16-17

1.3K 22 5
                                    

*🌈TSINTACCIYA🌈*

NIMCYLUV
FITATTU HUƊU🔥

Writer of
Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
Kwaila ce
The new emir
Jidda
Juyayi
Izzar so
Moon
Lamrat
Raino ne sila
Ranar Aure na
Ƙaddarar mace
Ashe ƴar babata ce
TSINTACCIYA

http://wa.me/+2348119237616
MASU SIYA SUYI MGN👆🏾

EPISODE1️⃣6️⃣-1️⃣7️⃣
Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai.
Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taɓa ganinsa a ciki ba yay saurin faɗin "Dr" idanuna da suke a Lumshe ya buɗe tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace "what... what happened to Akeem?" Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar wanda baya son yin magana ya buɗe baki da ƙyar yace "noting" yana faɗin hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baƙar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part ɗinsa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miƙe tana faɗin "Abbie na" bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama ture ta kai tsaye upstairs ya nufa yana dafe kansa yana jin yadda Amani ke kuka amma yau banza da ita, Didi dake zaune tayi saurin faɗin "Au! Yarinya ba sai dai kiyi tayiwa Ubanki istigifari ba, daɗin abin ko kashe ki yay shine ya haifa a toh" Aleema ce ta kama hannunta tana rarrashinta kasancewar weekend ne duk suna gida. Akeem na shiga side ɗinsa rest room ya nufa cire farar jallabiyar jikinsa yay tare da saƙale ta a hanger, fure fresh skin ɗinsa ta bayyana wani irin ƙwantaccen baƙin gashi ne a saman mararsa mai matuƙar ɗaukan hankali jikinsa a sanyaye ya nufi cikin tube tare da shigewa ciki, wani irin sauke numfashi yay a hankali kuma ya ƙara nutsewa cikin ruwan dake cike har bakin tube ɗin, zafin da zuciyarsa ke masa ya sanya gaba ɗaya yama mance a cikin ruwa yake, idan ya tuna irin faɗan da Ummi da Abbu sukai masa sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirjin, cikin ficewar hayyaci da kuma zallar damuwar dake ransa ya ƙara nutsa kansa cikin ruwan a hankali kuma ruwan ya fara shige masa cikin baki da hanci.

A hankali wata baƙar mota mai ƙirar Audi RS5 ta fara shigowa ciki Nasarawa daga farko farkon Nasarawa harya gifta sai kuma ya dawo baya a hankali yana zare baƙin glasses ɗin dake idanunsa,  saurayi ne ɗan kimanin shekaru 27 yana sanye da wani farin voyal wanda yay masa kyau sosai kasancewar sa farin bafulatani kana ganinsa Kasan cewar kuɗi sun zauna masa, a hankali yake tafiya da motar zuwa baya kasancewar shike driving ɗin ganin hakan yasa wanda ke kusa dashi yace "Ajmal me kake haka ne?"shiru Ajmal ɗin yay domin baya jin akwai abinda zai iya faɗa, a hankali ya gama tsayar da motar  tare da buɗe murfin motar ya fito ganin hakan yasa Karim yay saurin fitowa yana faɗin "wallahi kaifa ba hankali gare ka ba, kana ganin aikin dake gabanmu dole ne a wannan satin mu samu mu shawo hankali duk raguwar jama'ar" ina Ajmal baya gane yaran domin tuni idanunsa suka sauka akan fuskar Akeela dake kwance a ƙasan wata bishiya wallahi wallahi a wannan lokacin duk wanda yaga Akeela dole zuciyarsa ta buga domin ba zaka taɓa cewa ƴar hausawa bace, tana kwance kanta na zubda jini saboda wata muguwar faɗuwa da tayi gaba ɗaya kayan baccin dake jikinta sunyi wani bala'in yin datti gashinta ya wargatse yay ɗai ɗai, tsaye Ajmal yay akan Akeela yana jin zuciyarsa na bugawa, a hankali kuma ya tsuguna a gabanta dai-dai lokacin da Karim yake ƙarasuwa wajan cikin sauri yace "wai Ajmal meke damunka ne? Baka tsoran abin cutarwa ne? Kilama ba mutum bace Aljana ce, ina ka taɓa ganin mace mai gashin wannan?" Banza Ajmal yay masa domin yadda idanunsa suka sauka akan fuskarta yasa baya fahimtar komai dukkan wani abu na kansa sai da ya kunce, hannunsa ya miƙa tare da tattare sumar data rufe mata fuska cikin sauri ya rufe idanunsa yana faɗin "Ohh God"  Karim yay saurin faɗin "is she died?" Girgiza masa kai kawai Ajmal yay yana ƙoƙarin sanya hannunsa ya ɗauke ta Abbu dake ƙarasuwa wajan yace "Akeela! Allahamdulillah"
Da sauri ya sanya hannunsa ya ɗauke ta tare da kallon Ajmal yace "thank you son, wallahi tun jiya mukai missed nata yanzu na ƙara fitowa ne, kamar daga sama na hangeka ji nai kawai ina son ganin Meke faruwa cikin ikon Allah kuma naga Akeela thank you" jinjina kai kawai Ajmal yay yana shafa wuyansa sosai ya gane Abbu amma shi Abbu sam bai gane waye Ajmal ba, kamar bazai magana ba sai kuma yace "Dad! A nan kuke ne?" Kallon Ajmal Abbu yay yana karantarsa sai kuma yace "eh cikin Railway quarters no 112" idanunsa akan fuskar Akeela yace "ok Thank you" yana faɗin hakan ya nufi cikin motar tare da zama wajan driving ba ganin hakan yasa Karim shima ya shiga cikin motar da gudu Ajmal yaja suka bar wajan, mai makon yaje inda zashi sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar gida da Mamaki Karim yace "wai Ajmal Meke damun ka ne?" Cikin ɓacin rai Ajmal yace "ban sani ba, banza shege munafuki kawai haba" ya faɗa cikin ɓacin rai yana ƙara sharara gudu.
Abbu shima cikin farin ciki ya nufi motarsa bai yadda ya ajjiye ta a back seat ba a nan saman jikinsa ya barta key yaywa motar ya juya zuwa gida tun a hanya ya kira number Ummi da sauri tai picking call ɗin tana faɗin "Something news?" Cikin ƙasa da murya yace "I've seen her Ummi on my way yanzu" Murmushi tayi tace "Allahamdulillah"

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now