PAGE 9-10

30 5 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

                 ✍️
       *AISHA GALADIMA*


'''Follow me on Wattpad@Aysha galadima666'''

'''Are you looking for a unique and Qualitative abayas @ Affordable price ?
Esher general enterprises is always there for you, you can  get any kind of Arab Abayas of different countries @ Affordable prices just call or chat her on WhatsApp @ 08064933819'''
'''You will thank me later'''

9️⃣➡️🔟

____________________________


Jiki a sanyaye ya Isa part din nasa Daya daga cin securities dinsa dake biye dashi ya dagawa hannu sanin me yake nufi da hakan yasa ya ja ya tsaya a kofar sashen nasa ,da kansa ya ci gaba da tafiya har ya Isa ga Babbar kofar shiga falon  hannunsa ya sa  ya murda handle din kofar ta bude ,Rufe kofar yayi ya fara takowa daga ciki beyi mamakin Wanda ya gani ba a zaune a Daya daga cikin kujerun falon ,dauke kansa yayi bece dashi komai ba tafiyarsa ya ci gaba dayi ya nufi bedroom, munir dai kallonsa ya ci gaba da yi har ya bacewa ganinsa ,Dan Jim yayi Yana tunanin meke damun sa daga dawowarsa  kuma Dan yaga Alamar akwai abunda yake damun sa ,Yana shiga bedroom din kayan jikinsa ya fara cirewa daga Nan ya shiga bathroom, wanka yayi ya fito Dan ba karamar gajiya yake ji ba bayan ya fito tsane jikinsa yayi da karamin towel din Daya Dora Akan wuyansa , manyan turarukansa dake saman mirror ya dauka ya shiga feffesawa kamar ba gobe a take bedroom din ya Kara daukar wani daddaden kamshi da Kai tsaye bazakace ga kalar kamshin ba , wardrobe ya nufa Yafito  da wasu kayan baccinsa masu laushi Riga da wando ya saka ,har ya zauna bakin gado ,ya tuna da munir na falo,yasan har yanzu be tafi ba shi yake jira ,Dan guntun tsaki yayi sannan ya kwashi wayoyinsa dake kan gado ya riko a hannunsa ,Koda ya fito ko Yana Nan zaune Yana kallonsa kamar yadda yayi tsammani, a hankali ya tako ya zauna akan one sitter ,munir daukar remote yayi ya rage karar tv din tare da kallon turaki  da yaga ya lumshe idanunsa ,kafin yace "lafiya kake kuwa na ganka wani iri"? Se da ya Bata minti 2 Dan har ya cire Rai da amsarsa  kafin ya shiga koro Masa bayanin yadda yayi da Mai martaba ,ai Yana gama fada masa ,munir dariyar da yake ta kokarin mayarwa kasa riketa yayi har ta fito fili kafin ya tsagaita ganin kallon da Turaki ke Masa , "Ai me martaba ya kyauta kuwa sosai Mata hudun ya kama ce ka " wani guntun tsaki yaja tare da mikewa ya nufi bedroom dinsa ganin haka yasa munir Kara bude muryarsa yace "ka shirya gobe mu ziyarci  matan da aka ce sunzo ,in babu jibi mu shiga kauyuka" da karfi Turaki ya bugo kofar bedroom dinsa Yana me jin haushin munir din ,ganin ya dauki zancen nasa Almara,shi Kam munir dariyarsa ya ci gaba dayi dama kullum in Yana maganar aure Turaki. Katse sa yake yace ya cika son Mata tun be tafasa ba ze kone shekarar shi nawa A duniya ,Imagine me shekaru 29 ake cema tun be tafasa ba zaya kone🤣 kafin ya tashi ya kashe kayan kallon tare da nufar Daya daga cikin dakunan dake falon ya shiga domin ya kwanta dama indai munir ya shigo Zaria to munir ze dawo part dinsa da Zama in Kuma ya koma Abuja ko wurin aikin sa shikenan

Munir da Turaki tare suka taso duk da Turaki ya dan girmesa da kusan shekara 2 ,munir da ne ga wamban masarautar zazzau ,tun Yana yaro yake da sha'awar ganin dokuna dan haka kullum gidansu ze matsa a dai kawo sa gidan sarki a lokacin Kuma mahaifiyar Turaki Tana Zama gidan sarki tun da aka aurota kasancewar ta balarabiya 'yar kasar Riyad Bata San duk wasu al'adu ba na kasar Hausa ba shi yasa ta zauna a masarautar zazzau anan fa aka koyamata abubuwan da  dama harda harshen hausa   kafin mijin nata ya Zama shugaban kasa su koma Villa da zama ,nan fa yake ganin Turaki ,duk da shi Turaki tun Yana yaro yake miskili ba ya son hayaniya magana ma in ba yasanka ba ba  yayi ,Wanda be sanshi ba zece Izzar mulki ce Wanda dabi'arsa ce hakan ga Kuma jinin sarauta da ke yawo a jikinsa,anan fa suka fara abotar tasu Yana gama primary school aka dauke sa  gaba Daya zuwa kasar  UK a can fa  yayi karatun secondary da University Inda ya  karanci medicine a fannin Mata da gamawarsa kuwa a can suka rike sa ganin kwazonsa ya fara aiki dasu  A Yanzu haka babban consultant ne ko a kasar UK Ba kowa yake dubawa se jigajigai

NA TAKOWhere stories live. Discover now