PAGE 7-8

30 6 0
                                    

💐 *NA*
        *TAKO* 💐

              👠

                 ✍️
       *AISHA GALADIMA*

Follow me on Wattpad@Aysha galadima666

'''This Dunya is like a shadow if you try to catch it you will never be able to do so, but if you turn your back ''' towards it , '''it has no choice but to follow you'''


7️⃣➡️8️⃣

____________________________
Hayakin tabar da yake Sha ya busar daga cikin bakinsa sannan ya yarda konon ya take da kafarsa ,sanye yake cikin wando three quarter se bakar t-shirt dake jikinsa kansa dauke da askin da samarin bana bakwai ke Kira balatoli, bakin Nan nasa yayi bakikirin alamar mashayin taba ne da sauran Abubuwan kayan maye da ba'a rasaba ,bakine me matsakaicin tsayi,Yana da kyawonsa dai dai gwargwado, ganin yadda su Maryam suka ja baya yasa ya danyi wata siririyar dariya irin tasu ta 'yan duniya sannan yace "ji Mana baby se kace Baki gane Ni ba"jin muryar tasa yasa Maryam ta sake zaro idanunta Tana kallonsa ta gane shi tsaf Dan kusan kullum duk ta fita tallah se yaje ya Mata magana ita ce  take share shi ,Dan farkon zuwansa inda take sayar da koko har da 'yan gang dinsa ya zo  A lokacin niqab dinta na a fuskarta ,ji tayi kawai anyi sama dashi ,Abokan nasa ko shewa suka saka suna fadin "se oga TJ" Maryam ba karamin tsorata tayi ba Dago fararen idanunta tayi da suka cika da hawaye ta kalle sa ,sakin Baki Tj yayi Yana kallonta a take yaji ta shiga ransa Dan haka tsawa ya ma yaran nasa yace su wuce su bashi wuri ,duk wucewa sukayi suka bar Tj dake tsaye Yana kallon Maryam,niqab din ya Mika Mata ,a sanyaye ta dago hannunta dake rawa ta karba "kiyi hakuri kinji" T j yace ,kamar  ba zata tankashi ba se kuma tace "ba komai" Bayan ta daura niqab din kin tafiya yayi  se da ya tsaya ya sayi kokon nata sannan ya tafi ,to tunda ga ranar lokaci bayan lokaci se ya je wurin da take se da kokon, har yace Yana sonta itace tace ke sharesa duk lokacin da yaje ya gama zubarsa ya wuce ko A Bata ce masa, Dan Tj tun a kallon farko mutum ze gane tarbiya tayi karanci tattare dashi ,Rumtsar hanunta da Rahama tayi shi yasa  taji wani karfi yazo mata tace" ka kauce mu wuce Tijjani kaga magarib ta gabato " wani murmushi ne ya subuce Masa jin yadda ta Kira sunansa kafin yace "to yayi baby ammah Dan Allah ki dinga Kiran sunana haka " ya kare maganar kamar wani soko daga Maryam har Rahama galala sukayi suna kallonshi , Jaye wa yayi da sauri suka wuce ,tsaye yayi Yana kallon su har suka bacewa ganinsa a ransa ya Raya Allah ya kai giwa ga harawa ,Yana lasar harshe kamar wani maye , juyawarshi yayi ya tafi, tunda suka tafo ba Wanda yai magana har se da suka bullo layin gidansu ,sannan Rahama ta kasa jurewa tace"Maryam a'ina kika San wancan mutumin"? Jin Kiran sallar da'ake yasa Maryam kallon Rahama tace"Kinga bari se gobe idan mun hadu kinji Kiran sallah ake" daga Mata Kai kawai Rahama tayi Dan ta San tunda tace se gobe ba fadamata zata yi ba ,sallama suka yi kowace ta nufi nasu gidan ,da sallama ta shiga gidan nasu dai dai  sa'adatu da suke Kira da ummah ta fito daga kitchen, Amsa sallamar Maryam tayi kamar an Mata Dole, A sanyaye Maryam ta nufi dakin su ita da kakus "ki aje jakar kizo ki tacen kullun kokonnan" cewar ummah kafin Maryam ta amsa se jin muryar Kakus tayi data fito daga bandaki tace"bazata yi ba yo Dan rashin tausayi daga dawowar yarinya ko hutawa batayi ba zakice ta Miki tatar kullu,ke aikin me kike a cikin gidannan" da sauri ummah tace"to zanyi dama Dan zan  shiga sallah ne nace ta min" se da kakus ta kyafkyafta idanunta tace "ita kafirace kenan" Nan ummah ta shiga Bata hakuri Dan tasan halin Innar ba dadi ne da ita yanzu zata ci gaba da mitar maganar ,duk da itama ummar da kalar nata mugun halin ba Dan Innah a tsaye take ba da ba karamar wahala Maryam zata ci gaba da Sha a gidan nasu ba ,Dan haka ita dai kullum fatanta Allah ya ba jikanyar ta ta miji tayi aure inda zata huta ,Dan kusan ayyukan gidan ita ce ke yin su girki kadai ummah keyi a gidan se fa wankin kayanta ,ko shi taso maryam ta ci gaba dayi har na yaranta Innah ce ke taka Mata burki,Ita Kam Maryam ranta fari tas ta shiga dakin nasu Tana me Kara jin son kakar ta ta
____________________________

A natse ya fara saukowa matatakalar jirgin Yana shakar Iskar kasar tashi ,Yana jin wata natsuwa na Kara shiga jikinshi ,har ya sauko da sauri dogarawa da Kuma escort dinsa duk suka nufo shi "Takawarka lafiya dai ,barka da isowa Turakin zazzau,sikari bakai farin banza ba Allah ya ja zamaninka" Daya daga cikin dogaran ne ya fara wannan kirarin ,daga Masa hannu yayi ,sanin me yake nufi yasa ya kama bakinsa ya tsuke ,kallon motocin da aka zo dasu Kashi da Kashi yayi ,dogarawa ga Wanda suka zo dasu gefe ,body guard dinsa ga nasu a gefe, ya rasa me yasa duk lokacin da ze sauka Zaria me martaba yasan Yana da securities dinsa ammah se ya turo dogarawa da nasu motocin a daukoshi , ganin ba yada zabi yasa yace ma securities dinsa su bi su a baya shi Kuma ya shiga wata   black Jeep me suna Dodge da dogarawa suka zo da ita sauran suka shiga ragowar motocin, daga Nan suka shilla kan titi tafiyar minti 20 ce ta kawo su masarautar, tunda motocin suka shigo ba'abunda ke tashi se kade -kade da bushe bushe ,Yana daga zaune a cikin motar Yana tunanin me yasa ake wadannan abubuwan ko wani abun ke faruwa a masarautar ,to Ammah ko jiya yayi waya da Ummee Bata ce Masa wani Abu na faruwa ba ,tsayuwar motocin ya katse Masa tunani ,murfin motar da sauri wani bafade ya bude , se da ya kwashe kusan minti 3 be fito ba sannan ya zuro  kafarsa Daya waje dake sanye cikin cover shoe kafarsa sanye cikin black socks guntuwa ,zuro dayar yayi ya fito gaba Daya ,Nan fa kallo ya koma sama  ,masu kade kaden suka shiga yi Masa kirari ,be bi ta kansu ba yanu fi sashen me martaba Dan yasan yanzu Yana sashensa tunda yamma tayi ,Yana kaiwa se da ya jira aka Masa iso ,sannan ya shiga da Sallama ya shiga katafaren falon da aka kawata da ado irin na gidan saurata ga wani haddaden kamshi na tashi ,tsayawa fadar tsaruwarsa Bata lokaci ne , wani Kyakyawan dattijone kishingide Akan titimi Da murmushi akan fuskar tasa ya Amsa sallamar tasa ,takawa yayi har kusa dashi sannan ya zauna ,gaidashi yayi cike da girmamawa ,cikin jindadi yake amsa Masa ,tashi zaune yayi yasa hannu ya jawo dayan hannun Abie yasaka a nasa sannan yace "ya gajiyar hanya ya ka baro masu jajayen kunnuwan ,Koda yake kaima naka Jan ne ai" murmyshine ya subuce Masa sannan yace"lafiya Lau Ranka ya Dade" Nan dai ya shiga Masa tambayoyin akan abunda ya kaisa Yana bashi Amsa ,Kiran sallar magariba da akayi yasa yace yaje yayi Arwala suje masalaci,Bayan gama sallar magrib Basu baro masalacin ba daga shi har mai martaba seda suka yi Isha'i sannan suka fito hannun sa cikin na mai martaba suna tafe suna 'yar firarsu wadda Ni kaina bansan me suke tattaunawa ba,har suka Isa sashen me martaba Koda suka shiga daga ciki Nan suka tarar duk anjera manyan warmers tare da sauran kayan cin abinci akan wata Babbar carpet da shape  dinta yake cycle ,har suka shigo be saki hannun nasa ba Kai tsaye wurin kayan abincin ya nufa da shi suka zauna , jakadiya ce tayi sallama ta shigo  sarki ta fara gaisarwa kafin ta juyo kan Turaki shi ya rigata magana ta hanyar cewa "Barka da dare " Yana murmushi Dan dama Allah ya had a jinin sa da jakadiya duk da bawani sabo bane sosai a tsakaninta su ,cike da fari'a ta Amsa Dan Tana jin dadin yadda shalelen me martaba ke girmamata, Abincin ta zuba masu a kwano Daya, tare suka ci har suka kammala, Bayan sungama ,me martaba ya kalli Turaki yace "Al'amin " dagowa Turaki yayi ya kalle sa jin Kai tsaye ya Kira sunansa ci gaba da maganarsa yayi kamar haka" Na Dade Ina zuba ido naji daga gareka ko iyayanka akan zancen aurenka ammah naji shiru,shekararka 31 a lissafina tsararka daga me 'ya'ya 3zuwa hudu ne a yanzu ammah banji kana lissafin aure ba ,shiyasa lokacin da iyayanka suka zo da zancen turaka kasar turawannan ban so ba haka dai na hakura na barka ka tafi ,Bayan ka tafin ka gama karatun se kirana kayi kace ka fara aiki acan,Bayan ga tsatsonka Nan Nigeria Nan ya kamata ace kana aiki Dan ka tallafi kasarka ,duk naja bakina nayi shiru ,dama Mahaifinka ba son sarauta yake ba shiyasa ya shiga siyasa har ya Kai matsayin da ya Kai a yanzu na  shugaban kasa,Naga dai duk shugabanci ne da mulki da sarauta ,Dan haka ko zuwan Nan da yayi na sana'ar Masa zanyi murabus Nan bada jimawa ba Kuma shi zanba sarautar ya dawo gida yayi na gado in mulki yake so "
Tunda ya fara magana Turaki yake zufa yasan halin me martaba kaifi duya ne,fatansa Allah yasa ba Mata ya Masa ba Dan duk cikin karamin aikin sa ne ,maganar me martaba ta katse Masa tunani Da yace "shiyasa yau kaga gidan cike da mutane akwai 'ya'yan sarakuna da suka zo daga sassa daban daban akwai Kuma na dangi ka diba idan akwai wadda Tama ,idan babu kaje can dangin mahaifiyar ka dake Riyad ka samo ,koma a' in ne ka bincika na baka Nan da wata biyu ka fitar da matar aure,idan Kuma naji shiru daga gareka ,shi ke nuna ka bani zabi ,kaga in na tashi ko hudu ne zan iya hadama Rana Daya, Wata zufa ce ta keto a goshin Turaki ,Dan yasan duk abunda me martaba yace matukar be fidda wadda ze aura ba tsab ne ze Masa auren Mata hudu,shiko me martaba kamar ya Dara ganin yadda zufa ke ketowa jikin jikan nasa Kuma takwaransa ,da gayya ya fada Masa haka dama yayi magana da iyayensa suka ce Masa sunyi maganar har sun gaji se yace ba yanzu ba "Insha'Allah baza akai ga haka ba Allah ya huci zuciyar sarki me adalci" cewar Turaki
Murmushin Manya me martaba yayi ,kafin suka yi sallama ya tashi ya nufi part dinsa tafe yake ya na jefa kafarsa ba tare da kallon gabansa ba.........................✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

NA TAKOحيث تعيش القصص. اكتشف الآن