Page 5

842 16 1
                                    


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR
Call 08066268951*

EPISODE5️⃣
Http://wa.me/+234811237616

Bayan sallar magrib motocin su suka fara shigowa cikin haɗaɗɗan titin _Railway quarters Nasarawa, Kano_
A gida mai number 112 suka fara shigar da motocin bayan gatekeeper ya buɗe masu ƙaton gate ɗin.
Motar Abbu ce a farko shida Bala driver sai Akeela dake kwance a baya.
Mota ta biyu kuma P.a a ciki shi ɗaya yana janta motar ƙarshe kuma Oga Dr Abdul-hakeem Bukar Bello ne zaune ya ɗura hannunsa guda ɗaya a saman string motar ɗaya hannunsa kuma ya tsakiyar kansa yana hargitsa sumar kansa, a hankali kuma yake sauke ajjiyar zuciya ajajjere.
Zafi da raɗaɗi da zuciyarsa ke masa na tawowa da Akeela da Abbu yay yafi komai baƙanta masa, cos she's the reason behind anything daya samu Md Adnan.
Bama ya so ya buɗe ido yaga yarinyar shiyasa yau zamansa cikin motar tare da lumshe idanunsa yana so Abbu ya shige da ita domin ta riga data zame masa mujiya.
A hankali Abbu ya buɗe back seat tare da zura kansa cikin motar, dim! dim!! dim!! Haka zuciyarsa ke bugawa aduk sanda ya kalli ƙyakkyawar fuskarta wata nutsuwa ta saukar masa.
Zama yay cikin motar tare da miƙa hannunsa gaba ɗaya biyun ya jawota sosai very close to him, hannunsa dake rawa yasa tare da yin baya da gashin ta wanda ya sauke wai wist ɗinta,
Lumshe idanunsa yay cikin ƙasa da Murya yace "Uhm baby na mai kyau, nine ko?" Ya faɗa yana shafa kanta sai kuma ya cireta sama tare da fito da ita daga cikin motar, dai-dai kunnanta kamar wacce ta kejin sa yace.
"I'm your dad, your boyfriend uhm baby kina cin abinci kuwa? You are so light Baby" ya faɗa yana tafiya da ita kamar wani mai sabon jini bayan yay jika da ita.
P.a dake tsaye ya ɗauke idanunsa a hankali kuma yabi bayan Abbu da some things na Md Adnan.
Tsayawa Abbu yay tare da danna wani ma danni a hankali ƙofar ya fara ja baya tare da buɗewa ciki ya shiga babban Parlo ne daga cikin ƙofar, iya haɗuwa ya haɗu komai na Parlo Ash ne daga kujeru zuwa Flowers da labulaye anything dai.
Ga ƙatuwar cineme kusan rabin bango sai deep frizer mai gida wajan uku,ga senter table a tsakiyar mai ɗauke da wata ƙatuwar flower jikin bangon parlon duk Album ɗin ayatul kursiyu ne, da fatha e.t.c
Daga can bayansa yaji ana faɗin.
"Ya..yah kamar dai ƴan gudun hijira kuka faɗo mana gida babu ko Sallama? A'a babu ruwana kuda Allah tun dai duk musulmai ne a gidan da haka nan kamar ƴaƴan arna zaku faɗu mana gida, ai ko ƴan dama ne ku kwayi sallama musan da zuwanku kuma musan abinda zamu baku"
Kallon Didi Abbu yay kafin yace.
"Afuwa Didi"
Taɓe baki tayi kafin tace "A'a astagafirullah mene kuma afuwa fisabilillahi kamar dai nace akan Bukari siya min tsire? A'a ni rayuwar duniya mai sauƙi na ɗauke ta, Wacece wannan kuma Aljanu take ko shan Inna ce ta kamata"
Ta faɗa Idanunta akan Akeela wacce take jikin Abbu.
P.a Murmushi Yay domin yana son dramer tsohuwar kafin yace.
"Barka da dare Didi"
Washe baki Didi tayi tace "A'a ƙasimu ince dai ka samu matar aure? Yooo ba Gwamma kai ba ko babu komai zan baka shawara mai kyau kabi, kaga dai babu dangi iya babu na baba jinƙai da tausayi irin nawa nasa aka baka aiki gashi kuma yanzu nace kaje wajan yarinyar idan ubanta har yanzu yaƙi yadda ta Aure ka kawai kayi mata ciki kaga ko babu komai dole a baka ita ka aura ni wallahi yarinyar ba tayi min ba" shi dai Shiru kawai yay yana Murmushi ita a dole shawara ta bashi idan kuwa haka ake bada shawara da an shiga uku.
Kwantar da Akeela Abbu yay a hankali kuma fara faɗin.
"Ummi!! Mami!!"
Mami ce ta fara fitowa idanunta ya kumbura sosai saboda kuka, baƙa kana ganinta kaga mahaifiyarsa Md Adnan zatai shekaru wajan 42 tana sanye cikin wani haɗaɗɗan lace, Zama tayi a kujerar dake farcing Abbu ba tare da tace komai ba.
Not too long Ummi ta fito daga part ɗinta hannunta riƙe da wata ƙyakkyawar Yarinyar zatai shekaru 4 haka fara ce sosai kamanin Akeem zane raɗau a saman fuskarta Amani kenan jika a wajan Alhj Bukar Bello ƴar kuma wajan Dr Abdul-hakeem Bukar Bello.
Zama Ummi tayi kusa da Mami tana sanye cikin wata orange ɗin lafaya tai mata kyau sosai zatai shekara 45 haka amma jikinta a murje yake sosai har tafi Mami gogewa da kuma wayewa.
"Barka da dare ya hanya" Ummi ta faɗa murya ƙasa.
Kallon su duk yay kafin fuska a ɗan haɗe domin bai fiya sakin fuska ba idan ba keɓewa yay da matansa ba yace.
"Kunga abinda ya faru da Adnan ko? Jikina yana bani yana raye kuma komai jimawa zai dawo gare mu, i believe cewa komai sai Ubangiji ya tsara mu ɗauki hakan a wata sabuwar ƙaddara daga Allah wacce ya jarabce mu domin gwada imanin mu, ko yarda na yarda cewa hakan ya faru ne dalilin shigarsa ruwan, amma ruwan ne dai kawai ya zama sanadi amma tuntuni Ubangijin AL-ARSHI ya tsara faruwar hakan a Lauhil Mahfouz..."
Da sauri Didi tace.
"Sadaƙallahul Azeem,amma dai Bukari ka cuce mu da baka zama malami ba ka rasa mai zakai sai siyasa, ai yasin naji daɗi daka sauka daga kujerar mulkin baki ɗaya, ai da wallahi har govmet hausi ɗin zani nace bada yawo na ni Uwarka idan suka zaɓe maka, haka kurum na fita waje a dinga shunani da baki ana gata can ɗan ta yana handime kuɗin jama'a"
Ta faɗa tana cuna baki gaba, shi dai Abbu bai ce komai ba domin yasan rikicin tsofa ne.
"To! Ubangiji ya dubi idanun mu ya sanya Adnan yana raye ya kuma dawo gare mu, Allah ka dubi halin da muke ciki"
A sanyaye Mami tace "Ameen" idanunta na ƙara kawo ruwa ajjiyar zuciya Abbu ya sauke kafin ya kalli Akeela yace.
"Ɗiyar Baffa ce da Baba Rabi dalilinta Adnan ya faɗa ruwan kuma Thank God Dr ya ciro ta..."
A nan ya kwashe labarin kakaf abinda ya faru ya basu.
Ihu da kuuu Didi tasa zani na faɗuwa tace.
"Kun kashe min Adnanu wallahi hisba zan kaiku"
Tana faɗin hakan ta nufi waje a hanya taci karo da Akeem dake shigowa fuska ya haɗe sosai ko alamun annuri babu.
Ganin haka yasa Didi washe baki tace.
"Yooo yanzu naji bayani ai cewa nayi bari na leƙa naji mai gidan Shiru fa"
Bai ƙara kallon ta ya matsa can gefe sallama ma ciki yay kai tsaye upstairs ya nufa wajan part ɗinsa.
Ganin haka yasa Abbu faɗin "Dr kazo ka duba Akeela" jin sunanta yasa Akeem yaji kansa ya sara Mami kam Miƙewa tayi domin tunda taji a kanta Adnan ya faɗa ruwa taji wata muguwar tsanarta ya cika Zuciyarta.
Da ɗan sauri Akeem ya ƙarasa haurawa saman ko takan Abbu bai bi ba ganin hakan yasa Ummi faɗin.
"Bari na duba ta"
Ɗaukan ta Abbu yay zuwa part ɗin yaransa mata, ɗakin duhu alamar duk sunyi bacci On yay na wutar bedroom ɗin Aleema,Afaf  duk suna kwance wajan Ameera da take zuwa hutu ya kwantar da ita, lokacin tuni Ummi ta ɗauko kayan aiki, cikin sauri ta fara duba ta ganin har yanzu da ruwa a cikinta yasa ta danna cikin da sauri sai ga ruwa na fita.
Tana ƙara dannawa Akeela tai hau yin tari.
Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke tana gama tarin kuma bacci ya ɗauke ta, sai da Ummi tayi mata injection  kana ta ɗaura mata drip Abbu yi yayi kamar bazai fita ba ganin kallon da Ummi ke masa yasa ya ɗan shafa kansa yace.
"Miss You dear, let's go"
Gaba yay ta bisa a baya  kana ta jawo masu ƙofa,
Daman p.a tuni yay masu sallama ya tafi gida.

A hankali bakinsa ke motsawa yana tasbihi can ƙasa zuciyarsa, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, cikin haɗaɗɗan parlonsa ya shiga komai na Parlon white ne.
Ya haɗu sosai har ba'a magana, kai tsaye wata corridor ya bi hadle ɗin ƙofar ya buɗe, wani irin lumshe idanunsa yay tare da sauke wani maraitaccen numfashi yaja tare da saukewa, saboda wani sassanyan ƙamshi daya daki hancinsa ya sashi lumshe idanun da bai niyya ba.
Tura kansa cikin bedroom yay bakinsa ɗauke da wata kamilalliyar sallama yana maida ƙofar ya rufe.
Derect bathroom ya nufa yana mai zare kayan jikinsa, a saman hanger ya saƙale tare da sakarwa kansa shower, a hankali yake sauke ajjiyar zuciya yana jin yadda ruwan yake dukan saman fresh skin ɗinsa.
Bayan yay wankan ya ɗaura alwala kana ta ɗauki wani long white towel ya dauraia wist ɗinsa, ko kansa bai tsane ba ya fito ruwa na sauka daga sumar kansa zuwa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa.
Wani irin ɗaci bakinsa yake masa rabon da yaci abinci har ya manta wajan fridge ya nufa ya ɗauki Apple da cake ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya ajjiye.
Wasu haɗaɗɗun nightwear slik Pajamas milk colour, a hankali ya miƙe tare da goya hannunsa a bayansa ya ɗan fara tafiya yana mai karanta addu'a yana bin duk kusurwa ɗakin da tofi bayan ya gama ya kwanta saman bed ɗin tare da jan duvet ya rufe jikinsa, gaba ɗaya ya ƙasa bacci tunda matarsa ta rasu wajan haihuwar Amani baya iya cikakken bacci ya saba da jikin mace sosai duk da auran kamar na dole ne bai so amma ya saba da jikin matarsa ainun.
A haka bacci ya ɗauke sa.

Misalin 4 na dare ta shiga buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi kanta na sarawa sosai, hannunta mai ɗauke da carnoner ta kala ɗan marai-raice fuska tayi kamar wata ƴar baby Wanda ya sanya manyan dimples ɗinsa bala'in lomawa.
A hankali kuma ta shiga bin bedroom ɗin da kallo sosai gabanta ya faɗi ganin bata dan ɗakin ba, jiki babu ƙauri ta miƙe tsaye tana Miƙewa gashinta ta sauka har wajan manyan ass ɗinta.
Da Mamaki tabi jikinta da kallo ganin wata Robe Nightgown silver wacce ta sauka iya laps ɗinta gaba ɗaya manyan gwayen ƙafafuwanta suna waje ga wani gashi da yay kwance lub a saman fatar ta.
Shanyayyun idanunta wanda kullum suke a Lumshe ta ƙara buɗe, jikinta babu ƙwari ta nufi ƙofar data gani, tana tafe ko'ina na jikinta moving yake kamar tarwaɗa.
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita ita bama ta san dare bane sai da ta fito parlon daga duhu ga wani masifafan sanyi na Kaɗawa, da sauri ta matse jikinta waje guda ta shiga taune bakinta kamar wata ƴar turawa haka ta zama cikin nutsuwa take tafiya harta isa tsakiyar Parlo tana zuwa zata shige taji an sanya mata ƙafa baya tayi tare da hantsilawa zata faɗi wata kuma ƙyakkyawar Ajjiyar zuciya ta sauke jin ta faɗa saman ƙirjin mutum...

😂Abbu ya biyo dare jama'a

*TSINTACCIYA*
Na kuɗi ne kada ki siyi litaffi na idan kin san zaki fitar🤷🏾‍♀️.

NRML GRP: ₦300
VIP: ₦500 POSTING SAFE+YAMMA
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK, PLEASE MASU VIP IDAN DA HALI A TURAN TA BANK NA AKWAI P.O.S MA A GARI. EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616

*FITATTU HUƊU*

BAƘAR FATA
  Autar manya

DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo

SULTAAN
Mss flower

Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank, masu tura kati kuyi magan ta nan 08167888934, za ku tura Evedance of payment ta nan 08142105218 ƴan uwa na Niger ga number ku +22796515805

 

*SARAUTAR MARUBUTA*

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now