page 6

817 15 2
                                    

Http://wa.me/+2348119237616

EPISODE6️⃣
Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda ya sanyata saurin janye shanyayyun idanunta tare mai dasu ta rufe,
Wani irin harbawa Zuciyarta keyi tana jin wani matsananci tsoro na shigarta, gata dai male male a jikin mutum amma ta kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi bare tayi tunanin zame jikinta.
Yana zaune saman kujera 1 seater yana sanye cikin wani tattausan wando 3gauter sai farar singlet wacce ta kama jikinsa sosai ta fito da 6pack na jikinsa idanunsa a lumshe yana sauke numfashi, yayinda gudun da zuciyarsa ya ƙaro fiye da baya,
Idanunsa dake a Lumshe ya buɗe a hankali ɗan taune bakinsa yay jin yadda take masa sukur sukur a jiki kamar wata macijiya.
Hannunsa ya miƙa ta gefen lafaffan cikinta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya cup of coffee ɗin sa ya ɗauka, gently kuma yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar.
A hankali yake spending coffee ɗin a bakinsa ya ɗauki wajan 10minute kafin ya shanye coffee ɗin domin daman ƙa'ida ne sai ya sha Wannan coffee ɗin na Subhi da cikin dare kamar wani buzu ko labarabe.
Ajjiye cup ɗin yay cikin nutsuwa kuma ya sanya tafin hannunsa duk biyun tare da zurasu ta tsakiyar hammatar ta caraf ya ɗaga ta tsaye yana yatsuna fuskarsa.
Tsaye Akeela tayi kanta a ƙasa, kunya duk ya kamata through ba taga fuskar wanda ta zauna a cinyarsa ba, amma dadɗan ƙamshin parfume ɗinsa ya sanya tasan cewa shi ɗin daban yake ko a cikin maza.
Musamman yadda taji Physique chest ɗinsa dake cike da ƙwantaccen gashi lub! lub!!..
A razane ta sauke ajjiyar zuciya tare ƙanƙame Jikinta waje guda, naman jikinta ya wani irin rawa da ɓari dalilin saukar wani masifafan ruwan sanyi da taji tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, da alama ma ruwan daga cikin fridge aka ɗauko shi.
Idanunta da sukai wani irin juyewa suka ja ta buɗe da niyyar ganin wanda ya zuba mata ruwan.
Amma kamar walƙiya tuni Akeem ya haura upstairs babu mai cewa Shine yay punishing ɗin ta da wannan ruwan sanyin domin babu wani sign daya bari a wajan.
Abinka da mai ciwon ciki wanda jininta yake double SS tuni jininta yay wani daskarewa, tare da tsaya mata waje guda, a hankali kuma wata ƙwaya ta tsaya a tsakiyar jijiyar ƙafarta tare da lanƙwashewa kamar laushe.
Cikin ƙaramin lokaci ƙafarta ta fara wani irin matsanancin ciwo kamar ana sanya gatari ana datsa ɓargo da ƙashin ƙafarta haka ta keji.
Tsananin azabar da yay mata yawa ne yasa ko kuka ta kasa sai wani irin fitinannan numfashi da take gumi na yanko mata.
A hankali ta sulale tare zubewa a saman carpet ɗin parlon cikin wani irin wahalallan sabon yanayi ta kwanta tare da ɗura ƙafarta a saman kujera ta shiga jujjuya kanta tana sakin wani gigitaccen kuka iya zuci mai bala'in cin rai.
Gashi babu Folic acid da paludrine a kusa da ita bare tasha ko taji sauƙin abin.
Dukkan hannunta ta sanya a ƙafarta ta riƙe gam "ɗib! ɗib!! ɗib!!" Haka jijiyoyin ƙafarta suke harbawa alamar ciwo yayi ciwo a hankali kuma ciwo ya fara yawo a jikinta daga ƙafa zuwa kwankwasonta bata samu bacci ba sai wajan kiran sallar farko na Subhi.

A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen part ɗinsa, yana sanye da Embrodiery Islamic jallabiya white colour, wacce ta kasance mai santsi da taushi tana da half hand daga gaban ƙirjin kuma a ɗan tsage take..
A hankali yake tafiya kamar bai so cikin nutsuwa bakinsa ke motsawa alamar tasbihi yake ga Ubangiji.
Hannunsa a goyo da bayansa yana taka ƙafafuwansa dake sanye cikin Mon mule slippers masu kyau..
A tsakiyar parlon ya tsaya idanunsa a rufe  babu jimawa Abbu ya fito daga part ɗinsa shima sanye da jallabiya milk irinta Akeem.
Babu wanda yay magana a haka suka jera zuwa masallacin dake cikin estate ɗin nasu.
Rutse idanunsa yay da tuni su uku ne suke tafiya amma waccan shigiyar Yarinyar mai siffa da aljanun ruwa taja masa a rasa mafi muni a rayuwarsa.
Bayan an idar ya zauna zaman azkar ƙarfe 6 dai-dai suka fito daga cikin masjid ɗin zuwa gida.
Kai tsaye Akeem kitchen ya nufa yana zuwa ya samu Ummi a ciki sanye da ƙaton hijab har ƙasa, kallonsa tayi tana Murmushi, a sanyaye murya can ƙasa yace.
"Sabahul khair Ummina"
Mug ɗin hannunta dake cike da coffee ta ajjiye a hankali ta ƙarasu wajansa yana ganinta ya ɗan zube a ƙasan gwiwoyinsa tare da zame wular kansa, hannunta ta ɗura a saman sumar kansa kafin tace.
”Sabahul khair Hero”
Murmushi Yay irin Murmushin nan da idan ba ita ba ko Abbu babu mai ganinsa sai Md Adnan.
Addu'a ta shiga yi masa kafin gently ya miƙe, ganin yadda take kallonsa yasa ya ɗan kwaɓe fuska yana lumshe idanunsa cikin narkakkiyar murya yace.
“Ummi”
Hannu tasa ta ja dugun hancinsa tace "Allah ya kyauta maka, ƴarka tayi taɓara kai ma kayi"
Shi dai bai ce komai ba, maimakon ya fita daga kitchen ɗin sai yay zamansa akan kujera yay hakanne kuma saboda bai son fita yaga Akeela.
Fita Ummi tayi sam bata kula da Akeela ba kai tsaye part ɗinta ta shige.
Abbu da ya tsaya da Bala driver yana bashi hqr ne ya shigo cikin parlon kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Akeela wacce take baccin wahala a saman carpet..
Da sauri ya nufi inda take  yana faɗin.
"Ya Salam Babyna bacci a Parlo a ƙasan carpet why?"
Ya faɗa yana tsugunawa tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗauke ta zuwa jikinsa, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara kallon fuskarsa wacce tai jajirr idanunta ya kumbura sosai.
Cikin tausayinta da kuma masifafan sonta dake ƙara zautar da Abbu a hankali ya manna bakinsa a saman goshinta tare da sumbatar wajan karaf a idanun Akeem taɓe baki yay da kuma sauri ya juya tare da komawa kitchen ɗin.
"Sorry nine ko, sorry Babyn Abbu muje na goyaki kiyi bacci sosai, i promise to you cewa ba zaki kuma kuka ba, I'll be your side kinji Babyn Abbu na" ya faɗa yana ƙara shafa fuskarta tare dayin part ɗin yaransa da ita.

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now