NA TAKO

49 7 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

           ✍️

  *AISHA GALADIMA*




        3️⃣

------------------------------------

Maryam salis sa'ad shine cikakken sunanta ,Mahaifinta Dan Asalin jihar kebbi ne ,a yawuri local government,mahaifiyarta kuwa haifafiyar Riba local government ce duk a jihar kebbi , duk  da ba a gari Daya suke ba ammah akwai zumunci me karfi a tsakanin su ,Wanda auren zumunci ne aka ma malam salis da matarsa Hafsa ,

Malam salis shi kadai ne a wurin iyayensa mahaifinsa Allah ya Masa rasuwa tun Yana karaminsa mahaifiyar sa ce ta ci gaba da kula dashi har zuwa girmansa

bayan auren nasu malam salisu ya fara neman sana'ar da zeyi tunda auren yi Masa shi akayi irin auren gatan Nan ne da iyaye kewa 'ya'ya tun a shekarun samartaka ,babu irin fafutukar da beyi ba ganin ya samu abunyi ammah abun ya faskara ,kasuwa yake shiga kullum Yana dako Yana samun abunda zasu sa a bakin salati ,ana tsaka da hakan ne har yayi tunanin  fara facin Taya ,Kamar da wasa ko sana'ar tasa ta samu karbuwa ,hafsat irin matan Nan ne da surutu be dame su ba Dan haka malam salisu ke jin dadin Zama da ita auren su kusan shekaru hudu Allah be Basu haihuwa ba, A lokacin mahaifiyar malam salisu , Inna habi tayi ruwa tayi tsaki lalli se malam salisu yayi aure badan yaso ba ,ya Auri wata da ake Kira sa'adatu a bazawara ya aure ta irin masu Kai abincin Nan ne a tasha dama ta jima Tana sonsa shine baya kulata ,ganin Inna ta matsa Masa se yai tunani bari ya Auri wadda ke sonsa koba komai zata dinga yin yanda yake so, haka aka Sha biki sa'adatu tare ,ita Hafsa kwakwata Bata damar da  kanta ba tunda ba abunda ya canza daga wurin mijin nata ,ammah tun a wurin kawo amaryar jikinta yai sanyi ,a yadda dangin sa'adatu suke ta yi Mata habaici iri-iri  , yayar ta Hannatu da tazo ita ce bayan sun gama arerewar su ta shiga Bata Baki da shawarwarin da zasu amfane ta 

A haka zaman nasu ya ci gaba da kasancewa kadahan madahan ,bayan shekara biyu da auren sa'adatu ,Se ga ciki ya bullu a jikin Hafsa , malam salisu ba karamar murna yayi ba ,sa'adatu Kam ba karamin bakin ciki taji ba ,tunda ita ma har yanzu shiru ba abunda ta samu ,tun daga Nan fa se ta fara shige shige malam , Ammah da yake Allah mabuwayi ne gagara misali ,duk inda taje se ace Mata se dai fa hakuri , a haka Tana ji Tana gani har ya  girma ya shiga watan haihuwarsa

A wani dare hafsat ta tashi da nakuda gashi malam be dawo ba , anan cikin dakin nata tai ta nukurkusu ,can da taji abun yafi karfin ta ta shiga Kiran sa'adatu !!! , Sa'adatu na jinta tayi Kamar Bata ji ta ba ,Tana a cikin wannan halin ne Allah ya taimaketa ta haihu se dai abunda ta Haifa na fitowa ,jini ya balle Mata , can dai da sa'adatu taji kukan jariri ta maza ta fito daga dakinta Wanda yayi dai dai da shigowar malam salisu , a tare suka shiga dakin ,da sauri ya isa ga matar tasa ganin Kamar ko numfashi Bata yi  da sauri ya juyo yace ma sa'adatu ta dauko Masa ruwa

Kafin ta dawo se ga sallamar Inna tazo gidan Nan itama hankali tashe tai dakin Koda aka kawo ruwan Inna ta shafa Mata har so ukku batayi numfashi ba Nan ta shiga tataba jikinta hannu da wuya

Kawai se gani sukayi Inna ta shafeta tana matsar kwalla ,wasu zafafan hawaye ne suka zubuwo malam salis ,abunda aka samu sa'adatu har ta gyarata itama duk da ba zaman dadi suke ba se da jikinta yai sanyi a wannan Daren

Bayan sadakar ukku se ga Inna ta dawo gidan da Zama ace warta ita zata kula da jaririyar mai suna maryam ba yadda sa'adatu ta iya tunda Inna tafita iya rashin m shi yasa Ta kawo ido ta sa

Madara malam salisu ya dinga siya innah na kula da ita yadda ya kamata

Maryam nada shekara biyar a lokacin sa'adatu itama ta haifi 'ya'yanta maza har biyu , Auwal ,da haris ,Kuma a lokacin ne kasuwancin malam salisu yaja baya sosai , Dan se ya fita ya dawo ba a samo komai ba

Ana tsaka da wannan wani Amininsa dake zaune a kaduna ya matsa Masa akan ya dawo kaduna da Zama Dan Nan ba laifi masu irin sana'ar tasa suna samu sosai ,yace se yayi shawara da mahaifiyar sa ,da zullumi ya tambayi innah Dan ya dauka zata hanashi zuwa ,se ga shi ta amince ,shi ya fara zuwa daga baya ya kwashe su gaba Daya suka koma kd

A haka rayuwar ta ci gaba da gudana ,tun dawowarsu ya saka Maryam makarantar islamiya da Kuma boko ta government ,ba laifi Tana maida hankali musamman a islamiya ,yanzu Tana a ss2  ,sannan tayi saukar Alqur'ani har ta fara hadda

✍️ *Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

NA TAKOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang