PAGE 5-6

38 5 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

                 ✍️
       *AISHA GALADIMA*
  

'''Follow me on Wattpad@Aysha galadima 666
'''

'''May Allah give us the strength to smile when we feel sad ,to stay calm when we feel stressed and to have faith when we feel lost

'''

5️⃣➡️6️⃣

__________________________
Hadaddiyar wayar tasa ya dauka tare da latsa ta tsawon sakan ukku ya Kara a kunnensa "Wa'alaikumu Salam" yace cikin sanyayyan muryar tasa me dadin sauraro kafin yace" Ummee Afuwan na kusa missing flight ne shi yasa ban shigo ba ko Abbah ma tun A masalaci bamu hadu ba har yanzu nasan Yana cikin mutane da na Isa zan kirashi"Daga can dayan bangaren Tace "bakomai Abie na Allah ya tsare ka ya Kai ka lafiya ya dawo min da Kai lafiya" Kyakyawan murmushin da ya Kan dade bema wani irin sa ba yayi sannan yace "Amin Ummee jazakillahu bil jannat" itama tace "Amin " suka yi sallama aje wayar gefe yayi tare da kwantar da kansa bayan kujerar motar ya lumshe idanunsa Kamar me bacci , a haka har suka isa Airport din , da sauri aka bude Masa murfin motar ya fito ,da sauri excort din da suka shigo mota Daya ya dauko brief case din  sa ya rike ,wata mota da tun fitowar su daga masaurata take biye da su har suka shigo airport din itace wani chocolate guy ya fito daga cikinta Kai tsaye ya nufo inda yake tsaye Yana magana da sauran securities din nasa ,isowarsa yasa  securities din matsawa a gefe sanin matsayinsa a wurin ubangidan nasu , kallonsa ya shiga yi me hade da harara kafin  yace "habah Turaki Wai yaushe zaka bar wannan halin naka ace ka shigo Zaria har zaka fita baka kira Ni ba ma  " Dan guntun murmushi yayi kafin yace "ba haka bane Amir meeting din gaggawa ne ya tason a U S shiyasa  And is only two days zanyi na dawo"
Jin an fara sanarwa masu tafiya su shiga daga ciki yasa ya fasa fadin abunda yayi niya se  yace "ok Allah kiyaye hanya"
Nan ya sallami sauran masu tsaron nasa se mutum biyu da suka bi bayanshi , Wanda ya Kira daAmir se bayan tashin jirgin sannan ya bar Air port din

Ummee na sauke wayar wata kyakyawar yarinya ta fito daga dayan dakin wadda bata wuce shekara 21 cikin wata Arabian gown maroon colour wadda ta karbi farar fatarta cike da sangarta tace "Ummee Wai yaushe yaya Abie ze shigo   muyi pics din" Zama ta yi kusa da Ummee , kallonta Ummee tayi tace"Kinga balkisu se dai kiyi hakuri Dan yayan naki ma ya tafi U.S se dai idan ya dawo se muyi,turo Dan karamin bakinta mai kama Dana tsuntsu tayi kafin tace "shi Yaya baze gaji da aiki ba har da sallar ma baze zauna a gida ba, nasan Koda ze dawo ma Ummee ai mun bar Zaria ma "ta kare maganar cike da tabara, murmushi Ummee tayi kafin ta dauko wayarta tace "to bari na kirasa na ce Abla balkisu tace ka dawo" da sauri ta rike hannun Ummee tace "Afuwan Ummee Dan Allah kar ki kirasa" dama duk cika bakin balkisu tana matukar tsoron yayan nata, Dan ba wasa yake da ita ba duk da itace kauna Daya tilo da yake da ita, duk da shi ma Yana matukar son kanwar tasa Ammah ba ya wasa da ita acewar sa kar ta Rainasa ,Kuma ganin irin gidan dasu ke da rayuwar da suke ta jin dadi yasan dayawa zaka samu yaran masu kudi sun sangarce ,zaka same su da halaye kala kala marasa kyau shi yasa yake iya bakin kokarinsa ganin kanwartasa bata shiga a cikin wadannan abubuwan ba ,Dan haka ko Abu tayi shine ke mata hukunci duk da Tana kiyayewa,ita ko bala'in son yayan nata take , Ummee ce ta ce "ki shiga ciki ki sanyo mayafinki muje gaida me martaba" to tace tare da tashi
__________________________

Cikin sauri ta gama saka hijab din nata Ash colour da ya Kai Mata har kasa ,ga Kuma bakar safa a fuskarta ,madubi ta sake kallo zagayayyar fuskar ta ta tayi fayau ba komai a fuskar face farar powder da ta shafa se Kuma lipstick da ta shafa kadan , kakus dake zaune Tana kallon yadda take shiryawa tun dazu tace"Ni Kam mairo ki kwalli bazaki shafa a idon Nan naki ba kin bar ido haka kamar kwai" turo Dan karamin bakin ta tayi gaba sannan tace" barni a haka Dan Allah Ni da zanje makaranta kwalliyar me zanyi , "Ai ko ba makaranta ba karshen kwalliyarki kenan bari jin Ina cewa kin dauko farin hafsatu da kyanta in ba ki dinga daukar ado ba har yaushe Zaki samu mashinshini" cewar kakus, Jakarta ta Islamiyya ta dauka tare da niqab din da ta rike a hannu hanyar fita dakin ta nufa a ranta take cewa ai se ki yi Kuma bazan biye Miki ba kisa nayi latti bayan Wanda nayi, rike Baki kakus tayi Tana kallon Maryam da ta fice ko sallama Bata Mata tare da cewa a fili"oh ni habi Allah yasa yarinyarnan ba Aljannu ne da ita ba dai Dana Mata maganar aure se ta dinga kyaleni " Tana fita, dakin kusa da Wanda ta fito ta shiga inda babanta ke kwance akan wani gadon karfe Idon sa biyu  kuwa murmushi ya sakar Mata kafin ta shigo da nata murmushin ita ma dukawa tayi dai dai bakin gadon tace "Baba sannu ya karfin jikin naka "
Alhamdulillah yace da ita "Allah ya kara sauki Ni zan tafi Islamiyya kar na makara" cewar maryam
"Allah ya Miki Albarka " yace tare da Dora hannun sa akanta ,haka yake Mata tun kafin tayi wayon haka , murmushin dake matukar fidda kyawun nata duk lokacin da tayi shi tayi kafin tace "Amin baba kaima Allah yaba lafiya ya nuna min ranar da zaka taka da kafafunka" mikewa tayi tare da fita dakin kallonta ya ci gaba dayi har ta bacewa ganinsa kullum fatansa Allah ya bashi lafiyar da ze samu ya kula iyalin nasa
Malam salis tun bayan daurin da'aka Masa na gida hannun ya warke kafar ce dai da yanzu Kuma take Masa ciwo karayar ma ya samu saukinta da suka koma asibiti aka mashi gwaje gwaje suka ce ciwon sugar ne yake da shi se magunguna da aka rubuta mishi suka dawo ,yayi amfani dasu ya danji sauki ammah har yanzu baya zuwa ko'ina iyakarsa kofar gida wasu lokuttan, A hankali take tafiyarta har ta kawo kofar makarantar tasu Tana me jin nauyin yadda zata kalli malamin ajin nasu kusan kulum se ya Mata fadan latti Ammah har tarasa me yasa kusan kulum se tayi lattin kanta A kasa tayi sallama ajin nasu ,Malamin nasu ya amsa Mata ciki ta shiga ta samu wuri ta zauna har aka gama masu karatun be ce mata komai ba se bayan an tada su ne yace ita ta tsaya zeyi magana da ita, juyawa tayi ta kalli wata da kusan suke sa'ani da Maryam din tace "Dan Allah Rahama Dan jirani nazo mu tafi" dama tare suke zuwa wani lokacin , Dan gidan su Maryam be da Nisa da nasu Rahamar ,Maryam dince ma har  yanzu Bata saki jikinta da Rahamar  ba ganin ta fito gidan masu dashi shiyasa take Dan kakauce Mata a wasu abubuwan ,ita ko Rahamar son Maryam din ne take domin tun ranar farko da ta shigo islamiyyar taji maryam din ta kwanta Mata a rai duk yadda Maryam din ke son yaki ce ta duk ta kula Kuma tasan saboda banbance banbancen dake tsakaninsu yasa take haka shiyasa ma Bata fasa kula ta ba , fadan dai da ya Saba Mata shi yayi ,ita dai hakuri ta shiga basa ,Nan ya shiga Mata tambayoyin da suka daure Mata har ta fito Tana mamakin ya sayyadi Abdallah ganin tayi shiru Koda suka fara tafiya yasa Rahama ta katse shirun tare da cewa "me ya sayyadi yace Miki Maryam"? Dan Jim tayi kafin tace"fadan da ya Saba min ne dai yayi, da Kuma tambayoyin da ban fahimci me yasa ya min su ba " kamar ya Rahama tace
"Wai shekarata nawa? Kuma aji nawa nake a secondary? Dariya ce ta subucewa Rahama har ta sa Maryam tsayawa Tana kallonta kafin tace "Habah Maryam kamar ba 'yar boko ba ai duk inda kika ga kare na shinshina Abu dauka ze yi Ni dama tuni na harbo jirgin ya sayyadi Abdallah ,mutuminnan fa Maryam duk ajin Nan namu ke kadai ce yake daga ma kafa ko Abu ta faru ,su fati ma wancan satin naji suna zancenku ke da shi" ganin yadda Maryam ta zare idanunta gaba ki daya Tana kallonta yasa ta sake kwashewa da dariyarta ,Maryam Kam abun ba karamin mamaki ya Bata ba jin abunda Rahama tace yanzu ma wasu abubuwan da suka faru a baya suke dawo Mata irin yadda komai ya taso a ajin nasu itace ya sayyadi yake sakawa,A take Kuma taji wani tsoro ya kamata na ya sayyadin ina shi ina ita ai yafi karfinta wannan ai shi ake Kira wutsiyar rakumi (novel din billyn Abdul) saboda yadda taji a 'yan ajinsu baban ya sayyadi Abdallah babban alkali ne a kaduna ,shima daka gansa kasan Ra'ayi ne da neman lada yasa shi karantarwar ba Rashi ba tunda ga tsadaddun kayan da yake sakawa da irin kamshin da ke tashi a ajin nasu duk lokacin da ya shiga ajin nasu ,Dan kusan rabin Ajin wadanda suka ce suna sonshi ba zasu kirgu ba rashin samun fuska a wurinshi yasa suka Sha jinin jikinsu ,Maryam din da suka ga Yana yawan magana da ita itace suke ba Sako ko letter ta basa ,se dai itama Bata taba Gigin fada Masa ba ,ganin ta Lula duniyar tunani yasa Rahama Dan girgiza kafadarta , firgigit ta dawo hayyacinta ta kalli Rahama, ganin Bata dawo ma natsuwarta yasa Rahama cewa"Kinga Maryam kar ki daga hankalinki Mana Ni Banga abun damuwa a Nan ba kila hasashena ne kawai tunda har yanzu be fasa maki haka da bakin sa ba ,sannan in ya Sami kamarki ai ya samu macen kerewa sa'a ma" da sauri Maryam ta katseta tare da cewa" Kinga Ni nama fi son ya tsaya a matsayin malamina kawai yafi" girgiza Kai Rahama kawai tayi tare da cewa Kinga mu tafi Ni dai magarib ta kusa sun fara takowa kenan suka ji ansha gabansu da sauri duk suka ja baya.................✍️

*Aysha galadima ce*

*Vote*
*Comment*
*Share*

NA TAKOWhere stories live. Discover now