PAGE 13-14

25 6 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

                 ✍️
       *AISHA GALADIMA*

'''Follow me on Wattpad@Ayshagaladima666'''


'''Ya Allah ka kawo karshen matsalar tsaro a kasar  Nigeria  ka bamu zaman lafiya Mai''' '''dorewa'''


1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣

____________________________


Katse wayar yayi tare da hararar ta kamar munir ne a gabansa laptop dinsa dake kan table ya dauka tare da  bude kofar body guard dinsa dake zaune akan wasu kujeri dake fuskantar office din Daya ya matso da sauri ya karbi laptop din dake hanunsa kofar fita ya nufa suna biye dashi, suna fitowa harabar hospital din da sauri dayan  ya bude motar da ze shiga ya shiga Suma suka shiga ,Jan motocin akayi suka shilla kan titi tafiyar mintuna 10 ce ta kawo su Villa ,wadda mutane da dama ke Kira fadar shugaban kasa ,taci sunanta kuwa Dan hadaddin gidaje ne me kamar estate acan ciki fadar shugaban kasa take , Falon da ya San ze isko mahaifiyarsa Kai tsaye can yashiga ,fadar tsaruwar falon Bata lokaci ne zaune take cikin wasu Royal chairs ,Tana sanye da wani dakakken lace blue Wanda ya karbi fatar jikinta kamar ba ita ta haifi Turaki ba tsabar kyawon jiki,fuskarta dauke da murmushi take kallon Dan nata da ya shigo ,shima murmushin yayi tare da Zama a gefenta tare da cewa "Ashtaktu Iaikil katheer ummee(I miss you so much Mom) murmushi tayi cike da jin dadi daukar wani Abu tayi  ta latsa dake gefen kujerar da take ,cikin minti Daya se ga wata matashiya ta fito dauke da babban faranti dake dauke da glass cups da juice se snacks ajewa tayi akan center table din dake falon tare da gaida su ta wuce , lemun ya tsiyaya ya Sha sannan yace "ummee bilkisu fa? " "Tana dakinta Tana hada kayanta kasan gobe zata wuce zaria,Kai yaushe zaka je?" cewar ummee  "may be naje tare da itan gobe Dan har munir ya fara min korafi " cewar Turaki,  ummee tace "da gaskiyarsa ai ni tare da Abbanka zamu zo on Thursday tunda Friday za'a daura Auren, cike da jin dadi suka ci gaba da firarsu ,washe gari shida bilkisu suka zo Zaria sun samu tarba yadda ya kamata kuwa part din hajjo bilkisu ta sauka kakarsu ce kuma uwargidan sarki,  Turaki me martaba rike sa yayi Yana ta jansa da fira tare sukayi lunch har dinner se dare munir yazo da kansa ya jasa suka fita gidan Kara tattauna yadda shagalin ze kasance su kayi,Dinner ta mussaman Turaki ya dauki nauyin yima munir wadda Ranar Friday za'a yita da daddare ,suna tsaka da magana se ga wayar munir ta dauki Kara cike da murmushi ya daga tare da cewa"sweety na " Amsa gaisuwar da aka Masa daga dayan bangaren yayi daga Nan ya shiga cewa" kamar kin San Ina son Kiran naki maganar dinner dinnan mutum 50 muke bukata daga bangarenki zan aiko a kawo Miki gate pass, "50 fa habah nawan duk danginmu nikam wazan ba wazan hanawa kana ganin har Rahama ma Dana ta mutanen  "cewar Nabila numfashi ya furzar sannan yace" hakuri zakiyi fa yayan ki ne  ya shiryar da ita and  mutane 100 yake bukatar gani a wajan " sanin Wanda yake nufi yasa tace"ok ba damuwa se ka aiko din sallama sukayi sannan ya yanke wayar, dagowa Turaki yayi ya kalli munir Wanda tun lokacin da ya fara wayar yake latsa tasa wayar tare da cewa"A hakan zakuyi auren kana Bata hakuri komi kankanta Abu"? Dariya munir yayi kafin  yace "bazaka gane ba Ammah Allah ya hadaka da wadda zata dinga juya ka" kallon kanka ya kwance Turaki ke jifan munir dashi sannan yace "Ashe ko zaka mutu baka ga ranar ba" lokacine ze nuna haka" cewar munir

_____________________________

shirshirye na mussaman gidansu Rahama akeyi na bikin yayar ta ta ba kama hanun yaro an canza komai na part din Su Rahamar har fentin gidan su an sauya Bayan carnopi din dake akwai a  filin gate dinsu har wasu aka Kuma sakawa,shagala sosai Maryam tayi da kallon yadda gidan nasu ya Kuma kawatuwa Jan hanunta da Rahama tayi shi ya dawo da ita hayyacinta biyarta tayi suka cigaba da tafiya zuwa part dinsu Kai tsaye dakin da Yaya Nabila take suka shiga ,zaune suka same ta wata buzuwa na cigaba da shafa Mata wani hadin dilkensu ba abunda ke tashi se wani kamshi me dadi a dakin,matar ce ta Amsa sallamarsu shigowa sukayi ,tunda suka shigo Nabila ke kallon Maryam tasbihi take a ranta da yaba kyawon Maryam ,Maryam dince ta katse Mata zancen zuci da tace "Yaya Nabila ina wuni ya hidima"? Cike da sakin fuska tare da cewa" kece Maryam din Rahama ko " tare da kallon Rahama,itama Maryam Rahamar take kallo, dariya Rahama tayi tare da cewa "eh itace Yaya Nabila ya kika ga kawar tawa" hannu ta daga alamar tayi dinnan👌🏻 ita dai Maryam murmushi ne nata ,bari na cire uniform nazo na rakaki" cewar Rahama Bayan fitar Rahama Yaya Nabila fira ta cigaba da Jan Maryam din Dan haka kawai take jin ta kwanta Mata sosai ba Wai Dan kyawonta ko wani abuba ,Rahama ce ta dawo Bayan ta canza kayan sallama Tama Yaya Nabila suka nufi hanyar fita dakin "gobe kizo Maryam a maki lallen kema " cewar Yaya Nabila, "kwantar da hankalinki ai dolenta Yaya da kaina zanje na taho da ita " cewar Rahama, Bayan fitowarsu Nan Rahama take Kara jaddadama Maryam akan gobe tazo da wuri har saloon zasu je da to kawai take amsa Mata bawai Tana tunanin zata zo din ba ,Dan ganin take kamar ta zake sosai a sha'anin bikin duk da kuwa Rahamar ce ke sakata a ciki ,Kaya kusan set goma aka dinka Mata ita da Rahamar Wanda Abbansu ne yai hakan ga kala 3 na Ankon da momyn su Rahamar ta masu da shoes and veils da ta siya musu ,Ranar da Rahama ta kawo kayan Sosai Maryam ta dage bazata karba ba har kakus tasa baki biris Maryam tayi ,karshe Rahama daukar jakar kayan tayi ta koma da su tare da daukar fushi da Maryam ,washe gari se ga mommy tazo da kanta gidansu Maryam da kayan Sosai ta shiga yima Maryam fadan Bata dauketa mahaifiya ba kenan ,kunya duk ta cika Maryam har da hawayenta Tana ba mommy hakuri ,godiya marar adadi kakus Tai Tama mommy har ta wuce,washe gari se dai Maryam ta tashi Bata ga kakus ba ,Ashe gidansu Rahama taje yima Abbah godiya ,Nan dai yace ai base ta gode Masa ba Maryam kamar Rahama take a wajensa ,har kudi ko yaba kakus ,karbe abunta tayi data dawo take ba Maryam labarin inda taje ,aiko ta nuna jin dadinta Ammah jin har kudi Abbah ya Bata ta karba shine ya sosawa Maryam Rai sosai da Tai magana kakus cewa tayi bakin ciki take Mata Dole kyaleta Maryam tayi, a Islamiyya Rahama share Maryam tayi ,sanin Bata da gaskiya itace ta ba Rahama hakuri aka wuce wurin, Bayan Rahama ta kawo Maryam gida da kanta ta fada ma kakus cewar gobe Maryam tazo a musu lalle da saloon, "to zata je ai goben" cewar kakus  sallama Rahama ta musu ta tafi , "nace kin gano habilar da kika je gidan nasu"? Cewar kakus ,me Maryam zatayi kuwa in ba dariya ba sannan tace "habah kakus ya kike Bata Mata suna Nabila ne fa ba habila ba" fita kakus tayi a ranta take cewa ku ji min ja'ira a haifeta agabana Ni take koyawa fadar suna

A gurguje
An fara gudanar da sa lalle ne a gidan kanin baban su Rahama ,sa lallen yayi kyau sosai Yaya Nabila ba karamin kyawo tayi ba ,ranar Rahama da Maryam wata Holland lemon green suka saka dinkin Riga da skirt ne Suma ba karamin kyau sukayi ba kamar wasu 'yan biyu ,washe gari akayi  walima , inda malama juwairiya ta gabatar da wa'azi ,Yaya Nabila yau shigar Alkyabbar milk and golden tayi tayi kyau sosai abunta , Basu Dade da zuwa ba Maryam tace ma Rahama Bata jin dadi zata koma ,ganin yanayinta yasa Rahama Bata takurata ba kayan walimar ta Bata sannan ta hada ta da driver ya mayar da ita Bayan ta fada Mata Tasha magani tasan gobe dinner fa , to Maryam din tace,Koda ta dawo gida zazzabi rufeta yayi ga mararta data ji Tana Mata ciwo kadan kadan, da kyar dai kakus ta matsa mata ta tashi Tasha magani, dama Kuma haka take duk lokacin data kusa period se tayi ta zazzabi da ciwon mara ammah ba me tsanani ba ,Wanda a lissafin ta yau saura kwana 2 yazo , Koda ta tashi washe gari da dan sauki Dan zazzabin ya saketa ,tun 10 Rahama tazo gidansu cewar zata rakata wani wuri har kayanta tace ta dauka Dan bazasu dawo ta Nan ba , kakus ta Bata go ahead din zuwa ,ummah sa'adatu yanzu ita da Maryam se dai kallo tuni tabar fitar Mata tallar koko se dai a shigo cikin gida a siya , se dai wasu aikace aikacen , tafe suke cikin mota Rahama se wayarta take Maryam na kalle kallenta ganin ginin da motar tasu take kokarin shiga yasa Maryam kallon Rahama da gama wayarta kenan tace"Nan Ina ne kamar gidan sarauta"? Daga Mata Kai Rahama tayi tare da cewa"eh marasautar zazzau kenan, na manta na fada Miki ai mommy 'yar Nan gidan ce" shiru kawai Maryam tayi Bata ce komai ,se cigaba da kallon tsarin ginin gidan sarautar take Tana me jinjina kyawonsa a ranta ,tsayuwar motar ne ya dawo da ita tunaninta fita Rahama tayi itama fitowar tayi "yawwa malam Musa ka jira anan yanzu za'azo akwashi kayan " cewar Rahama ,nufar wanin babban part suka yi sun kawo part din  Rahama na kokarin rike handle din Taga an bude kofar  da fitowa Wanda Taga ya fiton ne yasa idanunta Kara girma....................✍️

*Aysha galadima ce*

*Littafinnan na kudi#300 ne ga masu bukata zaku iya turawa ta wannan account number *3118088470* *Aisha Muhammad galadima first bank*
*A tura shaidar biya a 08064933819*
*ko katin MTN a wannan number 08064933819*

NA TAKOWhere stories live. Discover now