PART 12

46 6 2
                                    

*TSANTSAR YAUDARA.*

*✍🏽'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban*

*Sadaukarwa ga habibaties💃🏼💞*

*Kuyi following d'ina a wattpad😰*
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=QUEENNASMERH08&wp_originator=Dc2LE0SO%2FHWLF8SESpNia9X2tmmDswdF2yVF%2FzkeABanEPiB8ElGpzFZb%2BI0yUUGqaOTCo28dfUw3u4i2mEF9RHgjz8oxYHgjF%2Fb0pqg0Ccscg9BjMmx%2BSBdzfiFB2K%2B

*Shafi na 12*

"Ina son irin wannan kwarin guiwar Sister mie, shiyasa nake k'aunarki sosai Allah ubangiji ya cika mana muradinmu" Khausar ta ce "Amin ya Allah Sister mie" Haka sukayi ta hirarsu ta duniya abun gwanin ban sha'awa, kuma suka cigaba da tsara yadda zasu cika muradinsu na auren Abban Fad'ima da Abban Abdurrahman.

         ***  ***  ***

Minal ce ta shigo d'akin Abdurrahman bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" D'agowa Abdurrahman yay tare da yi mana wani irin kallon banza, ba tare da ya amsa mata sallama ya ce "Meya kawo ki d'akina???" Minal cikin rawar murya ta ce "Yaya dan Allah karka koreni magana na zo muyi da kai" Tayi maganar kamar za ta yi kuka, Abdurrahman bai k'ara cewa komai ba, Minal ta k'araso ta zauna a kusa dashi tana kallonsa idonta cike da kwalla "Yayana haushina ku ke ji ko??" Abdurrahman ya kawar da kansa gefe dan baya son ya ga koda dai-dai da minti d'aya ran autarta su ya b'aci, Minal ba tare da ta damu da rashin maganar da bai yi mata ba ta cigaba da cewa "Yayana kasan kaf duniya babu wanda ya kai ni son ganin yau za'ayi aurenka, na fi kowa d'aukin ganin ranar d'aurin aurenka, munyi magana da Abba kuma ya fad'a mana kwakkwaran dalilin da yasa ya ce a fasa aurenka da Fad'ima kuma nima nayi bincike sosai na tabbatar da abin da ya fad'a mana gaskiya ne ba k'arya ba, Yaya Abba taimakonka yake son yi ba ya son ya ga yau matar d'ansa gudan jininsa tana safarar miyagun kwayoyi" Wata iriyar zamura yay yana cewa "Minal me kika ce?? Kina nufin Fad'ima ce take safarar miyagun kwayoyi" Abdul'aziz ya turo kofar d'akin tare da cewa "Tabbas wannan haka yake kuma muna da shaidar da zamu nuna maka da zaka tabbatar da hakan, Minal nuna masa wad'annan hotunan da video da yake cikin wayarki" Minal ta ce "To Yaya" Wayarta da ke hannunta ta shiga daddanawa hotunan da sukayi wa Fad'ima lokacin da taje wajen da suke adana miyagun kwayoyin ta shiga nuna masa har da video da sukayi mata, da yake tunda Abba ya fad'a musu abun da Fad'ima take yi suka shiga bibiyarta har sai da suka gano wajen da suke adana miyagun kwayoyin da suke safararsu, Abdulfatah da Abdallah suka shigo d'akin da sallama "Yaya Abdurrahman kuma akwai hotunan da mukayi mata a yau da muka".....Abdurrahman cikin k'unar zuci ya ce "Ya isa dan Allah ya isa haka, ashe daman Abba taimakona zai yi shiyasa ya ce a fasa auren nan ashe daman k'ullalliyar da Fad'ima take kulawa kenan shine kuma take shirin aurena" Duk yana kuka yake yin maganganun nan abun ban tausayi, rarrashinsa suka shiga yi da kalamai masu dad'i har yay shuru, tashi yay ya nufi hanyar fita daga d'akin su ma suka rufa masa baya, b'angaren Abbansu suka shiga Abdurrahman ne a gaba zaune suka tarar dashi a kan kujera Abdurrahman ya zube a gabansa yana kuka ya ce "Abba ashe daman abin da yasa kace a d'aga d'aurin auren kenan to Abba ina me tabbatar maka fasa auren ma za'ayi ba d'aga shi ba ma dan wallahi na tsani Fad'ima tunda na ji abun da take yi, Abba meyasa baka fad'a min ba?? Kasan dai idan har ka zaunar da ni ka fad'a min wannan b'oyayyan halin Fad'iman zan yarda kuma zan fasa auren" Alhaji Saleh yay murmushi ya ce "Abdurrahman kenan, a wanchan lokacin kona fad'a maka halin Fad'ima ba yarda za ka yi ba, saboda mahaifiyarka ta saka muguwar tsanata a zuciyarka, bayan kuma bata san dalilin da yasa nayi haka ba" Abdurrahman ya ce "Yanzu Abba ne sani dan haka ni ba zan iya auren Fad'ima ba, ba zan iya ba zanje har gidansu na sanar musu na fasa" Alhaji Saleh ya ce "Ba sai ka je har gidansu ka fad'a musu ba Abdul ka kwantar da hankalinka tunda yanzu kasan gaskiya ni da kai na zanje na sanarwa da Iyayenta mun jenye auren" Haka dai Abdurrahman yay ta ba wa mahaifin na sa hak'urin abubuwan da yay tayi masa da kuma maganganun da yay ta jifansa dashi.

Hajiya Saratu ce ta shigo d'akin fuskarta a murtuke, ta kalli Abdurrahman tare da cewa "Wato kai ma ka yarda da irin k'irk'irarrun labaran da wannan banzan yake zaunawa yake tsarawa ko??" Abdurrahman ya ce "Mummy, Abba gaskiya yake fad'a mana wallahi Fad'ima tana safarar miyagun kwayoyi kuma akwai video da hotunan da akayi da zaki tabbatar da haka" Hajiya Saratu cikin tsawa ta ce "Dalla rufe min baki banza mara zuciya kawai, zaka zo kana cewa wani Abba gaskiya yake fad'a sai aka ce maka kuma ba za'a iya had'a hoto ba dan ayiwa Fad'ima sharri ko??" Abdurrahman ya ce "Mummy wannan ba sharri akeyi wa Fad'ima ba da gaske ne wallahi" Hajiya Saratu ta kalli Abba tana cewa "Munafiki burinka ya cika sai ka zuba ruwa a k'asa ka sha ka rabani da yarana har ina fad'a suna maidar min da martani" Tana gama magana ta huce ta fita daga d'akin, Abdurrahman ya kalli mahaifinsa da ya rik'e kai ya ce "Abba kayi hak'uri ban san meyasa Mummy takeyi maka irin haka ba" Abdulfatah su ma hak'urin suka shiga ba wa mahaifin na su, murmushin ya'ke yay ya ce "Bakomai insha Allahu komai zai yi dai-dai" Haka suka fita daga d'akin kowannansu ya koma b'angarenshi, Abdurrahman yana shiga d'akinsa ya zauna a kan kujera ya d'auko wayarsa ya shiga yi wa Fad'ima text "To munafuka a haka kamar ta Allah ashe tsohuwar annamimiya ce, to yau dai asirinki ya tonu kuma ni Abdurrahman Saleh ba zan tab'a iya auren mai safarar miyagun kwayoyi ba, yau zan yarda kwallon mangoro zan huta da k'uda" Yana gama rubuta text d'in ya tura mata.

Fad'ima tana zaune a kan kujera kusa da mahaifiyarta text d'in Abdurrahman ya shigo wayarta, da sauri ta d'auki wayar tare da fara karanta text d'in, wata iriyar gigitatciyar k'ara ta saki tare da dora hannu akai tana cewa "Na shiga ukuna, yau me zan gani Abdurrahman karka yi min haka wallahi ina sonka sosai" Mummy ta kalleta cike da mamaki ta ce "Meya faru?? Me Abdurrahman d'in yay miki??" Fad'ima ta ce "Mummy Abdul d'ina zai rabu dani saboda mak'iya sun shiga tsakaninmu" Tana gama maganar ta d'auki hijabi tayi hanyar waje wani irin jiri ne ya kwasheta ji ka ke tim ta zube a wajen wanwar babu numfashi, Mummy ta k'araso wajen cikin kid'ima tana kiran sunan Fad'imar "Fad'ima! Fad'ima!! Fad'ima!!!" K'awarta Hajiya Sumayya ce tayi sallama da sauri Mamy ta ce "Yauwa Hajiya taimaka min mu kai ta asibiti" Hajiya Sumayya ta ce "Meya faru da ita haka??" Mummy ta ce "Yanzu ne muke zaune da ita wayarta tayi k'ara ta duba naga ta zabura tana cewa Abdurrahman zai rabu da ita, ta saka hijabi tana zuwa nan kuma ta zube" Duk cikin kuka Mummy take maganar.

Hajiya Sumayya ta taimaka mata suka d'aga Fad'ima suka fita suna zuwa wajen motar driver ya bud'eta suka saka Fad'ima su ma suna shiga ya ja motar ya nufi asibiti da ita gaba d'ayansu duk a gigice suke😂💃🏼🤞🏽

Anan zan dasa aya🤞🏽rashin comments d'inku ne yasa na dawo da typing sai na ga dama🤷🏼‍♀️

Share
Comment

TSANTSAR YAUDARATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon