Part 6

39 2 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA😭💔*

*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*
08122188717

*Sadaukarwa ga habibaties👯🏽‍♂️💃🏼*

_Ku cigaba da koyawa d'an gatanku yawo, dan yasan ko ina a duniya❤️🚴🏽‍♀️_

*Shafi na 6*

Haka ta mik'e ta shiga gida adaddafe a tsakar gida ta zube tana cigaba da kuka, Rahma ce ta fito daga d'akinta ta k'araso gurin da take tana cewa "meya faru sister mie" Khausar cikin shash-shekar kuka ta ce "Sister mie, na shiga uku ya suke so nayi da rayuwata" Rahama ta ce "Su waye??? Meya faru??" Khausar ta fad'a mata duk yadda sukayi da Alhaji Saleh da Alhaji Lawal, Ai Khausar na Kai wa k'arshen maganarta Rahma tayi wata iriyar gud'a tare da cewa "Alhamdulillah! Allah kai ne abin godiya burina yana daf da cika, Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!!!" Khausar ta bi ta da kallo cike da mamakin meyasa Rahman take murna, "Sister mie meya faru?? Meyasa kike murna?? Ku dai Baba ne zai dawo yau" Rahma ta kwashe da wata iriyar dariya ta ce "Ai wannan labarin da ki ka kawo min, shine ya saka ni murna da gaba d'aya jina nake babu dad'i amman yanzu baki ji yadda nake ji ba, zuciya ta gama cika da farin ciki" Khausar ta ce "Haba sister mie maimakon ki ta ya ni jimami shine zaki".......... A zababben marin da Rahma ta wanketa dashi ne yasa tayi shuru tare da dafe kuncinta, tana wani irin gunjin kuka mai ban tausayi "Idan kin manta bari na tuna miki, wannan shegen yaron Abdurrahman d'in da wannan 'yar iskar yarinyar Fad'ima sunyi miki tsantsar yaudarar da ban tab'a jinta a tarihin rayuwata ba, dan haka yanzu lokacin ramuwa ne, dole muyi amfani da wannan damar da ta zo domin mu kuntata musu fiye da yadda sukayi mana" Khausar ta d'ago dak'yar tana kallon Rahman cikin shash-shekar kuka ta ce "To ya kike so nayi, so ki ke na auresu duka biyun ne??" Rahma ta ce "A'a mutum d'aya zaki aura, kuma ba kowa ba ne sai Abban Abdurrahman ni kuma zan auri Abban Fad'ima" A firgice Khausar ta fiddo ido tana kallonta "Me ki ke cewa?? Dan Allah sister mie karki yi haka, dan Allah na rok'eki dan girman Allah ni na ji zan auri Abban Abdurrahman amman ni ba na so ki saka kanki a cikin wannan cakwakiyar kin san ina sonki sosai dan Allah kar".............. Hannu Rahma ta saka ta toshe mata bakinta tana cewa "Meyasa ki ke so na janye auren Abban Fad'ima???? To idan kin ga ban aureshi ba to tabbas mutuwa nayi, kuma zan je masa a matsayin Khausar ba zai tab'a gane cewa ba Khausar ba ce kamanninmu d'aya da ke, ko Babanmu baya iya gane mu,dan haka zan yi amfani da wannan wajen ganin na aureshi idan yaso daga baya ya san komai" Khausar tayi murmushin jin dad'i "Wallahi Sister mie har na ji wani irin dad'i, da gaba d'aya na tsorata da lamarin" Rahma ta mayar mata da martanin murmushin na ta "Haka nake son ji Sweet sistoo" Haka suka shiga d'akin Rahma tana cigaba da tsara musu yadda zasu azabtar da su Fad'ima, ita ma Khausar tana kawo shawarar yadda Rahma zatayi kar Alhaji Lawal ya san ba ita ba ce.

_To fa habibaties Abdurrahman da Fad'ima sun d'ebo ruwan dafa kansu😂_

*ALHAJI SALEH👩‍❤️‍💋‍👩💔*

Alhaji Saleh tunda ya koma gidansa ya shige b'angarensa, bedroom d'insa ya shiga bayan ya rage kayan jikinsa ya kwanta tunanin Khausar da irin yadda ya ga yarinyar ta gama had'uwa ta ko ina ya shiga yi, nutsuwa, kyau, hankali, addini,uwa uba kuma tarbiyya duka Khausar ta had'a wad'annan abubuwan, ya san idan ya aureta tabbas ba zai tab'a yin danasani ba, Wani irin lallausan murmishi ya shiga saki a hankali ya fad'i sunan Khausar tare da sauke ajiyar zuciya, lumshe ido ya yi ko minti d'aya bai yi ba bacci mai nauyi ya yi awan gaba dashi, haka ya yi baccin cike da mafarfakai kala-kala akan Khausar masu dad'i, Hajiya Saratu ce ta shigo bedroom d'in ganinsa yana bacci takaici ya cikata, "Wato ma kai ko a jikinka baccinka ma ka ke yi, wallahi zaka gane yanzun nan kuwa" Ruwan gora ta d'auko a cikin fridge mai sanyi ta bud'eshi ta nufi gurin da Alhaji Saleh yake kwance ta shek'a masa a jikinsa, A firgice ya tashi tare da cewa "Ya subhanallahi" Ya yi maganar yana kallon Hajiya Saratu, "Saratu meye haka?? Baki da hankali ne?? Ni fa mijinki ne amman saboda baki san darajar aure ba, shine kika shek'a min ruwa a jikina" Cikin hasala Hajiya Saratu ta ce "Saleh ai ni ban ga amfanin auren miji irinka ba, me ka tab'a yi min banda bak'in ciki da kullum ka ke kunsa min a zuciyata, kuma da ka ke cewa ban da hankali A'a dawanau ce k'arewar rashin hankali kenan" Alhaji Saleh da tuni ransa ya gama b'aci da maganganun matar ta sa, idanuwansa gaba d'aya sun chanza launi daga fari zuwa ja, " me ka tab'a yi min banda bak'in ciki da kullum ka ke kunsa min a cikin zuciyata" Wannan kalmar ita ce ta fi tsaya masa a rai, ace duk irin kyautatawar da yake yi mata shine yau take jifansa da wad'annan maganganun, "Saratu ni kike jifa da zafafan maganganun nan???" Wata iriyar dariya tayi ta ce "To wanene kai d'in da ba zan gaya maka magana son raina ba??? Saleh tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin uban da yake yi wa d'ansa bak'in cikin kar ya yi aure ba sai kai, Saleh kai azzalumi ne, Saleh kai mugu ne wanda ba ya son ganin farin cikin yaransa da na matarsa" Tana kai wa k'arshe a maganarta ta fita fuuuuuuuu! Daga b'angaren na sa, Alhaji Saleh hawaye ne ya shiga zubo masa amman ya gogeshi, ya tashi ya shiga toilet ya yi wanka ya fito wata tsadaddiyar jallabiya ya saka kofi colour, bayan ya chanza bedsheet d'in gadon ya kwanta zuciyarsa nayi masa zafi, tabbas yau Saratu tayi masa abin da tun da yake a rayuwa babu wanda ya tab'a yi masa, a wani b'angaren na zuciyarsa idan ya tuno Khausar sai ya ji sanyi a ranshi kad'an, fargabarsa d'aya kar Khausar d'in ta nuna bata son aureshi, idan hakan ya faru bai san yadda zai yi da ransa ba, bacci ne ya k'ara d'aukarshi mai nauyin gaske.

*FAD'IMA😂😰*

Wata nurse ce ta fito daga d'akin da aka shiga da Fad'ima gaba d'aya jikinta a sanyaye yake, da sauri Hajiya Laure ta sha gabanta tana tambayarta "Ya jikin yarinyata?? Ta farfad'o dai ko???" Dakyar nurse d'in ta iya cewa "Ki yi hak'uri Hajiya, Allah ya karb'i abun sa" Wani irin wawan haushi Hajiya Laure ta kaiwa nurse d'in tare da cukumarta tana cewa "Kun kashe min yarinyata, to wallahi kuma ba zan barku ba sai na kasheku" Haka Hajiya Laure ta shiga dukan nurse d'in ba ji ba gani, dakyar wasu nurse suka zo suka kwaceta daga hannun Hajiya Laure, ai kuwa kafin ace me, fuskar wannan nurse d'in ta hau sosai bakinta ya kumbura suntum, Hajiya Laure tayi kan nurses d'in da niyyar ta saka musu duka, gaba d'ayansu suka sa gudu, suka shiga cikin wani d'aki suka kulle, Hajiya Laure ta shiga buga kofar d'akin kamar zata karya, Doctor Hisham ne ya 'karaso gurin da take yana cewa "Haba Hajiya Laure ba girmanki ba ne ki dinga yin irin haka, kuma Fad'ima ba mutuwa tayi ba kawai dai doguwar suma tayi, yanzu haka ta farfad'o gaba d'ayanmu munyi tunanin mutuwa tayi saboda yadda muka ga bata numfashi kusan kwana biyu babu alamar cigaba" Hajiya Laure ta juyo tana yi masa wani irin kallo ta ce "Allah ya taimakeku da ace yarinyata ta mutu da kun gane dan ba zan yarda ba, kun san baku kwarai a aikinku ba, zaku fara aikin asibiti banzaye kawai" Tana gama magana ta huce ta nufi emargency room, Doctor Hisham ya girgiza kai tare da cewa "Allah ya kyauta" Daga nan ya koma office d'insa, yana mamakin irin haukar Hajiya Laure duk da kasancewar mijinta fitatcen d'an siyasa wanda gomnati suke ji dashi sosai, Hajiya Laure kuwa tana shiga d'akin ta ga Fad'ima zaune a kan gado ta jingina da k'arfen gadon idanuwanta a rufe, k'arasawa gurin da take tayi ta rumgumeta sosai tare da fashewa da kuka "Haba Fatiti meyasa za ki yi min haka, kin san dai ni ba zan tab'a yarda a hanaki cikar burinki ba, ki kwantar da hankalinki ni nasan me zan yi kinji ko" A hankali Fad'ima ta bud'e ido tana kallon mahaifiyar ta ta, "Mummy babu abin da za ki iya yi Abba ya gama yanke hukunci, ba zan tab'a auren Abdurrahman ba" Ta k'arasa magana tana kuka "Wa ya gaya miki ba za ki aureshi ba?? To idan kin ga baki aureshi ba to tabbas shine ya mutu" Fad'ima ta ce "Mummy ki daina yi wa Abdurrahman fatan mutuwa dan da ya mutu gwanda ni na mutu" Da sauri Hajiya Laure ta ce "Karki k'ara fad'an haka, ba za ki mutu yanzu ba insha Allahu" Fad'ima dai tayi shuru ba tare da ta ce komai ba, haka dai Hajiya Laure tayi ta janta da hira tare da yi mata alk'awarurrika a kan aurenta da Abdurrahman har Fad'iman ta sake, tana jin wani irin sanyi a ranta jin irin alk'awarin da Mummyn na ta tayi mata.

*BAYAN KWANA D'AYA🤸🏽‍♀️*

Yau ne ya kama su Alhaji Saleh da Alhaji Lawal zasu dawo wajen Khausar, Misalin k'arfe shida da rabi na yamma Rahma da Khausar sun sha kwalliya kamar wad'anda zasu je biki komai nasu iri d'aya, Sai yanzu na k'are musu kallo, baki na saki ina kallon ikon Allah sabida irin tsantsar kamar da sukayi kamar an tsaga kara, ba za ka tab'a iya banbance su ba, dan wasu 'yan unguwar na su ma 'yan biyu suke ce musu "Sister mie kin yi kyau sosai fa" Khausar tayi maganar tana kallon Rahma, Kallonta Rahma tayi ta ce "Ai ban kai ki ba 'yan biyu ta" Dariya Khausar tayi sosai tana cewa "Wato kin d'ana abin da 'yan unguwar nan suke fad'a mana kenan" Rahma ta bud'e baki za ta yi magana, suka ji sallamar wani yaro "Assalamu alaikum" Gaba d'ayansu suka amsa tare da fitowa daga d'akin da suke "Wa'alaikumussalam" Yaron ya ce "Wai an ce 'yan uwa Khausar ta zo inji Alhaji Saleh" Khausar ta kalli Rahman tana murmushi ba tare da ta ce komai ba, Rahma ce ta ce wa yaron ya je ya ce tana zuwa, yaron ya fita da sauri Rahma ta kalli Khausar tare da cewa "To ki je sweetynki na kiranki" Dariya Khausar tayi tana cewa.............🤸🏽‍♀️

*HABIBATIES SHIN LITTAFIN YANA YIN CITTA KUWA???IDAN EH NE AMSARKU TO KUYI SHARE D'INSA ZUWA WASU GROUPS D'IN SABODA ALLAH👏🏽*

*#Share*
*#Comments*
*Mrs Breaker*

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now