page 2

1.2K 21 1
                                    


“Tsundum” sautin Amon faɗawarsa cikin kogin ya bada, kafin kuma wasu manyan ƙwayaye su fara firfitowa alamar wanda ya shiga cikin ruwan yana fidda numfashi.
Malam ne ya sauke Ajjiyar zuciya tsoro duk ya cika masa zuciya, Musamman like Md Adnan did! Yay Wani good jum before he fall in to the river.
Cikin damuwa Malam ya kalli Drive yace "Yadai iya ruwan sosai ko? Nasan Adnanu gwamma shi da ɗan uwansa, bana son rasa rai biyu a lokaci guda, Akeela nada matuƙar muhimmaci a rayuwata haka Adnanu"
Shiru Driver yay domin like serious bai san komai ba amma dai yasan Adnan na yawan shiga wani ruwa.
Isiya ne yace "Uhm yadai iya ruwan ko?" Kallonsu driver yay kafin yace.
"Not sure! Amma Ƙaramin Mai gida yana shiga swwiming pool sosai yana son wasan ruwa, ta takalmin taya, amma dai ruwa kamar wannan bana da tabbacin yana shigarsa"
Malam ya kalli ruwan yace.
"Allah ka taimaka ni, ka duba lamarin wannan yaran"
Juyawa Driver yay yace "bari na kira taimakon kwanakwana incase"
Wajan motar ya nufa ya ɗauki Wayarsa tare da fara shiga goggle yana duba yadda zai samu impormation na ma'aikatan mafi kusa da garin.

Md Adnan wani numfashi yaja mai wahala yana jin yadda numfashin nasa ke wata fisga kamar zai bari ƙirjinsa.
A hankali kuma ya ɗaga hannunsa zuwa sama kafin ya ware legs ɗinsa, idanunsa dake a rufe ya buɗe yana kumbura bakinsa tare da fidda numfashi.
Girman ruwan da yadda yaga ruwa yay bala'in firgitar sa.
Cikin sauri kuma yay baya da hannunsu yana ware ƙafa tare da fara nutsu cikin ruwan yana ninƙaya, ya ɗauki good 10minutes yana duban Akeela amma babu ita, yana ƙoƙarin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana jin wani reshe na baƙin ruwan daya riƙe mata riƙa.
Hijab ɗin jikinta tuni ya zame yay gaba, gudun ya ƙara yana cimma ta yana gab da zuwa inda take wata igiyar ruwa ta riƙesa cikin kuma rashin Sa'a Wani irin ruwa mai yawan gaske ya tawo cure guda.
Wani kalan ware idanu Md Adnan yay kafin yay wani yunƙuri na guduwa ruwan yay gaba dashi ji kake "Shuuuuuu" sautin gudan ruwan ya bayar.
Dawo Driven yay yana faɗin "na kira, in sha Allah dukkan su noting will happen to them" Cikin damuwa Malam yace "Amma ko motsi babu, ji yadda ruwa ke gudu tsoro ya kamani sosai" "aifa da tsoro mutane har biyu ga wannan bawan Allan da gani bai saba da wahala ba" cewar Sunusi yana mai ƙara leƙawa cikin kogin.

A can cikin motar Md Adnan Wayarsa ce take ta ringing kira na wajan uku kenan amma babu respond! A hankali motar da fara shigewa wani matashi ya fara knocking Ƙofar motar hannunsa riƙe da wayarsa yana ƙara danna number Md Adnan yana mamakin abinda ya tsayar da shi har yanzu bai ƙarasu ba gashi lokaci na tafiya.
Daga cikin motar wani mutum ne mai kimanin shekaru 32 a duniya, yana zaune a back seat idanunsa maƙale da wani farin glass na haɗaɗɗun goyon nan.
Sanye yake da wata fitinanniyar Double breasted suit dark Maroon. Gashin kan nan nashi yay kwance har wuya daga gaba ya kwanto, sai ƙyalli yake yasha Ginger Geminal Oil hair.
Kakkauran laɓɓansa pink irin yirr ɗin nan lokacin zuwa lokacin yana taune su like his punishing kansa, fari ne tass irin farin nan da kai tsaye ba zaka iya tantance na wani ƙasa ko kuma jinsi ba, yana da kyau sosai looking soo damn sexcy and hot!
Irin manyan mutanan ne masu tashe da zamani irin definition of classic masu fama da mahaukacin kuɗi na halak.
Idanunsa ya janye daga kan haɗaɗɗiyar ƙaramar Apple system ɗinsa yana maida idanunsa Submariner Rolex ganin lokacin yaja ya ɗan saki siririn tsaki.
Deep down kuma zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi, like something bad gonna happen to him.
Irin mutanan ne da wahala ka fahimci sauyin fuskarsa, farin ciki da damuwa baya sanyawa kaga sauyi a saman fuskarsa.
Yana da kamilalliyar fuska mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa abu guda ke sauya masa tunani yaji ana masa ihu a saman kansa, ko kuma yaga anci zarafin wani ɗan Adam.
Zame system ɗin yay tare da ajjiye ta a gefensa, cikin nutsuwa ya fara juyawa laɓɓansa yana motsawa a hankali.
A taushashe sautin fitar amon muryarsa ke tashi yana faɗin.
_“Asstagafirullah, Walahamdulillah, Wallahu Akbar”_ shine Amon kalaman dake fita a bakinsa.
A karo na wajan huɗu P.a dake tsaye daga baƙin ƙofar ya ƙara Knocking ƙofar, taɓe baki yay kafin ya ɗaga hannunsa tare da danna glass ɗin motar yay ƙasa.
P.a ne ya kalli mutumin cikin motar yace.
"5times ina kiran number Md amma no answer"
A karo na farko bayan sauke glass motar  Dr. ABDUL-HAKEEM BUKAR BELLO ya ɗaga idanunsa tare da kallon P.a idanunsa kawai ya juya da sauri P.a yace.
"Ok lemme try it"
Ya faɗa yana ƙara danna number Md Adnan, kafin kuma gently ya miƙa hannunsa ya buɗe murfin motar, kamar bai so haka Dr A.b ya fito da ƙafarsa kafin kuma ya fito daga motar baki.
Lumshe idanunsa yay saboda iskar ƙasa da ƙamshin sabbin shukokin da akai da suke dukan hancinsa.
Yana da tsayi da faɗi jikinsa a murɗe yake ga wani faɗin ƙirji da yake dashi _(Physique chest)_ bayyanar ƙwayar idanunsa a yanzu ya tabbatar cewa shi ɗin _(Half-caste)_ ruwa biyu kenan.
Zare jacket ɗin yay ya saƙala a hannunsa yana mai sassauta necktie ɗin wuyansa.
"Sir har yanzu ga, gashi mun tara mutane sun taro mu kawai suke jira"
Taɓe baki yay walking slowly ya nufi wani ma dai-dai cin waje da aka gyara yay ta tass ga kujerar da aka sanya masa.
Maida wayar P.a yay zuwa aljihunsa yana mai mamakin abinda ya hana Md Adnan ɗaga wayar da kuma mamakin rashin ƙarasuwar sa is anything okay Babu damuwa ai rashin sanin dalilin shine damuwar.
Waje Dr A.b ya samu wanda wasu jama'ar suke kiransa da AKEEM ya zauna yana mai sassauta haɗewar fuskarsa saboda ganin duk manya ne a wajan wanda shekarunsu, suka ja ainun.
Cikin mutunci ya buɗe bakinsa a nutsu yace "Assalamu alaikum warahamatullah"
Gaba ɗaya mutanan suka amsa masa kafin yay Shiru yin shirun nasa ne kuma yasa P.a dake gefensa a tsaye yace.

TSINTACCIYAWhere stories live. Discover now