PART 13

56 3 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA.*

*✍🏽'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban*
                  *(MRS BREAKER🤗)*

*Sadaukarwa ga habibaties💃🏼💞*

*Masu wattpad ayi following d'in dijartyy Mrs BK😰*
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=QUEENNASMERH08&wp_originator=Dc2LE0SO%2FHWLF8SESpNia9X2tmmDswdF2yVF%2FzkeABanEPiB8ElGpzFZb%2BI0yUUGqaOTCo28dfUw3u4i2mEF9RHgjz8oxYHgjF%2Fb0pqg0Ccscg9BjMmx%2BSBdzfiFB2K%2B

*Shafi na 13*

Kwance yake a kan d'aya daga cikin kujerun d'akinsa zuciyarsa cike take da tunanin Khausar, ya san komai zai yi Khausar ba za ta tab'a yarda ta aureshi ba, tunda tayi niyyar auren Abbansa dan ta d'auki fansar abin da yay mata, wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo masa, a hankali ya saka hannunsa ya shiga goge hawayen zuciyarsa jinta yake kamar zata buga, a hankali ya furta "Ya Allah ka kawo min d'auki da gaggawa" Ji yay ance "Amin" Da sauri ya tashi zaune yana kallonta Minal ce ita ma idanuwanta sun ciko da kwalla, "Sweet sister meya sameki?? Waya tab'a ki??" Abdurrahman yay maganar cikin tashin hankalin ganin auta na kuka, Minal ta ce "Yaya ni kawai tausayinka nake ji, wannan shegiyar ta rud'eka ka rabu da Aunty Khausar ita kuma gashi bata da hali, yanzu kuma Abbanmu ne zai aureta ina tunanin sauran sati biyu a d'aura auren" Hawaye ne suka fara zuba daga cikin idanuwan Abdurrahman ya ce "Minal wallahi ni kai na ban san meyasa nayi wa Khausar haka ba, ban san lokacin da nayi mata haka ba, ni dai na san ina tsananin sonta amman rana d'aya na tsinci kai na da ina jin haushinta sosai kuma ina jin wata sabuwar tsanarta na ratsa cikin zuciyata" Minal tace "Yaya ka cigaba da addu'a Nima kuma zan ta ya ka, insha Allahu Aunty Khausar kai zaka aureta" Kallon Minal yay tare da yin wani irin murmushi me ciwo yace "Minal kenan wannan ba zai tab'a yiyuwa ba saboda Abbana ne zai aureta ni kuma ba zan tab'a yin soyayya da wacce mahaifina zai aura ba, dan ita kamar mahaifiyata ce" Minal tace "Yayana insha Allahu, kai zaka auri Khausar, tabbas za'ayi auren Abba nan da sati biyu Amman bada Khausar ba" Kallon mamaki Abdurrahman yake bin Minal dashi ya bud'e baki zai yi magana, Minal ta fita daga d'akin da sauri, zamewa yay ya kwanta a kan kujera tare da lumshe ido, a hankali bacci me nauyi yay awan gaba dashi.

     ***  ***  ***

Wata mota ce mai numfashi ta danno cikin gidan Alhaji Lawal a wajen da aka tanada dan ajiye motoci yay parking ya fito DPO ne, sanye yake da kayan 'yan sanda a jikinsa, d'aya daga cikin masu aikin gidan ne ya zo da gudu ya tsugunna a gabansa yana cewa "Ranka ya dad'e Alhaji ya ce idan ka zo ayi maka iso zuwa bak'i" DPO yay murmushi tare da cewa "To muje" Me aikin gidan yana gaba shi kuma DPO yana biye dashi a bayansa har suka isa falon bak'in, DPO ya nemi kujera ya zauna, shi kuma me aikin ya fita da sauri.

Ko minti biyar DPO bai yi a zaune ba, Alhaji Lawal ya shigo falon fuskarsa d'auke da murmushi, Zama yay yana cewa "DPO na zaunar da ka na ta jira ko??" Cikin ladabi ya ce "A'a wallahi ranka ya dad'e babu damuwa" Bayan sun gaisa cikin girmamawa DPO yay shuru yana tunanin ta inda zai fara yi wa Alhaji Lawal magana, Alhaji Lawal ya lura da hakan yay gyaran murya tare da cewa "DPO lafiya kuwa?? Fad'i abun da yake tafe da kai" D'ago kai yay yana kallon Alhaji Lawal fuskarsa cike da damuwa "Ranka ya dad'e nasan wannan maganar da zan yi zatayi matuk'ar girgiza ka, Amman kayi hak'uri zan fad'a maka ne dan ka d'auki mataki da wuri dan nasan baka san ni ba" Yay d'an yi shuru na minti goma sannan ya cigaba da cewa "Yarinyarka Fad'ima tana safarar miyagun kwayoyi"

Wata irin zabura Alhaji Lawal yay jikinsa sai rawa yake yi "Fad'imar ce take yin wannan muguwar harkar??" DPO ya ce "Tabbas kuwa ita ce kuma Ina da shaidar da zata sa ka tabbatar da hakan" Hotunan da Abdulfatah ya tura masa ya lalubo ya mik'awa Alhaji Lawal wayar ya shiga kallon hotunan idanuwansa na zubar da hawayen bak'in ciki, ya mik'a masa wayar cikin rawar murya ya ce "Nagode sosai DPO da baka zo ka fad'a min ba da ba zan tab'a sani ba" Wayarsa ya zaro tare da mik'awa DPO ya ce "Tura min hotunan" Ba musu DPO ya karb'i wayar ya tura Masa hotunan gaba d'ayansu, bayan ya gama ya mik'e Yana cewa "Alhaji nagode sosai" Yay maganar yana mika Masa wayarsa, karb'a yay bai iya cewa komai ba.

DPO yay masa sallama ya fita daga falon, Alhaji Lawal zubewa yay a kan kujera tare da rik'e kai yana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raju'un" Abun da yay ta maimaitawa kenan, Mummy ce ta fad'o falon bak'in ko sallama ba ta yi ba ta ce "Me na ga wanchan DPO d'in yake yi a gidan nan??" Wayarsa ya bud'e ya lalubo hotunan ya mik'a mata, wata muguwar harara tayi masa tare da warce wayar ta shiga kallon hotunan, jifa tayi da wayar tana yin wani irin huci tare da cewa "Wannan wane irin sabon munafirci ne kuma, wato sharrin ma da ake yi wa".......... Cikin muryar tsawa Alhaji Lawal ya ce "Keeeee! Idan baki da hankali to ki gaggauta neman hankali ki saka a kanki, ba na son hauka da jakanci ohhh wato ke kike goya mata bayan abubuwan da takeyi ko?? Ace wai niii Lawal nice 'yata take safarar miyagun kwayoyi to wallahi daga ke har ita sai na koya muku hankali zaku san dawa ku ke magana".

Fuuuuuuuuuu! Ya fice daga d'akin cikin zafin rai, waje ya fita yana zuwa wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya shiga motarsa ya figeta da k'arfi har yana kok'arin buge mai gadi.

Zubewa Mummy tayi a k'asa tare da dora hannunwata a kai "Na shiga uku Fad'ima kin cuceni kin yaudareni ashe mugun halinki kenan shine kika b'oye min" Wani tunani tayi da sauri ta tashi tare da goge hawayenta ta fita da sauri ta nufi waje, motarta ita ma ta shiga ta ja ta bi bayan Alhaji Lawal.

Asibitin da aka kwantar da Fad'ima anan Alhaji Lawal yay parking da yake lokacin da aka kai Fad'ima Mahaifiyarta ta kirashi ta fad'a masa sunan asibitin yana shirin zuwa kuma DPO ya kirashi ya ce zai zo, fitowa yay daga cikin motarshi a dai-dai lokacin kuma Mummy ita ma tayi parking ganin Alhaji yasa gabanta ya tsananta bugawa ta san tabbas idan har yaje d'akin da Fad'ima take zai iya kasheta, ta san halinsa sosai musamman idan ranshi ya b'aci zai iya yin komai.

Da sauri ta nufi d'akin da aka kwantar da Fad'ima, idanuwan Alhaji Lawal suka sauka a kanta bin bayanta yay shima da sauri daman bai san d'akin ba ya tsaya yana tunanin ina zai je, Mummy bata kula da Alhaji Lawal yana biye da ita a baya ba har sai da suka zo d'akin tana shirin shiga yay saurin fisgota yay wurgi da ita ya shiga d'akin babu kowa dan Hajiya Sumayya suna kawota ta fita dan akwai wajen da zataje, Alhaji Lawai bai yi wata-wata ba ya shiga dukanta ta ko ina tun tana iya ihu har ya zama bata iya wa, sai da Alhaji Lawal ya farfasa mata jikinta saboda dukan da yakeyi mata ba na wasa ba ne, da gaske yake yi mata dukan, Mummy ta rik'eshi da k'arfi wanda ita kanta bata san tana dashi ba sai yau "Haba ka daina dukanta so ka ke ka kasheta, bayan kasan ita kad'ai ce 'yarmu" Alhaji Lawal ya juyo cikin zafin nama ya fara magana da cewa "Ai na fison na kasheta domin wallahi da nasan wannan hatsabibiyar yarinyar zaki haifa da tun ranar da likita ya shaida min kina d'auke da ciki zan san duk yadda nayi cikin ya zube domin wannan yarinyar ba alheri bace a garemu" Kuka Mummy ta shiga yi tana kalli Fad'ima wacce dak'yar take iya numfashi "Fad'ima menene ba ma yi miki a duniyar nan da kika zab'i da ki ganmu muna cikin bak'in ciki sayar da miyagun kwayoyi" Tayi maganar tana kuka mai tsanani chan ta share hawayen ta cigaba da cewa "Fad'ima tsakanina da ke sai da nace Allah".........

"Haba Hajiya karki yi mata Allah ya isa ya addu'ar shiriya ya kamata kiyi mata" Doctor Ma'aruf wanda yake tsaye jikin kofar shigowa yay maganar cikin taushin murya, Alhaji Lawal ya ce "To doctor ai gwara tayi mata Allah ya isan domin ban ga amfanin wannan yarinyar a tattare damu ba" Doctor Ma'aruf ya zauna tare da yi musu maganganu masu dad'i da kuma nuna musu illar da Allah ya isa zata jaa a rayuwar Fad'ima har sai da ya tabbatar sun dawo cikin hayyacinsu, sannan ya mik'e ya kira wasu nurses suka zo aka d'auki Fad'ima aka kaita d'akin taimakon gaggawa.

*BAYAN SATI D'AYA*

A yau ne za'a d'aura auren Alhaji Lawal da Rahma da kuma Alhaji Saleh da Khausar, Abdurrahman ya shirya cikin wasu fararan kaya yayi kyau sosai duk da cewa zuciyarsa tana yi masa wani irin bugu amman ya kamata ta hak'ura da Khausar dan kuwa ba za ta tab'a zama mallakinsa ba, Fitowa Falon yay inda ya tarar da mahaifin nasa da sauran 'yan uwansa duk sun shirya zasuje d'aurin auren, murmushi yay musu bayan ya gaisar da mahaifin nasa ya kalli Abdulfatah wanda sai kallonsa yake yana murmushi ya ce "To malam d'an sa ido meya faru?? Ka ke yi min wannan kallon kamar na ci maka bashi" Dariya Minal tayi sosai ta ce "Kai dai yaya ka daina magana ku tafi d'aurin aure, amman fa karka manta ka zo min a alewar d'aurin aure da kuma goro" Abdurrahman ya ce "Goro kuma?? Sai ka ce tsohuwa" Dariya sukayi gaba d'aya Abba ya ce "Ka ga Abdurrahmanu tafi karmu makara, dan kasan auta da shegen surutu kamar aku"

Haka suka fita daga gidan motoci guda uku suka tafi dasu, inda suna zuwa masallacin suka had'u da Kawu tare suka shiga cikin masallacin bayan anyi addu'o'i Liman ya ce "An daura auren Alhaji Lawal da Rahma  da kuma.........................😂😂😂😂

*_HABIBATIES WA KU KE GANIN KHAUSAR ZATA DAURA???😂😂😂👩🏼‍🦯👩🏼‍🦯_*

*SHARE👏🏽👏🏽👏🏽👯🏽‍♀️👯🏽‍♀️*

*MRS BK🤗❤️*

TSANTSAR YAUDARAOnde as histórias ganham vida. Descobre agora