa part din nashi bayan ya shiga Kai tsaye bedroom din sa ya wuce ,zaune yayi akan gefen wani haddaden royal bed tare da jawo laptop dinsa dake jone a jikin socket ya fara lallatsawa tsawon 10minutes
Knocking din kofar aka yi har kusan sau biyu ana ukku yace come in ,  jin an shigo ammah an tsaya daga bakin kofar yasa ya dago lumsassun idanunsa masu kama Dana mage ya Dora su akan mutumin dake tsaye sanin me yake nufi da kallon nasa yasa yace "sir dama Abincinka ne aka aiko " se da ya Dan ja wasu sakanni sannan yace "ok su aje a dinning"

"Ok" bakin mutumin yace dake sanye da black suit ya juya ,shima komawa yayi a cikin dakin dama wani aiki yake a laptop dinsa ,bayan kusan 10minutes ya tashi ya fito daga dakin a hankali yake takowa steps din zuwa falon Kamar Wanda baya son takawa har ya sauko ba kowa a katafaren falon nasa se wani daddadan kamshi dake tashi da Kuma sanyin A c dake shiga har cikin bargo,

Direct dinning table din ya nufa tare da jawo Daya daga cikin kujerun ya zauna ,se da yaja wasu sakanni sannan ya bude wata hadaddiyar kula dake gabansa , sinasir ne  a ciki se kuma dayar da ya bude tuwo ne a ciki da aka saka a farar leda yayi fari kar da shi ,Dan guntun murmushi ne ya subuce Masa , yasan wannan duk aikin umee ne tafi kowa sanin abubuwan da yake so , ledar tuwon Daya ya fito da ita ya Dora Akan plate se Miya da ya zuba a Dan karamin bowl
Bisimillah yayi ya fara cin abincinsa hankali kwance salon yadda yake cin abincin abun kallo ne ci yake Kamar ba ya son ci ,karar wayarsa tasa ya dago kansa Yana kallon screen din wayar da ya Dora Akan table ,number ce kawai ba suna,har ta katse be daga ba haka aka ci gaba da Kira har kusan sau ukku Dan karamin tsaki yaja tare dasa dayan hannunsa ya jawo wayar ya kashe ta Baki Daya  ,ya rasa me yasa ma ya kunna wanna wayar da kowa ya San number tasa ,bayan ya kammala cin abincinsa ne ya tashi ya nufi bedroom din sa toilet ya sake shiga tsawon 5 minutes se gashi ya fito sanye da rigar wanka a jikinsa ,a gurguje ya canza kayan dake jikin sa zuwa dark blue suit dinsa ,manyan turarukansa Dake kan madubi ya shiga feffesa wa jikinsa  ,sak ya fito a baturensa ,wayoyinsa dake Kan gado ya dauka tare da brief case din da ya fito da ita ya fito ,Yana fitowa Daya daga cikin excourt din nasa yazo da sassarfa ya karbi brief case din hannun nasa ,da sauri ya nufi motar da ya matso da ita dai dai part din ya bude Masa ya shiga tare da rufe ta shiga yayi yaja sauran securities din Suma shiga suka yi motocin suka masu biya se bayan sun fito ne suka gyara motocin wadda yake ciki ta dawo ita ce tsakiya.......
.....................✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

NA TAKOजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें