Page 7

775 12 5
                                    


Idanunta tayi saurin kullewa tana jin yadda haɗaɗɗan Baccarat rouge (Maison Francis) parfume ɗin sa ya wani daki hancinta, al'amarin daya haddasa mata lumshewar idanunta, jikinta na wani irin rawa domin this is the first time a tsayin rayuwata da  wani ya riƙe ta har ya sanyata a jikinsa so close to him, abin sai ya zama wani Extraordinary to her.
Ajjiyar zuciya ta sauke a hankali ta ɗaga hannunta da suka sauka a saman ƙirjinsa tana wani motsawa saboda zafi da zugin da ƙafarta ke mata yasa sam ba zata iya jure tsaiwar ba, a hankali ta fara yin ƙasa zata zille naman jikinta na wani irin motsi gaba ɗaya jijiyoyin ƙafarta har bawa suke saboda tsananin ciwo..
A karo na biyu Akeem ya ƙara ware gajiyayyun Maraitattun idanunsa tare da sauke su akan Akeela, wani irin lumshe idanunsa yay yana taune bakinsa ji yake kamar ya shaƙe ta ya wuta dama ganinta baki ɗaya a gidan.
Buɗe idanunsa yay yana jan wani mugun tsaki shi dai Abbunsa ya gama dashi, ganin yadda take ƙoƙarin zillewa daga jikinsa ya gently ya gyara tsaiwarsa, tare da ɗaga left hand ɗinsa ya wani manna shi a saman waist ɗinta slowly kuma ya haɗa ta da lafiyayyan jikinsa a hakan yana jin yadda naman jikinta ke rawa na tsananin azaba, cikin nutsuwa kuma ya fara murza Nightgown ɗin dake jikinta da sauri ta buɗe lumshasshun idanunta for the frist time ta sauke idanunta akan kamilalliyar fuskarsa.
Wani irin ƙyakƙyawan bugawa Zuciyarta tayi, zata iya cewa bata taɓa ganin Mutum mai mugun kyau kamar Abdul-hakeem Bukar Bello ba,  ƙwayar idanunsa kaɗai zata zautar da mace dalilin daya sanya koshi karan kansa ba kowa yake kalla da idanunsa ba, fuskar nan kamar tai tsartuwar jini saboda wani irin fari da yake da shi, ga wani haɗaɗɗan kewayayyan ƙwantaccen sajansa wanda ya taho da sumar kansa ya ke waye fuskarsa dashi da wani gashin baki amma akwai gemu da saje mai ɗaukan hankali.
Ga bakinsa kamar na mace Ƙarami laɓɓansa masu kauri jajaye wani yirrrrr dasu very cute and softness.
Da sauri ta rufe idanunta domin ba zata iya ci gaba da kallonsa ba wani mugun tsoransa ta keji, laɓɓanta ne suka shiga rawa gaba ɗaya suka jiƙe da yawo a karo na farko ta fisgi kalmar "Uhm..dan Allah kada kayi min zan mutu uhm" ta faɗa tana runtse idanunta sosai bugun Zuciyarta na ƙaruwa.
Taɓe bakinsa yay irin ko a jikinsa ɗin nan kima mutu waye yay asara, gumi ne ya shiga tsastsafo mata a tsakiyar goshinta tsakaninta da Allah take gudun allura, jin yaci gaba da murza rigar jikinta yana son fito da ass ɗinta waje yasa ta matse jikinta domin bata taɓa ganin sabon iskanci irin haka ba sai yanzu ko hannu ba'a taɓa riƙe mata ba, da sauri ta sanya tattausan tafin hannunta wanda ya jiƙe da gumi ga wani irin ɗumi da yake da shi ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kanta kamar wacce take shirin shiɗewa tace.
"Dan Allah banso, kaji...uhm kada ka kalli jikina"
Wani zaro idanu waje yay wato saboda jikinta take wannan abin jikinta ɗin banza yay uwar me dashi, village gal like her ma harta san wani ɓoye jiki.
Wani cije lips ɗinsa yay yana ƙara haɗata ta  da jikinsa domin bai zo nan dan kallan wani part of her body ba, banda ɗoyi Meye ma jikin yake yanzu ma sai yaje yay wanka ysin.
Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware dukkan hannayenta ta wani zura su ta tsakanin hammatar sa ta wani irin ƙanƙamesa sosai lokacin daya caka mata allurar cike da zallar mugunta.
Cije bakinta tayi jikinta na rawa kafin ta wani fashe da maraitaccen kuka mai ratsa zuciya tare da kifa kanta a ƙirjinsa, ba taɓa sanin akwai mugunta irin haka ba, ana faɗin zafin allura bata taɓa sanin haka allura keda mafifaffan zafi ba sai yanzu, ji tayi ta ƙara jin haushinsa bata sanshi ba amma daga jiya zuwa yanzu yay mata abinda ko maƙiyinta ba lallai yay mata shi ba.
Ajjiye emtyn injection ɗin yay tare da sauke fuskarsa a tsakanin wuyanta cikin wata kasalalliyyar murya mai ratsa zuciya yace.
_“I would rather waltz with the devil of loneliness than tango with a devil like you. I hate you.”_ ya faɗa yana wani jan numfashi tare ƙara sauke kansa a wuyanta cikin wata husky voice idanunsa na wani ruwa ruwa yace.
_“Do you know the real meaning of the world Selfish? Take a look into the mirror and you will find out. I hate you_, ke selfish ce kin kashe min ƙani ke gaki nan You still alive kina shaƙar iskar duniya, _You killed my brother_ wallahi na tsane ki bana son ko buɗe idanu na ganki _I hate you.. I hate you, I hate you! You stupid gal witch!!!_
Ya faɗa yana wani cilli da ita tare da hankaɗata baya Allah yasa da bed kusa da ita gaba ɗaya tai bed ɗin ta faɗa saman sa "Auchhhiiii!!" Ta faɗa tana tura ƙaramin bakinta gaba saboda zafin burgewar da tayi, abinda bai sani ba tunda yay mata allurar bacci yay gaba da ita, gyara kwanciya tayi wani nauyayyan bacci ya ɗauke ta.

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now