Part 1

150 3 0
                                    

*TSANTSAR YAUDA😭💔*

*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*

*Sadaukarwa ga Habibaties😂💃🏽ku ji dad'inku Luvly🙌🏽*

*Marubuciyar:-*
*'Kaddarata*
*Babana ne sanadi*
*Nasmarh Neenarh Luv*
*Daren aurena*
*Tambad'add'iya*
*Duniyarmu a yau*

*And now💃🏽*
*Tsantsar Yaudara*

'''Allah ka tsaremun alk'alamina daga rubuta shirme🙏🏽Allah kasa na fara wannan littafin a sa'a👏🏽💥'''

*_Idan har na ga comments mai fasa waya zan fara sako muku littafinmu mai suna ZATO NE! kuma tambad'add'iya zan dinga turo muku shi duk ranar friday💃🏼_*

*Shafi na d'aya*

"Meyasa Abdulrahman da Fad'ima za su min haka, ban cancanci haka daga gurinsu ba, ina son shi sosai amman meyasa shi ya zab'i da ya wulak'anta soyayyar da nake yi masa, ita kuma Fad'ima ta ci amanata duk da ta san na yarda da ita sosai, amman za ta yi min wannan yankan bayan, Eh Rahma meyasa?" Ta k'arasa maganar tare da cukumar Rahman tana girgizata tare da rushewa da wani irin wahalallen kuka, Rahma wacce tausayin Khausar ya gama cika mata zuciya ta ce "Khausar ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai zai huce, ki manta da duk abun da Abdulrahman da Fad'ima su ka yi miki tunda dai yanzu kin san aurensu za'ayi anan da kwana uku masu zuwa, tabbas dan yaudarenki sun riga da sun yaudareki kuma insha Allahu, Allah sai ya saka miki da gaggawa" Rahma tayi maganar zuciyarta nayi mata zafi, haka dai tai-ta rarrashin Khausar har ta samu ta shawo kanta tayi shuru, bacci mai nauyi ya yi awan gaba da ita dan daman rabonta da yin bacci har ta manta, saboda tsantsar yaudarar da Abdulrahman da Fad'ima sukayi mata ta yi matuk'ar firgitata kuma ta tsaya mata a rai.

Wata 'yar gajeriyar yarinya ce sosai kallo d'aya za ka yi mata kasan tana da yawan shekaru kawai dai rashin tsayi ne da bata dashi, bak'a ce amman irin bak'in nan ne da ita da turawa suke kiransa da black beauty, sanye take cikin wasu k'ananan kaya riga da wando pink colour, bata da wani kyau amman muryarta tana da dad'i sosai da jan hankalin mai sauraron muryar, kwance take a kan d'an tafkeken gadon d'akin tana daddanna wayarta da alama chatting ta ke yi, wani lallausan murmushi ne yake bayyana a kan fuskarta, wayarta ce ta fara ringing, wani irin murmushi tayi na musamman idanuwanta na kan screen d'in wayar tana kallon sunab da ta sakawa wanda yake kiranta *Habibina* abin da yake rubuce kenan, ta d'auki kusan minti d'aya tana kallon sunan har kiran ya kusan katsewa tayi saurin d'aga tare da yin sallama "Assalamu alaikum Habibina" Daga chan 'bangaren ya amsa bayan ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya "Wa'alaikumussalam Luvly, wallahi da baki d'aga ba to tabbas zuciyata zata iya bugawa" Mik'ewa tayi daga kwanciyar da tayi ta zauna a kan gadon, fuskarta kunshe da damuwa "Haba Habibina karka ce haka idan zuciyarka ta buga ya ka ke son nayi da raina, kasancewa kai ne rayuwata" Murmushin jin dad'i ya yi tare da cewa "Fad'ima wallahi ina tsananin sonki sosai" Fad'ima ta d'an 'bata fuska tare da cewa "Abdulrahman dan Allah ina son kayi min alk'awarin ba za ka koma wajen Khausar ba, wallahi ina sonka ba zan iya jure rashinka ba" Abdulrahman ya ce "Luvly kenan tabbas duk da nasan cewa abin da mukayi wa Khausar ba mu kyauta mata ba, amman ba laifinmu ba ne laifin zuciyoyinmu ne kuma ni yanzu ke nake so ba Khausar ba, dan haka nayi miki alk'awarin ba zan koma wajenta ba har abada ina yi mata fatan Allah ubangiji ya bata wanda yafi ni komai da komai" Fad'ima ta tab'e baki tare da cewa "hmmm! Allah dai ya bata dai-dai da ita, amman bana tunanin zata auri wanda yafi ka, dan kai d'in d'aya ne tamkar da dubu" Abdulrahman ya yi wani murmushin jin dad'i "Luvly kina fasa min kai fa da yawa, kina sakawa ina ji nafi kowa ne d'a namiji","Mijina idan ban yaba ka ba wa zan yaba, kuma ai gaskiya nake fad'a kai d'in na daban ne","Luvly yanzu dai ya shirye-shiryen biki?" Fad'ima ta ce "Alhamdullahi nan da 'yan kwanaki zan zama matarka kai kuma mijina har na k'osa na ga wannan ranar","Nima haka Luvly" Abdulrahman ya yi maganar yana lumshe ido, suka cigaba da hirarsu ta masoya sun d'auki kusan mintina arba'in sannan daga k'arshe sukayi sallama kowannan su ya kashe wayarsa zuciyoyinsu cike da matsanancin farin ciki.

~WASHE GARI☄️~

"Khausar! Khausar!! Khausar!!!" Rahma ta shigo d'akin Khausar tana kiranta, fitowa Khausar tayi daga toilet idanuwanta sunyi jajur "Na'am Rahma" Ta amsa mata cikin dasasshiyar murya, Rahma ta 'karaso inda Khausar d'in take tana cewa "Khausar ina son ki kwantar da hankalinki dan Allah kin ji 'yar uwata,ba na jin dad'in ganinki cikin irin wannan yanayin zuciyata tana min zafi, ba zan iya jurewa ba Luvly sister" Rahma ta k'arasa maganar cikin rawar murya, Khausar tayi wani murmushin yak'e kafin ta ce "Karki damu 'yar uwata komai ya huce, kawai dai kin san dole naji zafin abin da sukayi min na yarda dasu suka ci amanata, kuma yi min tsantsar yaudarar da ban yi tunanin zasu iya yi min ita ba" Rahma ta rumgume Khausar tana bubbuga bayanta "Ki yi hak'uri kin ji darling sister......................!

Anan zan dasa aya🥲🥲ku yi hak'uri dashi kun ji habibaties gobe zan yi typing me yawa💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

*Please🙏🏽*

*Share👏🏽👏🏽*
*Comments👏🏽👏🏽*

*Mrs breaker🔐❣️*

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now