LAST PAGE

36 3 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA.*

✍🏾'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban

*Last page*

Anan dai Abdurrahman suka raya wannan daren cikin farin ciki mai tsanani.

*WASHE GARI.*

Rahma ce zaune akan gado tana fad'awa Alhaji Lawal gaskiyar shirin da sukayi tace "Kayi hak'uri Amman gaskiyar lamarin shine ni sunana Rahama ba Khausar ba ce naga"....

Cikin bak'in cikin irin k'aryar da tayi masa ya dinga watsa mata wata uwar harara, ya bud'e baki zai yi magana, suka ji an turo kofar d'akin da k'arfi, duk suka kalli kofar dan ganin me shigowar, Mummy ce, kallonsu take hawaye na kok'arin zubo Mata, ganin Rahama da Alhaji Lawal daga su sai kayan bacci, Amman ta maidar dasu, idanuwanta ne suka sauka akan k'afafuwan Rahma da suke kan cinyar Abban, "Amman wallahi Alhaji kaji kunya, karasa da wa zaka kwanta sai da 'yar cikinka" Alhaji Lawal ya kalli inda Rahma take tuno irin yadda tak'i amincewa dashi Daren jiya yay, ita kuma kanta a k'asa tana jin kunyarsa sosai saboda irin k'aryar da tayi Masa da kuma yadda tak'i amincewa dashi, Mummy ganin yadda Alhaji Lawal yake kallon Rahma ransa a b'ace yasa ta saki murmushi tare da cewa "Kodai angon gaba yake yi da amaryarsa daga".... Rahma ta d'ago da sauri tana kallon wajen da Mummy take tace "Gaba Kuma?? Sai kace ba auren soyayya mukayi ba" Mummy tace "Ai shiyasa na ga ya d'aure fuska kamar hadari" Tayi maganar tana dariya, Rahma tace "Ba dole ya d'aure fuska ba, muna cikin soyayyarmu zaki shigo sai kace wacce bata san abin da take yi ba" Mummy cikin zafin nama ta nufo gurin da Rahma take da niyyarta koya Mata hankali, Alhaji Lawal ya daka mata tsawa Yana cewa "Keee Hajiya ki gaggauta fita daga d'akin nan kafin nayi miki abin da Baki yi zato ba" Irin yadda yay magana yasa Mummy tayi saurin fita daga d'akin tana surutai ciki-ciki.

Alhaji Lawal ya juyo kan Rahma wacce jikinta sai b'ari yake yace "Ke Kuma tunda mak'aryaciya ce kuma munafuka duk sanda kika buk'aci takaddar Sa"......Rahma ta d'ago tana zubar da hawaye tace "Kayi hak'uri, wallahi akwai dalilin da yasa nayi hakan, kai ma kasan ina sonka, da ba na sonka ba zan yarda a d'aura mana aure ba, zance na fasa amman ban yi hakan ba, ka tsaya ka saurareni, abin da yasa nayi hakan saboda ina son kasan gaskiyar idan ka na da ra'ayin zama da ni shikenan, ni a shirya nake da na baka duk abin da ka ke buk'ata" Ajiyar zuciya Alhaji Lawal ya sauke "To shikenan Rahma na yarda da ke kuma nima ina sonki sosai" Rahma tayi murmushi zatayi magana sai jin k'arar bindiga sukayi, a firgice Rahma tace "Honey 'yan fashi ne suka shigo gidan, innalillahi wa inna ilaihi raju'un" Hannunta ya kama suka fita a falo sukayi kicifus da wasu d'irka-d'irkan maza guda biyar masu ji da k'arfi, "Wayyoo sun kashe Fad'ima" Rahma ta fad'a da k'arfi tana nuna wajen da Fad'ima take kwance kallo d'aya zaka yi mata kasan ta mutu ga jini sai malala yake a k'asa, Sojojin gidan ne suka shigo jin harbin da aka yi, "Meyasa ku ka kashe min yarinya?" Alhaji Lawal yay maganar hawaye na zuba daga cikin idonsa, d'aya daga cikin mazan wanda da alama shine oga yace "Ni sunana Goga yarinyarka ita da aminiyarta wacce ita muka fara shek'ewa sun ci amanata, kuma duk wanda ya ci amanar Goga tabbas wannan shine hukuncin da nake yi masa" Cikin izza yake magana ko kad'an babu alamar tsoro a tattare dashi, Alhaji Lawal ya kira sunan d'aya daga cikin sojojin "Captain Sani" Cikin kakkausar murya yay maganar, Captain Sani ya sara masa tare da cewa "Naam sir" Alhaji Lawal yace "Ku tafi dasu gidan sojoji ku tabbatar kun hukuntasu kamar yadda suka yi wa yarinyata" Captain Sani da sauran muk'arrabansa suka tisa kan su Goga.

Alhaji Lawal ya kalli wajen dasu Mummy da Rahma suke sun rumgume juna suna rera kuka, shima zama yay a kan kujera yana yin kukan dan a duniya yana son Fad'ima sosai.

*BAYAN SADAKAR UKUN FAD'IMA😢*

Khausar ce zaune akan kujera kusa da Rahma da yake dare ne kowa ya watse daga gidan gaisuwar ya rage Rahma, Khausar sai kuma Mummy.

"Dan Allah Khausar ki yafe mana ni da Fad'ima, nasan wannan duk alhakinki ne yake ta bibiyarmu"Mummy tayi maganar tana goge hawaye fuskarta.

Khausar tace "Haba Mummy ni wallahi tuntuni na yafe muku dan Allah ki daina kukan nan haka".

Rahma tace "Karki damu Mummy Khausar ta yafe muku, Allah ya yafe mana gaba d'aya".

Mummy tace "Amin nagode sosai".

Sai wajen goma Abdurrahman ya zo ya d'auki Khausar suka tafi gida.

     ****   ****   *****

A yau Alhaji Saleh ya yanke shawarar aurar dasu Meenal da kuma Yayanninta, anyi shagali sosai dan waje aka kama babba, ana fitowa daga wajen fatin kowannansu ya d'auki amaryarsa ya tafi da ita gidansa, dan umarnin Abba ne baya son a kai kowacce dukkansu angoyansu su tafi dasu.

      ****   ****  ****

Khausar ce kwance akan gado ga wani k'ato ciki,wanda zan iya cewa haihuwa yau ko gobe, Abdurrahman cikin tsokana yake ce mata "Maman biyu da fatan babyna yana lafiya??" Hararar wasa ta watsa masa "Babynka gashi nan yana ta ba ni wahala" Abdurrahman yace "Ayyah sorry dear" Khausar ta rik'o hannun Abdurrahman da k'arfi tana cewa "Wayyoo cikina, ka taimaka min cikina" Abdurrahman yay saurin ya d'aukarta cak, ya fita daga d'akin wajen da motarsa yake ya nufa tare da saka Khausar a bayan motar suka nufi asibiti, suna zuwa nurses suka d'auketa a gadon d'aukar marasa lafiya suka nufi labour room da ita, ko awa d'aya ba'ayi da shigar da Khausar Labour room ba, wata nurse ta fito rik'e da jaririya a hannunta ta kalli Abdurrahman tace "Congrats matarka ta haifu lafiya".

Abdurrahman ya karb'i jaririyar yana cewa "Ma sha Allah! Kamanninmu d'aya da ita, dole na baki tukuci" Hannunsa ya saka ya zaro 'yan dubu-dubu wanda zasu iya kai wa dubu hamsin ya ba wa nurse d'in ta karb'a tana godiya, yace "Zan iya shiga na ganta??" Nurse d'in tace "Eh mana zaka iya shiga" Abdurrahman ya bud'e kofar d'akin ya shiga ido biyu sukayi da Khausar ya sakar mata murmushi ita ma Murmushin tayi masa, zama yay kusa da ita yana cewa "Nagode sosai sweetheart Allah yay miki albarka" Khausar tace "Amin".

Doctor Wasil ne ya shigo bayan ya yi wa Khausar da Abdurrahman barka ya basu takaddar sallama, Haka Abdurrahman ya rik'e jariryar da Khausar suka shiga mota, kai tsaye gidansu ya nufa da ita, bayan ya kira Abba ya fad'a masa Khausar ta haihu shine yace ya kawota gida, dan a kula da ita har zuwa ranar da zatayi arba'in.

Suna shiga gidan ya tarar da Aunty Naja'atu da kuma Mummynsa suna tsaye suna jiran shigowarsu, Abdurrahman ya fito yana kallon mahaifiyarta sa da ido a zuciyarsa yana cewa "To yaushe Mummy ta dawo??" Ba zai iya tambayarta ba, dan yanzu sai ta hayyak'o masa dan haka ya ja baki yay shuru, Mummy ta karb'i jaririyar "Sannu kinji Khausar" Murmushi Khausar tayi tace "Yauwa Mummyna" Aunty Naja'atu ta kama Khausar suka shiga gida, Abdurrahman kuma mota ya shiga dan yaje ya kwaso kayan Khausar, ya kawo mata.

     *****   *****   *****

A yau akayi sunan Khausar yarinya ta ci sunan kakarsu Abdurrahman Hajara, dukka familyn sun zo an ci an sha, anyi shagali sosai inda na hango habibaties d'ina su ma suna cin abincin suna, sai wajen k'arfe takwas taron sunan ya watse, kowa ya tafi gidansa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Khausar tana shan kulawa sosai a gidansu Abdurrahman har wani kyau da k'iba tayi, a yau ne suka cika kwana arba'in da haihuwa dan haka Mummy ba dan ta so ba suka tattara Khausar suka komar da ita gidan mijinta.

Aunty Rahma ta haifi d'anta namiji yau farin ciki wajen  Alhaji Lawal baa magana, ranar suna anyi bidiri sosai an zubar naira sosa a sunan.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiyarwa wannan familyn cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Meenal, Fanal da Finat duk sun haihu kuma yaransu mata ne dukkansu kuma sunan sirikansu aka sakawa yaran, Matar Abdulfatah ta haifi namiji ya saka sunan kakansa Tahir, matar Abdulaziz kuma 'yan biyu ta haifa aka saka sunan Mummy da kuma Abba, sai kuma matar Abdullahi ta haifi mace ya saka sunan sirikar Maimuna.

Hannayensu rik'e da juna suna yi wa junansu kallon soyayya, Abdurrahman tace "Ina sonki Sweetheart" Khausar ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima ina sonka sosai mijina".

*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFIN NA TSANTSAR YAUDARA ME CIKE DA DARUSAN RAYUWA, YAUDARA TSAKANIN AMINTATTUN K'AWAYE*

*SAI MUN HAD'U A CIKIN SABON LITTAFINMU MAI SUNA,WURIN DABA ƘASA.. (Anan ake gaddamar kokawa)*

*LOVE D'IN LOVE CE😍MRS BREAKER❤️🥰*

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now