page 3

952 14 1
                                    


EPISODE3️⃣
http://wa.me/+2348119237616
*_domin magana dani kai tsaye👆🏾_*

Tura kansa dake cikin ruwan zuwa waje yay yana haɗa numfashi, cikin wata kasalalliyyar murya mai cike da alhini yace "I got her" yana faɗin hakan kwanakwanan suka cilla masa duguwar igiya ya kama tare da ɗaura igiyar a ququnsa.
Cikin saurin ya nusa cikin ruwan kafin a hankali ya kama igiyar data riƙe ƙafar Akeela.
A hankali ya kunce igiyar gaba ɗaya Akeela tayi baya tare da fara yawo a ruwan zata matsa can gefe saboda ruwan da yake gudu sosai,
Fararan tafin ƙafafuwanta yabi da kallo, sunyi wani mugun haske kamar jini zai zuba a jikinta saboda farin da take dashi.
Tattausan hannunsa ya miƙa tare da jawo tafin ƙafarta "kittt" ya jata da zuwa inda take ƙarar tawowar wani ruwa ne ya daki kunnansa da sauri ya fisgota yana runtse idanunsa tare da sanya dukkan hannayensa ya wist ɗinta ya wani ƙanƙame idanuna da hannunsa dake bisa jikinta ko motsi ya ƙiyi.
Ya ɗauke dukkan Numfashinsa yana jin sanda ruwan ya shige ta gefensu kamar zai tafi dasu.
Zaro kanta dake jikinsu yay sai a lokacin idanunsa ya sauka akan fuskarta _Tsarki  tabbata ga Ubangijin daya halicci sammai bakwai da ƙassai bakwai, Ubangijin daya halicci wannan duniya ya kuma halicci wannan surar dake hannun Akeem_ faɗin asalin kyan fuskar Akeela bata baki ne, tana da wani irin sahihin kyau, wanda ya wuce tunanin mai tunani, idanunta a rufe suke ruff amma eye lashes ɗin nan da suke dugwaye  slick dark blck sunyi kwance saman kumburarrun idanunta, ga dugun hancin nan mai kyau sosai, wanda ya tsaya dai-dai tsagen laɓɓanta wanda suke da kauri sunyi jajir dasu.
Gashin kanta data ɗaure da ribbon tuni ya wargatse ya baje yana yawo cikin ruwa sai ta zama kamar wata aljanar cikin ruwan da mutanan suke faɗa.
Taɓe baki Akeem yay kafin cikin zafin nama yay wani cillata bayansa ya goyata sosai kafin ya gyara zaman igiyar jikinsa.
A hankali ya fara ta suwa sama cikin ƙwarewa kwanakwanan na ganinsa suka fara jawo igiyar ruwan.
P.a ne yabi Ubangidan nasa da kallo yana tuna wani abu daya wuce amma ya rasa ko menene, amma Tabbas ganin Akeem goyo da Akeela ya tuna basa wani abu mai mata tuƙar muhimmacin a rayuwarsa.
A fili Malam ya furta "Allahamdulillah biii rahmatiikaa"
Suna zuwa bakin ruwan yay wani irin baya yana daga tsaye yay wurgi da Akeela ta faɗi ƙasa ji kake "timmm" kanta ya bugu ƙasa amma ko motsi ba tayi ba saboda bata hayyacinta ta jima da sumewa.
Jikin Akeem na wani irin kyarma da rawa idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun yi bala'in tashi sai wuci yake na zafin zuciya da kuma sayin ruwan daya gama ratsa dukkan kofofin jikinsa.
Kai tsaye wajan Bala driver ya nufa, ganin haka yasa P.a ya mara masa y domin yasan anything can happen idan Akeem ya ƙarasa domin a wannan karan ɓarin da jikinsa yake ya bayyana asalin zafi da kuma ƙuncin da zuciyarsa keyi, ya bayyana how sad he's.
Yana zuwa ya kalli Bala driver murya can ƙasa yace.
"Car keys?" Zare idanu Bala driver yay kafin ya fashe da kuka yace "Dan Allah dan Annabi kayi min suttura Babban mai gida, ka tausaya min kada ka kuran i don wanna lose my job dan Allah, dashi kawai nake kula da iyali na, na sani a made a mistake amma bani na tursasa Ƙaramin Mai gida shiga ru..."
Gigitacciyyar tsawar da Akeem ya daka masa yana faɗin "Heyyy, car keys nace kaban, kada ka tunzura ni ka bari zanyi Shari'a dakai da ita kanta tsinanniyar datai Coursing wannan abun i hate her, idan ina da rai da lafiya billahi I'll take a revenge, you'll see mene zan, common my friend bani" da sauri Bala  driver ya miƙa masa tarin kyes ɗin, huci kawai Akeem yake idanunsa a ƙasa domin duk abinda zai bai fiya kallon mutum ba, gyaran murya yay jin haka yasa p.a faɗin Md Adnan's phone's, his I.d card" wayar ya miƙa masu kafin ya ɗauki walet ɗin dukkan wani card da ake amfani da shi ya bawa P.a.
Kai tsaye mota Akeem ya nufa zai shiga ko takan Yarinyar baibi ba, kafin ya shiga motar P.a yace "Sir" da sauri ya juya yana dafe kansa  cikin haɗewar fuskarsa nan nashi yace "what again P.a Al'kaseem Yahya gama?" Yadda ya kira full name ɗin P.a yasa kowa na wajan kallonsa a sanyaye p.a yace "Abbu" ke kira.
Kamar bazai amshi wayar ba sai kuma ya amsa walking slowly yake tafiya yana baje gashin kansa wanda ruwa ya jiƙa daga can ɓangaren Abbu yace.
"Son" marai-raice  fuska yay ba tare da yace komai ba, jin haka yasa Abbu faɗin "Are You okey?" Nan ma shiru yay bai ce komai ba hakan yasa Ummi dake gefensa faɗin "Is everything okay?" Didi dake tsaye riƙe da bakin zani tsohuwa ce sosai shekaru sun ja tace.
"Ihuu jama'a, bana faɗa ba? To kai dai Bukari ka haifi ɗa baka haifi halinsa ba, yaro baƙin hali yay masa yawa a to ai duk duniya ba sun shaida, jiya kana gani ilahirin tsiran daka kawo min ta tasss yabi dare ya sace, to ɓarawo ne fa? Banda maye waye ne zaice wani tsire ehe? Ai saini da cinsa ya zame min dole amma ina dai ba faɗin wasa wallahi Bukari ka nemawa ɗan ka magani bana son na fita ana min cune da baki ana gata can, jikanta maye ne, mece cin nama da zaro harshe waje....."
Shiru tayi Saboda saukar Muryar Akeem da taji ta wayar tana faɗin "Keeee!" Zare ido Didi tayi sai kuma ta fashe da kuka tana zare bakin zabi tana faɗin "to! A nan gidan duniya idan ban sawa Audil albarka ba wa zan sawa? Eh? Ta ka samu Iyaye da basu san komai ba ina nan ina jan casbie sai da nayi salati miliyan tamanin da shida to astagafirullah kamar dai bakai haka ba"
Girgiza kai kawai Abbu yay kafin yace.
"Friend ina son?" Ajjiyar zuciya Akeem ya sauke kafin yace "Abbu she killed my brother ta kashe mana Adnan" Miƙewa Abbu yay kafin yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Adnan ya mutu?" Wane kalar zabura Didi tayi sai ga zani a ƙasa tama ƙasa magana.
Ummi bakinta ta rufe saboda kukan da yazo mata da sauri tayi bedroom ɗinta, Mami kuwa idanunta kawai ta ƙurawa Abbu Allah yasa raguwar yaran duk suna makaranta Amani kuma tana bacci.
Cikin dauriya Abbu yace "Stay there Abdul-hakeem, in sha Allah on my way yanzu nan kuje gidan Baffa" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da nufar part ɗinsa..
Ƙasa Mami tayi da kanta sai sauke Ajjiyar zuciya take, Didi kuka kuka ta fasa tana faɗin "Wanne gantalallan ne Adunan? Laa Muhammadur Rasulullah S.a.w ku tare ni kada naje ƙasa"

Kwantar da Akeela akai a ƙasa Taɓa jikinta Malam yay yaji wani mugun sanyi, a dai-dai lokacin har sarkin ruwa yazo amma neman duniya babu Md Adnan gaba ɗaya suka rankaya zuwa gidan Baffa, suna zuwa Malam yace "Rabi maza haɗu min gaushi" babu jimawa ta dawo ɗauke da gaushi Miƙewa yay yana fita yace "maza sauya mata kaya Wannan na jikinta yay sanyi da yawa" Murmushi kawai Baba Rabi tayi yana fita ta miƙe tsaye tare da kunce bakin zani wata ƙaramar (Laya) ta ɗauko tare da samun kan Akeela wajan tsakiyar kanta ta haɗa da Layar ta rufke gashin wajan layar da shige ciki.
Wani Murmushin ta sakeyi ita kaɗan tasan abinda take kafin ta sauyawa Akeela kaya ta rufe ta da zani jikinta yay sanyi sosai kamar ƙanƙara.
Har lokacin Akeem bai shigo gidan ba, yana cikin mota sallah kawai ke fito dashi.
Wajejen Magrib Abbu ya ƙarasu daga kano da Wudil, har lokacin kuma Akeela bata farka ba, jiki a sanyaye Abbu yace "Baka da laifi, infact Adnan taimako yaje yi, Allah kaɗai yasan abinda ya samu Adnan, yana ruwan? Mutuwa yay? Tafiya ruwan yay dashi no one's know! Tabbas idan nace banji zafi da baƙin cikin abinda ya faru ba nayi ƙarya, amma ni musulmi ne waman ƙaddararllahu haƙƙa ƙadrihi, kuma Innallaha ba'assabirin  zanyi addu'a zan saka ai idan har Adnan n raye Tabbas zai dawo gare ni"
Jinjina kai Malam yay kafin yace "haka ne, Ubangiji yasa Adnanu yana raye yaron ƙwarai" Miƙewa Abbu yay yace "Ina ita yarinyar ya farka ne?" Girgiza kai Malam yay yace "A'a muje ka ganta" gaba Malam yay Abbu ya bisa a baya cikin tafiyar nan nashi irin na Akeem yana sanye da wata bugaggiyar shadda dark Ash sai jaddara sai ƙamshi yake.
Malam ne ya fara shiga sai Abbu yana shiga idanunsa ya sauka akan Akeela gaba ɗaya tunaninsa ne ya tsaya cak, zuciyarsa na wani irin harbawa Kallonta yake tamkar zai cinyeta ko ya mayar da ita ciki, wani irin kallo ne mai kama da wanda ya kamo da soyayya! "Bukar! Bukar!" Da sauri yaja numfashi yana shafa ƙirjinsa kafin ya kalli Malam da sauri kuma ya juya yana kallon Akeela dafe ƙirjinsa yay ji yay wani mugun so da ƙaunar Akeela ya sauka a zuciyarsa har yana jin idan bai aureta ba zai iya mutu....

😂 Alhaji ka taro match, mata biyu? Eh? Yara sama da biyar kaga ɗanya sabuwar nona kace kana so? Jama'a me kukace anya Abbu bai so zuciyarsa ba????

ANJIMA DA FARA PAYMENT TUN KAFIN NA FARA POSTING

     

*TSINTACCIYA*
NRML GRP: ₦300
VIP: POSTING SAFE+YAMMA ₦500
ACCT NO: 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S
BANK NAME: UNION BANK
EVEDANCE OF PAYMENT
08119237616

*FITATTU HUƊU🔥*

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Baƙar fata
Autar manya

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

SULTAN
Mss flower

Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218


*SARAUTAR MARUBUTA* For more information😇
http://wa.me/+2348119237616

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now