Page 1

1.8K 35 3
                                    

_1.Meke Coursing Masturbation??_
_2.illar Masturbation??_
_3.Let's talk about NOMA, Amfaninta ga matasa!!!!!_
_4.Sharrin Aljanu, da hanyar da suke shiga jikin mutum_

_A kakkaɓe zani jama'a💃🏽 ki tabbatar kin kammala girki before you start reading my book....... Ready goooo!!!_

EPISODE1️⃣
http://wa.me/+2348119237616
Safiyar garin Lahadin yau ta kasance safiya mai ɗumbin tarihi ga dukkan jama'ar da suke yankin Kano kuma a sassa daban daban, Dalilin Kwantaccen baƙin hadarin dake garin, kasantuwar yanayin damu na da muke ciki, kuma farkon watan Agusta.
A hankali sassanyar iskar hadarin take Kaɗawa yayinda kuma dukkan baƙin hadarin yaywa samaniya tsinke, cikin nutsuwa baƙin hadarin ke joyewa zuwa jaa, alamar ko wanne lokaci ruwa na iya sauka.
Wata ƙaƙƙarfar iska ce mai tafiya da rufin gidaje ta fara fatali da dukkan wasu abubuwa marasa nauyi, ƙarfin isakar da rugugin hadarin ya wuce tunanin dukkan mai tunani da dukkan alama yau ruwan na musamman ne.

A hankali kuma gajimaren ke gudu yana haɗa jikinsa waje guda, cikin lokaci kaɗan samaniya tai wani irin jaa wanda ya wuce tunani mutane, ga wata ƙara da rugugi da hadarin yake, wanda ya haddasa tashin tsuntsayen daga saman bishiyoyi zuwa ma ɓoya.
Ƙarfin gudun isakar da kuma yadda take fatali da dukkan wani abu dake kan hanya, ya sanya dabbobi fara gudu suna kuka, yayinda abeben hawa suka shiga tsayawa a saman shimfiɗaɗɗan titin Sabon Garin!
"Shuuuu" haka sautin saukar ruwan saman ya bada Amo! Amon daya tsorata dukkan mutanan da suke waje, domin tunda aka fara damuna today is the first day! Da akai ruwa mai tsananin yawa wanda yake sauka da wata iska mai yaye dukkan rufin gidajen da basu da Kwari, saukar ruwan saman yay worse da yaywa al'amarin da yay Coursing wani irin hatsari mai munin gaske.

Saukar ruwan saman bai hanata ko da motsi ba, bare tayi Attempting na gudu zuwa wani wajan domin tsira da lafiyarta.
Tana zaune a saman wata kan bolar kasuwar Sabon gari, the way she's acting zaka san cewa akwai wani abu da yake tattare da ita.
Farar macace mai matsakaicin jiki, ƙyakƙyawa ce sosai saukar long dark hair ɗinta zuwa gadon bayanta zai tabbatar maka cewa ita ɗin ruwa biyu ce wato _(Half-caste)_.
Dukkan sassan jikinta rawa yake yana wani irin ɓari, na tsananin dukan ruwan saman, a dai-dai lokacin da kuma saukar ruwan saman ya juye zuwa saukar ƙanƙara yasa tai wani irin firgita tare da ɗago kanta sama.
”Yasubuhanallah!” hasken fuskarta shi kaɗai zai tabbatar maka cewa wannan ko a mahaukatan ita sabon kamo ce, idanunta sunyi jajirrr Jikinta na wani irin ɓari ta tashi tsaye _”Ya hayyu ya ƙayyum”_ ashe tsirara take babu komai jikinta sai dugun gashin daya rufe asalin kayan fuskarta.
Idanunta ta ɗaga sama kamar mai tunani a hankali kuma bakinta ke motsawa yadda babu mai iya jin abinda take faɗa.
Cikin nutsuwa kuma sautin maganar ke fitowa fili tana faɗin.
_“Allahumma Innakaa, Afuuwun! Tuhibbun Afu-afuu Anniii”_
Sune kaɗai kalaman dake fita a bakinta, wanda Ubangiji ne kaɗai ya sahale mata faɗar su, da kuma ƙarfin Imanin da Zuciyarta ke dashi, amma banda haka yaya cikakkiyar Mahaukaciya mai yawo tsirara wacce ta maida kan Bola wajan kwananta, ruwan kwanta ya zama abin kashe ƙishinta, yayinda abubuwan kan Bolan suka zama abincin sawa a cikinta zata iya wannan salati¿ _ONLY GOD KNOWS_.

A dai-dai lokacin ne kuma wata haɗaɗɗiyar mota Rolls-Royce Phantom mai tintak tai parking a wajan, cikin nutsuwa kuma aka buɗe Murfin motar aka fita, wani Babban mutum kuma attajiri ne ya fito yana gyara zaman laimar dake hannunsa.
Idanunsa ya juya tare da sauke ganinsa akanta, wani irin lumshe idanunsa yay yana siɗe laɓɓansa da harshe kamar tsuhun maye.
Cikin wata fitinannan Murya wacce buƙatar kasancewa da mahaukaciyar ya gama narkar da ita, ji yake J ɗinsa na wani irin fisga saboda ganinta da yay naked a gabansa.
Frm head to toe yake binta da kallo!
Cikin zaucewa ya ƙara ji J ɗinsa ta fara fisga to Yarinyar tai bala'in haɗuwa.
A zuciyarsa yake faɗin.
"Young innocent pretty gril aka haukata haka? She's different kyanta daban, komanta daban, that's illiteracy ji ɓeta kamar ƴar sarauta, so pretty my Lord! Yasubuhanallah, masu haukata Yarinyar nan sumbin gata, na samu full chances zaɓe zai zo min a dai-dai, kalleta her body is so soft ga idanu ka manyan kaya,  look at her. Snatch waist wallahi zama ƊAN MAJALISA _(Members federal house of Representatives)_ Dole!”
Ya ƙare zan can zucin yana wani sauke ajjiyar zuciya da shafa ƙirji.
Motsin da taji a bayanta ya sanya ta juya da sauri ganin mutum dake can nesa da ita yasa ta razana sosai.
Tsoro, firgici ya haɗe mata waje guda, Ada kafin shigowar sa cikin rayuwarta _DAMUWA_ ce, amma shigowar sa cikin rayuwarta a yanzu ya zama _ƘALUBALE!_

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now