PART 9

40 5 4
                                    

*TSANTSAR YAUDARA*

✍🏾'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban
08122188717

*Sad'aukarwa ga habibaties💃🚴🏽‍♀️*

Kuyi following dina a Wattpad.
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=QUEENNASMERH08&wp_originator=Dc2LE0SO%2FHWLF8SESpNia9X2tmmDswdF2yVF%2FzkeABanEPiB8ElGpzFZb%2BI0yUUGqaOTCo28dfUw3u4i2mEF9RHgjz8oxYHgjF%2Fb0pqg0Ccscg9BjMmx%2BSBdzfiFB2K%2B

Shafi 9

Ta nufi motarta ta shiga, ta jingina da kujerar motar tana saukar da numfashi sama-sama, wayarta ce ta shiga ruri da sauri ta d'aga ganin mai kiran nata "Hajiya gashi nan mun taho da kayan aiki Amman 'yan sanda sun kama mu, sun kwace komai suna shirin tafiya damu" Fad'ima cikin fushi ta ce "Ba wa d'aya daga cikin 'yan sandan wayar" Babu musu ya mik'awa wani d'an sandan da ya fuskanci kamar shine babba a gurin wayar ba tare da ya ce komai ba, ya karb'i wayar tare da karawa a kunnansa bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Fad'ima cikin tsawa ta fara yi Masa magana.

"Ku wane irin jakuna ne, ku har kun isa a kawo min kaya kuce zaku kamashi, to idan Baku San kayan waye ba yanzu Ina son kasan kayan Fad'ima Lawal Abdulkarim ne, Kuma yanzunnan zan iya sakawa gaba d'ayanku a sauke ku daga aikinku banzaye mahaukata kawai"

D'an sandan jin wacece yasa ya shiga ba ta hak'uri dan kuwa yasan waya kawai za ta yi a sauke su daga aikinsu, ya mik'awa yaron nata waya tare da umartar sauran 'yan sandan da su barsu su tafi tare da kayan, yaran Fad'ima suka shiga motar da suka d'auko kayan maye iri-iri wasu ma ban tab'a ganinsu ba, sai yau.

Bayan sun ja motar sun tafi d'an sandan ya shiga mamakin kenan daman haka halin Fad'ima yake bayan cin amana ma, har da siyar da kayan maye take yi, anya Alhaji Lawal ya san abin da take yi kuwa??? Ya san halin Alhaji Lawal sosai da sosai tabbas bai San abin da tantiriyar 'yar ta sa take shukawa ba, Kuma insha Allahu shi zai yi kok'arin ganin ya sanar dashi komai dan ya d'auki mataki tsatstsaura a kan ta.

Da wanda shawarar da ya yanke ya samu ya koma cikin motar 'yan sanda ya zauna, ya cigaba da cin abincin da yake yi.

*ABDURRAHMAN*

Tuk'i yake yi amman kwata-kwata hankalinsa baya kan tuk'i, gefen titi ya tsaya bayan ya yi parking ya zaro wayarsa daga aljihunsa ya shiga kiran number Fad'ima, ringing d'aya-biyu ta d'auki wayar tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum habibina"

Abdurrahman cikin sanyin murya ya amsa mata sallamar "Wa'alaikissalam habibatyy ya kike"

Fad'ima ta ce "Lafiya lau da fatan Kai ma haka"

Abdurrahman ya ce "Eh lafiya nake"

Fad'ima ta ce "Abdurrahman yau insha Allahu za'a saka ranar Abbanmu da Khausar, Khausar ta ci amanata bai kamata ta auri Abbana ba"

Wata iriyar zabura ya yi tare da yin magana cikin wata murya mai nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki "Khausar ce zata auri Abba, lallai wannan yarinyar ban tab'a tunanin bata da hankali ba sai yau, Dan Allah ki kwantar da hankalinki zan je na sameta dole ta janye auren nan" Fad'ima tayi wani murmushin jin dad'in maganar Abdurrahman dan ta san Khausar tana sonshi sosai Kuma idan yace ta janye dole zata hak'ura domin ganin ba ta b'ata masa rai ba, dan idan ta ga yazo wajenta zata iya yin tunanin ko dai dawowa yake son ya yi.

Habibaties ku ji min shashashar nan😂kuna ganin Khausar zata kalli Abdurrahman ma idan yaje barantana har ta saurari maganganunsa???😂

Bayan ya kwantar Mata da hankali tare da yi Mata Alk'awarin ba zai tab'a barin Khausar ta auri Abba ba sannan suka yi sallama kowannansu ya kashe wayar.

Abdurrahman ya dad'e a cikin motar ba tare da ya ja ta ba, Yana tunanin abin da Khausar d'in take Shirin yi "Lallai ma yarinyar nan, wato tanan Kuma ki ka biyo, to Baki Isa ba mun fi k'arfinki" Yana gama fad'ar haka ya ja motar ya nufi gidansu Khausar.

_Hy! Habibaties karku manta fa SO SHU'UMI Yana nan Yana jiran ku nuna Masa SOYAYYA ta hanyar siyansa #300 ku yi min magana 08122188717_

Yana isa gidan ya fito daga cikin mota, wani yaro ne ya zo hucewa Abdurrahman ya kirasa "Kai zo" Yaron ya zo Yana cewa "Gani nan","Dan Allah ka shiga gidan nan kace ana sallama da Khausar" Yaron ya amsa da to sannan ya shiga gidansu Khausar bakinsa d'auke da sallama.

"Assalamu alaikum"

Rahma wacce take wanke-wanke ta amsa masa sallamar "Wa'alaikassalam"

"Wai ance Khausar ta zo inji wani"

Khausar ta fito daga d'akinta tana kallon yaron "inji wani kuma?" Ta tambayeshi tana kallonshi cike da mamaki, yaron ya gyad'a kai alamar eh.

Khausar ta ce "To kace Ina zuwa" Yaron ya juya ya fita ya fad'awa Abdurrahman ta ce tana zuwa, sannan ya yi nasa wajen.

Khausar ta saka hijabinta tare da kallon Rahma ta ce "Sister mie bari na je na ga waye yake nema na" Rahma ta ce "To shikenan" Khausar ta nufi  hanyar waje.

Wani irin burki ta ja ganin Abdurrahman abin da ya ba ni mamaki sai ganin Khausar nayi tana wani irin shu'umin murmushi sannan ta k'arasa gurin da yake tana cewa.

"Yau kuwa d'a ne ya zo gaisar da uwarsa" Abdurrahman ya yi mata wani wulak'antatcen kallo ya ce "Waye d'an naki?? Kaii Khausar Ina so ki shiga hankalinki sosai wallahi ni d'in nan ba mutunci ne da ni ba, na ji kina shirin auren Abban Fad'i"......

"Dakata malam, waye kuma Abban Fad'ima, to baka ji dai-dai ba dan ni ubanka zan aura, dan haka ka shirya kirana da mummy" Khausar tayi maganar tana dariyar jindad'i.

Abdurrahman ya yi wata iriyar dariya har yana buga motar da k'arfi "Lallai Khausar ban san baki da hankali ba sai yau, Abbana kike son ki aura, to idan mafarki kike ki yi gaggawar farkawa dan wallahi Abbana ba zai tab'a aurenki ba" Ya yi maganar yana yi Mata wata muguwar harara.

Khausar tayi murmushi tare da yin tafi tana cewa "To Bari na nuna maka wani Abu" Wayarta ta shiga latsawa sai gashi ta nemo hoton da sukayi da Alhaji Saleh suna sakarwa junansu murmushi, ta nunawa Abdurrahman ta ce "ka ga shaida ko?? Kuma Abban Fad'ima Sister mie ce zata aureshi Ka fahimta" Khausar tayi maganar tana yi masa wani irin kallo.

Abdurrahman ya zaro ido sosai ganin Abbansa tare da Khausar bakinsa na rawa ya shiga cewar "Khau.....Khau....Khausar Abbana ne fa, shi kike nufi zaki aura" Khausar ta harareshi tare da jan tsaki ta shiga gida tana rera wak'arta.

Abdurrahman ya zame ya yi zaman dirshen a k'asa hawaye na zuba daga idonsa ya fara sambatu.......

Share plss🙏🏾

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now