Part 2

47 1 0
                                    

*TSANTSAR YAUDARA😭💔*

*'Yar mutan zazzau Naanah M Sha'aban✍🏾*

*Sadaukarwa ga Habibaties💃🏼*

*Wannan salon na daman ne wallahi nasan zaku ji dad'in littafin nan habibaties, sadaukarwa ne gareku da fatan zakuyi wa 'yar uwarku sharing zuwa groups d'in da ku ke💃🏼💃🏼kai duk inda ma ku ka san kuna amfani facebook da dai sauransu💃🏼💃🏼*

Shafi na 2

*Wacece Khausar?*

Khausar Muhd Lawal shine asalin sunanta, mahaifinta Malam Muhd Lawal malamin makaranta ne na secondary mahaifiyarta ta rasu tun tana k'arama su biyu su ne kad'ai a wajen mahaifinsu, Rahma ita ce babba sai kuma Khausar d'in, sun had'u da Fad'ima a makarantar islamiyya, lokacin da Khausar d'in tana sabuwar zuwa a makarantar da yake ajin su Fad'imar aka kai ta, tun daga ranar Fad'imar tai-ta jan Khausar d'in a jiki har ta sakin jikinta da ita suka zama k'awaye sosai, duk inda Khausar take Fad'ima tana mak'ale da ita, kullum tana gidansu Khausar anan take wuni sai dadaddare wajen goma zata tafi gida, anan suka k'ara shak'uwa sosai dan har ta kai ga Fad'ima wata rana tana kwana a gidansu saboda iyayen Fad'ima suna da kud'i sosai kuma duk abin da take so suna yi mata, ita kad'ai ce 'yarsu shiyasa suka shagwab'ata sosai, duk wani sirrin Khausar Fad'ima ta sanshi babu abin da Khausar take 'boyewa Fad'ima ita ma kuma haka, Abdulrahman Adam Saraki d'an gidan wani shahararran mai kud'i ne, ya zo unguwarsu Khausar gurin wani abokinsa da sukayi makaranta d'aya mahaifinsa bashi da lafiya ya zo duba jikinsa anan ya ga Khausar ta dawo daga islamiyya ita kad'ai ranar Fad'ima bata je islamiyyar ba ta je birthday d'in k'awarta, Abdulrahman bai bar unguwar ba sai da ya tabbatar ya samu soyayyar Khausar bayan sun yi musayar number, ya tafi gida zuciyarsa cike da farin ciki.

Khausar kuwa Abdulrahman yana tafiya ta shiga gida zuciyarta fal farin ciki kiran Fad'ima tayi a waya take fad'a mata tayi saurayi, Fad'ima tayi murna matuk'ar tare da yi mata fatan Allah ubangiji ya barsu tare yasa ta ga bikinsu, Khausar ta amsa da Amin, Khausar da Abdulrahman sun d'auki kusan watanni biyar suna soyayya ba tare da Fad'ima ta tab'a ganin Abdulrahman ba saboda Fad'ima macece mai tsananin izza da ta'ka dan ita a cewarta wai ba za ta iya tsayawa wani ta had'u da Abdulrahman ba dan bai kai matsayin da zata had'u dashi ba dan kawai saurayin k'awarta ne shiyasa ta ke d'an ganin mutuncinsa.

Ranar wata alhamis Fad'ima ta zo gidansu Khausar tun da safe suna ta hirarsu sai wajen k'arfe 5pm na yamma ta tashi zata tafi gida Khausar ta saka hijabinta dan rakata,Fad'ima tayiwa Rahma sallama suka fito hannayensu rik'e dana juna, Khausar ce ta ja ta tsaya a kofar gida tana kallon Abdulrahman wanda yake jingine a jikin motarsa yana murmushi, ita ma murmushin ta shiga sakar masa, Fad'ima ta kalli inda Khausar d'in take kallo tana murmushi, lokaci d'aya gabanta ya fad'i tare da k'urawa kyakkyawan saurayin da yake tsaye yana kallon Khausar ido, zuciyar Fad'ima tayi wani irin bugu a zuciyarta ta ce "Kar dai wannan had'add'en guy d'in ne saurayin Khausar, ai kuwa akwai k'ura dan sam bai dace da ita ba, wannan ai ba kalarta ba ne, nice nafi dacewa dashi domin ni ce dai-dai dashi tabbas ni zan aureshi kuma zai zama mallakina ni kad'ai" Khausar ta kalli Fad'ima ganin tayi mata magana amman sam bata ma san tana yi ba,ta lula duniyar tunani girgiza hannun Fad'ima tayi tare da kiran sunanta "Fad'ima besty" A firgice Fad'ima ta kalli Khausar tare da yi mata murmushin yak'e "Na'am Bestyna" Khausar ta ce "Kin ga Abdulrahman ya zo yau dai zaku gaisa dashi, daman ina ta bashi labarinki gashi yau zai ga bestyna" Fad'ima dai bata iya cewa komai ba sai murmushin yak'e take faman yi, haka suka k'arasa gurin da Abdulrahman d'in yake suka gaisa da Fad'ima sannan ya kalli Khausar yana cewa "Amincin Allah ya 'kara tabbata a gareki ya ma'abociyar kyau da kyan hali" Murmushin kan fuskar Khausar ya k'ara fad'ad'a ta ce "Kai ma haka sarkin zuciyata, ga Fad'ima k'awata da nake yawon baka labarinta" Abdulrahman ya d'an k'ara kallon Fad'ima tare da ce mata "sannu k'awarmu ya gida" Fad'ima cikin sanyin jiki ta ce "Lafiya" Sannan ta kalli Khausar ta ce "besty zan huce gida sai anjima" Tana gama fad'ar haka ta huce da sauri ta tsayar da mai keke napep ta shiga, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta idanuwanta sun kad'a sunyi jawur sai huci takeyi sautin muryar Abdulrahman take ji yana yawo a cikin dodon kunnanta "Wannan guy d'in daga gani ya iya soyayya sosai, amman nasan abin da zan yi dole sai ya dawo gareni".

Fad'ima kusan kwana biyu tayi ba tare da taje gidansu Khausar ba, dan gaba d'aya haushin Khausar d'in take ji, kamar kullum tana zaune a d'akinta ta zabga tagumi tana tunanin yadda zatayi ta samu number Abdulrahman ta san a wayar Khausar kad'ai zata samu number amman kuma bata son ta k'ara ganin Khausar a rayuwarta saboda ta san inda suka had'u sai tayi mata maganar Abdulrahman da yadda yake fad'a mata irin son da ya ke yi mata "Assalamu alaikum" Fad'ima ta ji muryar Khausar a cikin dodon kunnanta, da sauri ta kalli kofar shigowa suka had'a ido da Khausar, harara Khausar ta watsa mata tare da cewa "Ai kin kyauta tunda kin k'i zuwa wajena ni gani na zo" Fad'ika ta saki murmushin jin dad'i dan yanzu ta samu mafita tunda ga Khausar nan dole zata san yadda zatayi mata dabara ta d'auki number Abdulrahman "Ki yi hak'uri besty ba na jin dad'i ne kwana biyu shiyasa ban zo wajenki ba" Khausar cikin tashin hankali take tambayar Khausar bayan ta zauna kusa da ita "Me ya sameki shine kuma baki fad'a min ba??? Ko dai kin chanza k'awa ne ban sani ba???" Girgiza kai Fad'ima tayi ta ce "Sam ban chanza 'kawa ba, ba na son fad'a miki kar hankalinki ya tashi wannan shine dalilin da yasa nayi shuru ban fad'a miki ba" Khausar ta ce "To shikenan na ji amman daga yau karki k'ara b'oye min idan baki da lafiya kinji dan Allah" Fad'ima ta gyad'a kai alamar to, daga nan suka cigaba da yin hirarsu, chan Fad'ima ta kalli wayar Khausar tare da cewa "Besty dan Allah ban wayarki zan turo Facebook ban san ya akayi ba nawa ya goge" Khausar ta mik'awa Fad'imar wayar ta ta da yake babu security a wayar Fad'ima kai tsaye ta shiga wajen contacts ta shiga laluben number Abdulrahman anan ta ci karo da numbersa kuwa inda Khausar d'in tayi saving da *Rabin raina* Mik'ewa Fad'ima tayi ta ce bari na d'auko miki ruwa ki sha, bata jira jin abin da Khausar d'in zata ce ba ta fita sai da ta copy number Abdulrahman d'in tayi saving da *Habibina* sannan ta dawo d'akinta rik'e da gorar ruwa ta zauna kusa da Khausar tare da bata wayar "Gashi nan nagode sosai besty" Khausar ta harareta tare da cewa "Dan kin tura facebook d'in ki ke yi min godiya, dan Allah ki bari mana karki ba ni kunya" Fad'ima tayi wani irin murmushi wanda ita kad'ai ce ta san manufarsa "To shikenan ki sha ruwan" Khausar ta sha ruwan kad'an ta ajiye sannan suka d'an tab'a hira daga k'arshe tayi mata sallama ta tafi gidansu.

A daren ranar Fad'ima ta kira Abdulrahman ta fad'a masa abin da yake cikin ranta bayan tayi masa bayanin ita ce k'awar Khausar, ya yi mamaki sosai anan dai ya yi mata rashin mutunci tare da ce mata shi ba zai iya cin amanar Khausar ba, ya kashe wayar ta sa gaba d'aya, ranar da wani irin matsanancin ciwon kai ta kwanta bacci saboda irin kukan da ta sha, kuma ta ji wata iriyar tsanar Khausar a cikin zuciyarta, Fad'ima dai bata bar Abdulrahman ba,dan kullum sai ta kirasa kusan sau hamsin, wani ya d'aga ko minti d'aya ba zai yi ba,zai ce mata shi ta kyaleshi sannan ya kashe wayar, wani kuma yak'i d'agawa ya shareta, a haka dai Abdulrahman ganin irin kiran da Fad'ima takeyi masa babu dare babu ranar yasa ya fara kulata a hankali kuma soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninsu, har ya zama ya daina zuwa gidansu Khausar kuma ya daina kiranta ko ta kirashi baya d'auka, watansu biyu da fara soyayya aka saka ranar auren Fad'ima da Abdulrahman, zance ya zaga gari anan ne Khausar ta san cewa Abdulrahman gurin Fad'ima ya koma shiyasa ya daina zuwa wajenta kuma ya daina kiranta, ita ma Fad'ima ta daina kulata kwata-kwata dan akwai ranar da ta je gidansu Fad'imar mai gadin gidan ya hanata shiga yace wai sun tashi, ranar Khausar tayi kuka mai isarta har ta godewa Allah Yayarta Rahma ta shiga rarrashinta tare da kwantar mata da hankali.

Wajen k'arfe biyar na yamma Khausar ta shirya dan zuwa wajen Abdulrahman domin ta tambayesa laifin me tayi masa da ya yi mata wannan tsantsar yaudarar, koda ta je Office d'in Abdulrahman ya yi mata kaca-kaca sannan ya saka wasu k'arti suka fitar da ita daga Office d'in bayan zafafan maganganun da ya yi mata na cin zarafi, haka ta koma gida tana faman raira kuka kamar ranta zai fita.

Cigaban labarin🥲🚴🏽‍♀️

*Please👏🏽👏🏽👏🏽*
*Share👏🏽👏🏽*
*Comments*

*Habibaties dan Allah kowannanku ya yi min sharing kun ji dan manzon Allah💃🏼💃🏼🚴🏽‍♀️🙏🏽👏🏽*



*MRS BREAKER💥*

TSANTSAR YAUDARAWhere stories live. Discover now