4

732 102 5
                                    


*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 4*

Maimartaba *SARKI SULAIMAN ABDULLAHI KARGI* Shine sarki na goma sha Takwas Dake kan karagan Mulkin Garin na Kargi gabadaya bayan rasuwar mahaifinsa Abdullahi Sulaiman ya gaji Sarautan awajensa.
Garin na Kargi karamin gari ne mai Cike da Tarihi kamar yadda kuka sani kuma Ita Kargin Tana garin Kubai Local Goverment ne Dake Jahar Kaduna.
Kowa ya san Masarautar garin Kargi babban Masaurata ce da kowa ya sanu mai Dimbin Tarihi Masauratace mai Fadi da Tarihi Tun azamanin baya ana Al"adun gargajiya kafin Boko da wayewa yazo mana ammh duk da Haka basu yadda Tsofaffun al"adun gargajiya ba har yau har gobe  akwai tsofaffun al"adun da Masarautar ta Kargi bata manta dashi ba.
Sarautar Tana ta Tashi Daga Gida Dayane Ashekaru Talatin da suka Gabata Sarauta ta Dawo Dakin Sarki su Sulaiman,Tun bayan Da tar bar Dakin su Marigayi Sarki Hamza,wanda Lokacin da Sarkin kargi na Uku ya Rasu sai sarautar batar gidansa ba ita ta Dinga Zagayawa Tundaga kasa har ta Dago sama,har zuwa yau da Sarautar ta koma Hannun Sarkin Sulaimam Abdullahi shi din kuma ya kasance Uhum uhum din Marigayi Sarki Hamza ne Tundaga wannan Lardin.
Kowa yasan Masarautar Kargi Masauratace adala mai adalci da Sanin ya kamata mai Kula da Hakkin Talakawa da kwatatan adalci a Tsakanin Mutane tun a shekarun baya Mutanen Kargi basu Taba kuka da Sarautar garinsu ba ,domin Adalan Sarakuna ke Hawa in wannan ya Shide wanda za"a Zaba sai yazo ya Dokesa a kwatatan adalci Atsakanin Al"uummar da suke mulka kowa yasan su Wajen Daukan Talaka da masu Sarauta Dayane awajensu Tun a Zamanin baya Daular Masarautar sun sha Rike ya"ya mata da basu da gata su kuma aurar dasu ga amintattun Hadiman Masaurata shiyasa Kowa ya Bude baki sai dai kaji yace Masarautar Kargi ai baya goya Marayu ce kuma ita din Buhun Siga ne kowa ya Rabeki sai ya Dankwali Zaki.
Tun azamanin baya Kowa yasani basa Fita waje su yi aure gabadayan su Daga kan iyaye da ya"yansu da Kannensu Dukkansu auran Gida ake yi musu Da"n wanchan da Da"n wanchan ake Hadawa Shiyasa Gabadayansu yanayinsu Daya da kamminsu sannan suna da Tarin yawa da Yalwar Zuru"a wanda ba nuna Bambamci Tunda gabadayansu Daya suke kuma na Gida ne.
Wannan al'adar ita suke rike kuma suka Taso tashi Har zuwa kan Iyalan Sarki mai kan karagar Mulki Wato Sarki Maimartaba Sulaiman Abdullahi Sulaiman.
Maimairtaba Sulaiman Abdullahi ya Hau karagar Mulki Shekaru goma da suka Gabata Lokacin da Maimartaba Mahaifinsu ya rasu akwai yan sauran Daki da yawa Tunda Mata Hudu Reras yayi Rayuwa dasu Biyu sukayimai Takaba Biyu shi ya Rufesu,akwai Tarin ya"ya Maza da mata dayake da su,Kuma Mazan kamar su Hudu suka Fito Takaran Sarautar Alokacin Sarki Sulaiman ma bai Nuna Sha"awar Sarautan ba saidai da Wakilai suka Zauna sai aka gano yafi su Chanchanta Tunda shiyayi ilimin Boko mai Zurfi har yakai matakin Master yayin da Sauran suka fi karfi wajen Ilimin Muhammadiya Allah ne ya Bama Sarki Sulaiman wannan Sarautan ammh bai Taba Zato ba kuma Dayake suna da kyakyawan Hadin kai gabadaya yan"uwansa sukayi masa Mubaya"a suka mai Fatan Alheri Domin kowa yayi shedansu Wajen Hadin kai da Zaman Lafiya.
Sarki Sulaiman Abdullahi yana da Matan Aure Biyu ne Fulani Itace Uwar gidansa ita kuma din jikar Sarki ce Domin marigayi kakanta ya Taba Mulkan Masarautar garin na Kargi,aka Hadasu auran Zumunci a Tsakaninsu bayan ita sai ya auri Kilashi Itama din diyar diyar masu Masarautar Kargi ne ta Dakin Hajiya Uwa mai Dakin Saasa cikin Matan Marigayi Hamza itama aka Hadasu auran Zumunci.
Dagasu bai kara sha"awar kara aure ba Duk da Tarin Ya"yan da ake kawo masa matsayin ya aura bai maida kai ba Fulani ya aureta ne tun kafin ya Zama Sarki bayan ya zama Sarki sai aka Bashi Kilashi alokacin.
Ya"yan Sarki Sulaiman Abdullahi sun kai Ashirin in ma basu fi ba Saboda Duka Dakunan suna Haihuwa sosai,yana da manya ya'yansa Mata wadanda ya aurar dasu suma acikin Dangi da yanzu sun zama kakkani Saboda sun Hayayyafa da Ya"ya da jikoki.
Sai da ya jera Mata Ta kwas kafin ya Fara Haihuwan ya"ya Maza acikin Matan Hudun Farko sune suka Tsaya Hudun karshe kuma Sun Rasu Ta Farko akwai Hajiya Zinatu wacce ake Kiranta Hajiya Uwa Domin ta zama Uwar kuma Allah ya bata Girman Duk Gidan Maimartaba itace Babba acikin Masaratar alokacin,Daga Hajiya Uwa sai Hajiya Mandiya,kamar Uwa suke dukkansu Biyu suna aure anan garin Kargi ne,Sai Jamila wacce itama Take aure anan garin Kaduna itama Dan cikin Masaurata take aure,Daga ita sai Bilkisu mai gadon Zinare Wacce Take auran Babban yaron yayan Sarki Sulaiman,dan kasuwa ne mai kudi sosai suna Zaune agarin Lagos ita da Iyalanta da mijinta.
Daganan ya Fara Haihuwan ya"ya Maza Lawali ne Babba sai Sa"idu sai magaji Abdullahi kenan Sai Aliyu suna da Sauran kannensu mata irin su Hauwa"u,Zainab,Hadiza da Sauransu akwai kananun yan Jerin Karshe irin su Salamatu da ake Kira Salame da Kaltume,Dukkansu ba wacce ba"a aurar da ita ba Suna da kananan shekaru ake karban kudin auransu da sun tasa sai aurr karatu zamani Ki cigaba adakin mijin sai dai na arabiyan sai kin Haddace Qur"ani za"a zAuna aasan wanda za"a Hadaki ba auran soyayya suke yi ba ammh Biyayyan da Hakuri yakai su ga wannan Matakin
Zabba"u Tana daga cikin ya"yan da Sarki Sulaimam ya rike Mahaifinta shine Autansu a Dakinsu Sun Rasu shi da Matarsa Asiya asakamakon Hadarim Mota suka bar yarsu kwara Daya Zabba"u wacce Ta dawo wajen Sarki da Zama Fulani ta Hadata da Salame alokacin ta rikesu Gam kamar ya"yanta in ba Fadamaka akayi bazaka Taba Tsammanin Ba Sarki da Fulani suka Haifi Zabba"u ba.
Lawali da Sa"idu duka sun Fita Daga Gidan Masarauta Lawali yana garin Gombe chan yake aikin gwannati da Hukumar agajin gaggawa,sai Sa"idu dake garin Zaria yana lecturing a Federal collage of Edu dake nan Zaria kuma anan yake Zaune da iyalansa Magaji yana Masarauta Domin shi ke kula da Babban Gidan Gonar Maimartaba yana Zaune da iyalansa anan garin na Kargi.
Sai Aliyu Dayafi Zurfafa alimin Zamani Domin yakai matakin Phd akaratunsa akan Harkan kasuwanci yayi karatunsa na Degree a Abu Zaria Degrre dinsa na Biyu a Universty of Ibadan Daganan ya Haura kasar Amurka ya Hada Phd dinsa akan Harkan Dayafi kwarewa kan kasuwanci Aliyu Allah ne ya Dorasa kan Kasuwanci da kuma Baiwa Domin yasan Harkan sosai komai ya saka Hannu sai yayi albarka Tun kafin ya mallaki kamfani ya Fara Safarar sai da kayan Fatan Hada jakunkuna da Takalma karon Farko Tun kafin yayi karfi ya Hada Hannu da Jajayen Fata da manyan ma"aikatu ya Zuba Hannun Jari kuma alokacin Kafin ya baro kasar Amurka yayi aiki da wani Babban Kamfanin Sarrafa Fata zuwa Nau"in ababen da ake Sarrafashi da Fata kuma yana Shigowa dasu Nageria har suka Samu Karbuwa.
Tun Tasowar Zabba"u Sarki Sulaiman Abdullahi ya Zabama Dansa Aliyu ita Domin ta kowani bangare sun Dace Zabba"u tun tana Karamarta Macece Tsayayyiya mai Dakiyar Zuciya mai iko da Izza Sannan ita Jinin Sarauta na yawo sosai ajikinta kodaga ganin Takunta da yanayin mganarta sai ka Rantse ga Allah Sarki Sulaiman alokacin shine Shakikin Ubanta ko amakaranta batakai su Salame nuna Izza ba ita abun nata a Fili yake Zabba"u tana son kyale kyale sosai da Harkan Jin Dadi Tana da wayewa sosai Shiyasa Sarki Abdullahi yayi ma D'ansa Aliyu Sha"awarta.
Kuma lokacin da Hadin ya Fito Sarari Zabba"u tayi Na"am da Hadin sosai Domin tun kafin haka tasha yin Sallar Dare akan Allah yasa Sarki yace Aliyu Zata aura Domin Kaf Masarautar da ya"yan Dangi bata ga wanda ya Dace da ita ba irinsa shi kuma bai Damu ba Biyayyah yayi ma Mahaifnssa Tunda baya Zama alokacin sai yayi wata bashi agida Duk acikin ya"yan Sarki shi kadai ne yake yawaon Kashashen Ketare.
Tare akayi auransu da Salame itama Yaron Yayan Sarki Sulaiman Aka bata Shi dan Siyasa ne anan garin Kaduna da Farko kafin suyi kaura su koma garin Jos da Zama,nan garin Kargi Aliyu ya Fara ijiye Zabba"u Saboda Har yanzu kafarsa bata tsaya waje Daya kuma Cikin ikon Allah adakin Fulani aka Haifi Sulaiman Fulani da Kilashi su suka karbi Haihuwansa cikin Taimakon anguwan Zoman Masarauta alokacin Aliyu baya nan yana garin lagos yaje wani Taro,Aka Kirasa a waya aka Sanar dashi Haihuwan Zabba"u Ana kuma gayamai ya sanar da Cewa Takwaran Takawa ne wato Sulaiman wannan abun ya Farantama Sarki sosai kuma Tundaga Lokacin Allah ya Dora Kauna mai Tsanani a Tsakaninsa da Jikansa.
Amasarauta akayi shagalin sunan Sulaiman,anyi yanke yanke sosai da Shagalin wannan sunan Sarki yayi Bajintar sosai bajintar da bai taba Yi ba Duk Haifafan da ake yimasa yace wannan Jikan na Musamman ne Jikansa Sulaiman yana Fata watarana ya Gajesa.
Sulaiman shi dan Masarauta ne,Domin anan kargi ya Fara Rayuwarsa,kullum yana Fada Tare da Sarki shiyasa sukayi matukar Shakuwa Tun yana karami ya samu Dubaran zama da manya da sanin Hikaman Zence acikin Gida kuwa kamar ba Zabba"u ta Haifesa ba Domin Fulani da Kilashi sune iyayansa.
Sai da sulaiman yakai kimanin Shekara Tara kafin Aliyu yazo ya Tattarasu su koma garin kaduna da Zama inda ya Fara aiki da Wata ma"aikatan Sarrafa Fata alokacin kuma Zabba'u tayi ma Sulaiman kanne Bayanshi ta Haifi Sadiya da Fadila Duka mata alokacin ita Salame tana chan sunaneman Haihuwa ba asibitin da basu je ba Tundaga Gida Nageria har kasar waje ammh amsa Dayane ance Lafiyansu kalau.
Sulaiman da Sarki yake kiransa Saraki Tun yana yaro kuma afada dashi kowa ya sanshi ya Fara karatun Boko anan Kargi na addini kuma yayi ma Sa'o"insa Zarra sai bayan komawarsu kaduna suka fara Sabuwar Rayuwa achan
Shekaru suna Tafiya abubuwan Cigaba suna kara Faruwa alokacin Hajiya Zabba'u ta kara Haihuwan Fatima akuma lokacin ne Alhaji Aliyu ya kara aure da Matarsa Falmata yar Maiduguri ce,Diyar uban gidansa ne dayake matsayin Manajan dayake mai aiki a ma"aikatansa ya wanke Falmata ya basa Daya nuna basa auran wata mace Daga waje Har Masarauta yaje ya samu Maimartaba suka gana ba wanda yasan me sukace ma juna ammh Maimartaba karo na Farko ya amince Falmata ta shigo Cikin Zuru"arsa Ita kadai ce bare ta Farko Da taba Shigowa Cikin Zuru"arsu Shiyasa afarkom auran ta Fuskanci Kalubale sosai Daga Dangin Mijin nata Sai da Takawa ya tsawarta kana Alokcin Zabba"u ta koma amsa sunan Hajiya Zabba"u mai Iko da Izza auran Aliyu kamar Rufa ido bata isa taja da wannan ikon ba Allah ya Kaddara hakan sai dai ita kanta Falmata duk da Mahaifinta nada kudi bata yadda ta Nuna Zata shige gaban Zabba"u ba Dole dai ya kasance itace abayanta akomai na Gidan itace ke da Jagoransa Dayake ta iya Kissa da Zamba irin na wadanda suka Tashi a Gidan Sarauta Hajiya Zabba"u tasan kan kissa da Kissina Dashi take siye kowa Harda kuwa shi kanshi maimartaban.
Auran Falmata da Aliyu yazo da wani Budi sosai,Domin ashekaran Farko ta Haihu yarta Mace Radiya,daga ita sai Raliya,sai Hauwa"u sai tayi yan Biyu Mace da Namiji Sadiq da Saddiqa wadanda aka Haifesu kusan kai Daya da autar Hajiya Zabba"u mai suna Sadiya Halimatis Sadiya.
Zuwa Lokacin Budi da Kyakyawan Rayuwa ya Dabaibaye Aliyu ya samu Nasaran Gina Ma"aikatansa na Sarrafa Fata agarin Abuja mai suna A.S.KARGI ENTERPRISES wanda ya Bude shi da Taimakon Maimartaba da Sauran yan"uwansa Hade da Tallafawan Uban gidansa Alhaji Bukar gana Mahaifin Falmata wanda Bai ma ga Bude Ma"aikatan ba Allah yayi mai Rasuwa Sakamakon Hadarin Mota,alokaci Daya tare da gina makeken gidansa Dake Garki Abuja suka koma chan da zama.
Sulaiman ya taso da Burin Mahaifinsa Domin Alhaji Aliyu jajrtattace ne kuma Tsayayye duk acikin su shi ya dauko Hallayar Takawa na Juriya da Hakuri da naci kan abunda suka sakama Gaba Sulaiman bashi da Role Model irin mahaifinsa Shiyasa yake da Burin shima ya Zama kamarsa Watarana.
Alhaji Aliyu yaji matukar Farincikin Jin Sulaiman zai karanta Kasuwanci Shima bayan ya gama Karatunsa na Secondary anan Jami"ar Abu yayi Degree dinsa na Farko,Azuwa Lokacin Sulaiman yasan shi dan gata ne ta bangaran Hajiya Zabba"u da kowa ke Kiranta Hajiyarmu,da Mahaifinsa da shi kanshi Maimartaba Sarki Sulaiman Musamman Sulaiman ke zuwa Hutun karshem Sati Daga makaranta Saboda su samuZama da Sarki su Tattauna da Matayensa Tsofaffi Fulani da Kilashi Shiyasa kaf Jikokin maimartaba Soyayyar Dayake ma Sulaiman nadabam ne Kowa kuma yasan haka yafi kowa saninsa da Shakuwa dashi Duk wani abu na Sarauta Sulaiman ya sani sai dai bai maida Hankali ne saboda bashi da Sha"awar Sarauta kamar yadda Kakan nashi ke Buri watarana.
Laila Diya ce kwara Daya wajen Hajiya Salame Diyar da"a ka sameta bayan an cire rai da samunta Tun bayan ita kuma Hajiya Salame bata kara Haihuwa ba Wato Laila Taga gata iya gata kuma Tana kan ganin Gatan har ya baci ta Sangarcr sai abunda Taga dama Take yi Tun tasowarta gidan Su sulaiman take Hutu Saboda Shakuwar da kawancen Dake Tsakanin Hajiya Zabba"u da Hajiya Salame da kudurin suna son Hada Laila da Sulaiman aure sun yarda da Hakan kuma sun yi Na"aman batare da sun Taba Shawara da kowa ba Hajiya Salame bata da aminiya ko kawa kamar Hajiya Zabba"u kamar yadda itama bata dashi Hajiya Salame ko yan"uwanta da suka Fito Ciki Daya basu santa Ciki da Waje ba kamar yadda Zabba"u tasanta itama tasanta kai ko Fulani bata isa tasan Taakaninsu ba Shakuwarsu ta zama abun kwantance Sannan Hallayarsu tazo Daya duk da akwai wadanda suka Bambamta kamar Izza da ikon Zabba"u Salame bata Cika Dagawa ba in bama Fadi take yi sai taje waje ta fito ba wanda yasan ita din Jinin Sarautace Sabanin Zabba"u duk inda ta shiga yanayinta Kadai ke sa ka gane cewa Jinin Sarauta yana yawo acikin Jikinta.
Alokacin da suka so bayyanar da Kudurinsu sai wata Kaddaran ta Gifta Sulaiman yaci karo da Sunaira akan Hanyarta ta dawo Daga makaranta akaduna Lokacin sun je Kaduna Tunda awatan suka shiga Camp anan Kaduna,Haduwar da Allah yayi Ikonsa alokacin aganin Farko da Sulaiman yayi ma Sunaira ta gama Tafiya da Duka Tunanunsa da Zuciyarsa alokacin Daya rika binta har yaga Gidansu bai Tuna da al"adunsu na Auran junansu ba Idonsa ya Rufe adaran bai bari gari ya waye ba ya isa ga Sunaira ya Fadamata Sirrin Zuciyarta alokacin Sunaira Tana da Shekaru shatakwas ne aduniya Tana Shekarar karshe a makarantar Secondry ayayinda Yayarta Sunaima Take Makarantar Nursing na Barrau Dukku Dake Zaria sai sun samu Hutu take zuwa Gida.
Mallam Abdu Datti Haifffan garin Zuntu ne Dake nan jahar kaduna,Daga shi har matarsa Rukayyah yan chan ne,ba auran zumunci bane sai dai auran na gani ina so Mallam Abdu Datti yayi karatun boko yakai matakin samun kwalin Degree da kwalin Shaidar Educatuon abangaran Karatunsa,afarkon Rayuwarsu azuntu suka fara domin Sunaima itace yarsu ta Fari agarin Zuntu suka Haifeta har ta Fara makaranta sai bayan Shekara Biyar suka samu Sunaira alokacin ya bar koyarwa a makarantan Secondary Zuntu,lokacin da gwannatin Kaduna tayi Chanjin ma"ikata sai ya nema ya samu Headmaste a wata Makaranta Dake Hayin dan mani Dake Kaduna.
Sun dawo anguwar Dosa inda ya Siya Karamin Gidansa Daidai gwargwardo na Talaka Sunaira tana karama.
Tsakanin Sunaira da Ahmad Shekara hudu ne aka Haifesa Daga kansu kuma basu kara haihuba sai suka Rumgume ya"yansu uku suka Rikesu Bisa amana da Kiyaye kiwon da Allah ya basu.
Tun atasowarsu kowa yasan Sunaima bata da Hayaniya,tana da kamewa da Kawaici Sabanin Sunaira Yarinya mai Fara"a da Barkwanci ga Sakij jiki da Faram Faram da Mutane Inna ta gado Domin Inna haka take Da ya"yanta kamar Jikokinta da Mijinta kuma yayanta Tana da Fada da Mita ammh akwaita da Kirki Ballatana Mallam Abdu shima yana da Kirki da Dattako ga Kamewa da sanin ya kamata ta wani Fanni shi Sunaima ta Dauko arashin Sakewa Bata da yalwar Fara"a kamar sauran kaninta tun suna Zuntu Dangi suna Tunanin saboda Rashin Bata da kani ko kanwa yasa take Shuru Shuru sai dai Lokacin da aka Haifi Sunaira ma bata Sauya ba sai aka Fahimci Halinta ne Kuma Hali ai Zanen Dutse.
Tun tasowar Sunaima bata da wata Kawa ko abokiyar Hira Kawarta Dayane Inna Duk kuwa da basa Shiri Inna mita da Fada ita kuma Sunaima Kyaluwa da basarwa Tun Tasowarta Bataan kowa ba sai iyayenta da Danginta Daga baya kuma ta samu karin yan"uwa.
Sunaima bata da kowa sai kanwarta Sunaira itace abokiyarta kawarta kanwata da sukayi matukar Shaku da juna da karamin kaninsu Ahmad Daya kasance sanyin Idaniyansu Ahmad irin Inna ne barkwanci da ban Dariya Karya ne ya Zauna Dakai bai saka ka Dariya shida Sunaira kullum Cikin Fadan Sako suke suna barin Inna da Mita,Sunaima sai dai Ta kallesa tadan Murmusa ita ba kasafai Take Dariya ba Kamewarta Har tayi yawa Shiyasan yan anguwa sun fi Sabawa da Ahmad da Sunaira sune na Jama"a sai dai kaji mutane na Fadin kannenta sun Fita Fara"a da Som Mutane tun ana ganin abun nata Hallita ne har wasu suka Fara Dubarta amtsayin mai son Girma da Izza ita ba yar kowa ba.
Tun da ta gama makarantar take sha"awan karatun aikin Asibiti Dayake Tana da Kokari sai Malam Abdu Datti ya Shiga ya Fita har ta samu kurbi a Makarantar Barau Dikko Dayake Zaria shima da Taimakon Wani dan malajisar su na Zuntu gidansu Daya da Malam Abdu Datti da kuma chanchantarta yasa Ta samu Gurbi a wannan makarantar Iyayenta suka Tattarata tatafi sai sun samu Hutu take zuwa Gida Sunaira da Ahmad sun fi kowa Shiga Damuwa da Tafiyarta Haka zasu Zauna Shuru shuru basu da wani Sakewa sai Sunaima ta dawo kuma bata da wani Hira sosai ammh ita din wata abace mai Soyuwa garesu Suna abunsu Tana gefe Tana kallonsu Tana Mirmishi hakan kawai ya ishesu Sunaira ita ta Fara Samata sunan Antynmu sunan Daya Bita Har yan makarantansu da Yan anguwa da makota da Danginsu na Chan Zuntu sunanta ya Bace Daga Sunaima ya koma kowa Antynmu Saboda Shekarunta sun kai akirata haka har kuma alokacin Sunaima Bata Taba bama wani namiji Fuska ba,Sun samu Bambamci da Sunaira ita tun Tana da kananun Shekarunta allah ya bata Farinjinin Samari yayinda ita Sunaima bata da wannan Farinjinin Kamar hakan yana Tare da Kaddaranta ne maza da Dama suna Tsoron mata mgana suna ganin Tafi karfinsu tana da Kwarjini sannan bata da Sakewar da Namiji zai ga Fuska a wajenta.
Tana Shekararta ta Biyu amakaranta Mganar Sulaiman da Sunaira tataso har aka gama Takaddaman aka Daidaita aka sanya Lokaci Wata Biyu Sunaima bata sani ba tana makaranta,A mganar auran Sunaira da Sulaiman an shammaci wasu mutanen sosai Ciki harda da Hajiya Zabba"u da Hajiya Salame domin Lokacin da Sulaiman ya samu soyayyar Sunaira bai Tsaya wasa ba ya shiga har gida ya gana da Mahaifinta yaga Inna kafin kace me ya Zama Dan gida,Saboda Nagartansa da Dattakonsa Kuma bai taba Fadamusu shi jikan Sarkin Kargi bane saida neman auran ya shigo..
Da fari Sulaiman Maimartaba ya samu da mganar kai Tsaye bai ce komai ba sai dai aransa Daman yasan Watarana Sulaimam zai gaji Mahaifinsa Sarki Da kansa ya Kira Alhaji Aliyu ya sanar mai da Batun Sulaiman yaso da Farko ya nuna A"a Maimartaba yace Za"a karboma Sulaiman auran wacce yake so.
Kuma ahaka ya kira sauran ya"yansa ya shaida musu ba kuma wanda yayi musu sanin Sulaiman ai Dan Gatan gaban goshin Maimartaba ne batare da sanin matan ba Maimartaba da kansa yaje Har Fadar Sarkin Zuntu ba Sako ba ya Karbo ma Sulaiman auran sunaira.
Wannan abun ya bama kowa mamaki an Dade ana Aure ammh Maimartaba Sai dai ya aika baya zuwa da kansa sai dai yayi aike,sai gashi yau da kansa yaje Su kansu Dangin Malam Abdu Datti sun sha mamaki Daya Fada musu Takawa ne da kansa Sarkin Kargi yazo neman ma jikansa Auran yar"su wannan abun alfahari ne Da Fariya Dayasa tunda abun na Sarakuna ne sai suka kai mganar Wajen Sarkin Zuntu shi kuma ya karba ya Zama Uban Amarya aranar akuma lokacin aka gabatar da kayan nagani ina so da Sadaki Dubu dari Uku Da kayan Amarya akwati guda da kayan abinci aka kuma saka Rana nan da wata Biyu aka tashi,sai dai Malam Abdu Datti yazo da kaya Niki niki shi da jama"ar Zuntu suka zo suna Labarin Irin Dattako na Sarkin Kargi sai alokacin Sunaira tasan waye ainihun Sulaiman,Tasha mamaki sosai Bata zata Allah zai kaita wannan Mtsayin ba,Data Kirasa sai ya Fara mata Dariya Daman mamakin yake so ya bata.
Ai fa ansha mamaki haka su Hajiya Zabba"u sukaji abun kamar Daga sama Ita da Salame sun yi kamar suyi Hauka wajen nuna kin auran ammh ba Fuska Daga wajen Alhaji Aliyu zuwa wajen shi kanshi Maimartaba Sulaiman sai Lokacin yasan Kudurin Turo Laila Gidansu kuma shi baitaba Sonta ba yana kallonta kamar Sauran kannensa ne su Safiya da Fadila da sukayi aure dukkansu anan garin Abujan,sai Fatima datake aure garin kano Sadiya itace auta batayi aure ba Karatu take suma su Raliya dukkansu sunyi aure yan Biyu ne kadai da Sadiya ke gabansu yanzu.
Ba Barazanar da bai gani ba akan ya bar mganar Sunaira sulaiman yaki ganin ba Riba yasa Hajiya Zabba"u da kanta tasa aka Bincikomata Komai akan Sunaira takuma yi Tattaki ita da Hajiya Salame suka je har kaduna gidan su Sunaira atsakar gida suka cima Inna Zarafi ita da Sunaira da Ahmad da Sunaima da aranar ta zo Gida Hutu bata ma kaika samun Cikakken Labarin abunda yake wakana sai gasu Hajiya Zabba'u sun yi tijira sosai Ba wanda ya Tanka musu sai Sunaima ai ita Tana da Zafi kuma bata Daukan Reni Ammh sai Inna ta Tsawarta mata sai bayan Tafiyarsu ne aka Fara maida  mgana har Sunaima taji bakin Zaren ita Sunaira tana ta kuka taji auran ya Fitar mata akanta,Aranar da Sulaiman yazo sai da ya Fahimci abunda ya Faru duk da Malam Abdu Datti ya hana su Fadamai abunda ya Faru Tunda Sunairan ta nuna bata son auran Daga baya,Dalilin da Mgana Takai kunnen maimairtaba ya kuma Tsawarta musu yaci Mutumcinsu ya kuma sa suka Taka sukaje suka suka bama Sunaira da iyayenta Hakuri basu isa suce don me ba Dole suka Tafi sukace domin basu taba ganin bacin ran Maimartaba irin na Lokacin ba Zabba"u ga Fadan Abba Daya abun ya Hade mata,itakuma Salame ga Tashin Hankalin Laila Datayi Rantsuwan in ba Sulaiman bazata auri kowa ba,Ga Takumkumin Sarki Dayace in ya karajin sun aikata wani abu sai sun raina kansu.
Wannan al"amarin shi yasa sukayi Shuru har Akayi Bikin aka gama Lafiya ba wani Tashin Hankali Cikin ya"yan Hajiya Zabba"u ba wacce ke adawa da Auran irin Safiya Tare suke ta Kullawa suna Warwarewa
Bayan auran anan Kaduna Alhaji Aliyu ya siyama Sulaiman gida suka Fara Zama Tunda anan yake Service lokacin da akayi Bikinsu sunaima Tana makarabta sai da tadawo taje ta Daga Dakin kanwarta kuma Har alokacin basu Hadu da sulaiman sau uku ba Duk ganin dayake mata sama sama ne sai dai yasan tana da Muhimmamci wajen Sunaira Koda yaushe Labarinta Antynmu ammh shi yana mata kallon mai Girman kai da Isa bai taba Zama sun yi Hira ba Tsakaninshi Dashi gaisuwa ce Sama sama Dukkansu sun Mu"amalanci juna a hugunace kowa na ganin Dam"uwansa nada Girman kai da son Girma.
Ita Sunaima Tana ganin kamar don yana D'an masu kudi yacika Girman kai kuma Tana ganin ba wasu Shekaru ya bata ba,Sai isa Kaawai ita Bata da sakewa ne ballatana Tana ganin kamar Mijin kanwarta ai kaninta ne,Shiyasa kowa yake ganin Dan"uwansa mai mugun akida.
Sunaira tasha Wahalan da Dangin Sulaiman sosai kafin ta Fara samun kansu da kyakyawan Hallayarta da son Mutanenta da Kirkinta sannan kuma Tazo ta Haifi Wasim Wannan Rabon shi yadan Fara kore wannan Kiyayyar ammh duk da haka duk Sanda Sunaira taje abuja sai dai ta Sauka Shashen Hajiya karama Falmata sai dai Sadiya ta Dauki Wasim akai mata shi shi kam Jininta ne tana Kaunarsa Gabadaya kannesaa suna Girmamata Safiya ce kadai Bata Darajata Ammh Hakurinta da Kirkinta da kuma Maimartaba da Abba Dake Tsaye kan Lamuran sai komai ya Fara sauki ammh har Lokacin Laila Taki kowa sai Sulaiman,Har ahadata dan"uwanta  taki yarda har ikirarin Kashe kanta taso yi shiyasa aka Kyaleta..
Bayan Haihuwar Wasim ne wanda yaci sunan Abba Aliyu Sulaiman ya Samu gurbin Karatu a jami"ar Nottingham,Inda Abba ya Turasa Domin Hado Degree dinsa na Biyu kan kasuwanci,Sunaira tayi kuka sosai alokacin da zai tafi ammh Maimartaba da kansa ya Lallasheta Alokacin ne aka kawo mata magajiya Tana Taimaka mata.
Dayafi tafi sai da ya shekara Daya ya Dawo Ganin gida kuma chan ne suka Hadu da Saifullahi suka zama abokai,shekara uku sukayi suka Dawo Gida Gabadaya da kwalin Karatunsu,alokacin ne kuma Abba ya Gama Gina karamar ma"ikatan A.S.KARGI ENTERPTLRISES,dake Reshen Kaduna ya kuma Bude ma Sulaiman ne Domin ya gwada irin Hazakarsa shi kuma ya jawo Saifullahi suka fara aiki Tare
Ashekaran da suka Rike Kamfanin an samu Cigaba da Riba sosai har kuma ashekara ta Biyu Sulaiman ya Gina wannan Gidan nashi na Malali suka koma Da Zama bayan Haihuwan mai sunan Hajiya Zabba"u Suna Kiranta Wafiyya.
Azuwa Lokacin abubuwan duk sun Zama ayadda ake so Sulaiman ya Samu Rufin asiri sosai har ya Bude Gidan Sarrafa Madara da Fura na S.A.KARGI YOGHURT AND FURA,Akwai wani amintattacen sa Habib Dake kular mai da ma"aikatansa,Sannan Saifullahi yayi aure ammh yar"uwansa ya aura Tana Karaye domin iyayensa basu yarda ya Daukota ba gani suke in ya taho da ita nan kaduna baza su gansa ba yana komawa Gida Duk bayan Sati Biyu.
Bangaran gidansu Sunaira kuwa suna Cikin Rufin asiri domin Sulaiman iyayensa ya Daukesu Tun bayan auransu da Sunaira duka karfin komai ya koma Hannunsa Abba ma da Maimartaba suma ba"a barsu abaya ba suna Kokarin kyautatawa Shiyasa har yau har gobe inna da Malam suna godema Sulaiman basu Haifesa ba ammh Wlh kamar dansu haka suke kallonsa kowa yabonsa yake Hatta kudin makarantar Sunaima na karshe Daya Kakare shi ya Biya mata tayi Jarabawa karshe ta Fita bayan kuma sakamako ya Fito da alfarman Maimartaba Sarkin Kargi Ta samu aiki a Asibitin Barau Dukku Dake Garin na Kaduna.
Sani Direban Sulaiman ne da suka Dade tare yana Tukasa sun saba da juna Sani dan kaduna ne dan anguwan Kabala ne babansa ya Rasu yana Zaune da mahaifiyarsa da Matarsa Sulaiman bai Dauki Sani a direba ba,Domin babu abunda baya yimai na Jin Dadin Rayuwa kamar wani kaninsa ya Daukesa.
Kowa yasan Sulaiman Akwai Dattako irin na Maimartaba ga Sanin ya kamata yana da Girmama na gaba dashi,bashi da saurin Fushi sai dai yana Da Hakuri in Ransa ya baci Ba kyau ammh yakan Dade bai yi bacin Ranba yana da kyalyawan alaqa da Duka Yan"uwansa sanin shi dan gata ne sai gatansa baisa ya Sangarce ba Namiji ne mai amsa sunan Namiji.
Arayuwar auran Sunaira Sunaima bata Taka Gidanta sau Uku ba sai da Wata Lalura in ba Wajen aiki ba sai Gida Tana cikin Daki Inna ta gama Mita ta gaji Sai Ahmed ya Dawo Daga makaranta ya bita Daki yana mata Hira sai ta gaji ta korosa Da Mallan ne kadai suke samun Daidaito ta wani Fanni Saboda yafi kowa karantar ta.
Wasim da Wafiyya tun sunaira na raye suka saba da ita,Domin Tana son yara matuka ballatana ya"yan Sunaira In aka kawo su Gidan ita ke Wahala Dasu Wasiyya nada shekara Uku aduniya Kaddaran Sunaima ya afku Sunaira ta Samu Zamewa abandaki Koda aka kaita aasibiti aka gano Ciki ya shiga wajen mahaifanta,kuma Faduwar datayi ya Tabasa har yana neman ya Gangara ya shiga inda bai kamata ba anyi saurin mata aiki an maida Cikin mahaifa,sai dai kwana ya Kare kwana Biyu da Faruwar haka Ta koma ga Allah.
Mutuwar data sauya kadarori dadama na Rayuwar Sunaima da Sulaimam Domin mutuwar tafi kowa Girgizasu Sulaiman sai da aka Hadamai da Rubutu ya dawo Daidai su Wasim kuma Tun da akayi Rasuwar suna Kargi sai daga baya Maimartaba yasa ka aka Dawo dasu Gidansu Sunaira wajen Sunaima ita take kula dasu ita kuwa Sunaima sai da kyar ta Dawo Daidai ta Cigaba da zuwa aiki..
Ba wanda yasani kuma basu yi Shawara da kowa ba Duk da alokacin Hajiya Zabba"u da Hajiya Salame sun Hango Cikar Burinsu da Auran Laila da Sulaiman wacce har Lokacin Taki aure Tana zaman jiran sulaiman takai Shekaru ashirin 26 aduniya,kawai kwatsan aranar Addu"ar arba"in Din Sunaira akofar Gidan Mallam Datti Abdu da Danginsa Maimartaba Da Rakiyan Yan Fadansa da Yaransa da Abba suka zo kara yimusu gaisuwa akuma Lokacin suka Riko alfarman adaura auran Sunaima da Sulaiman auran da kowa yajisa kamar Daga Sama ba Musu Waliyansu na Zuntu suka basu Sunaima Tare da Hujjan ta Rike ya"yan yar"uwanta.
Kamar yadda Sulaiman yaji abun Daga sama haka Sunaima taji Tayi kuka kamar ranta zai fita Tana Kiran wannan wata irin kaddara ce da Zata Ratso Mijin kanwarta Cikin Rayuwarta wanda takema kallon kaninta karaf akunnen Sulaiman da Saifullahi da Abba da Maimartaba suka Tursasamai ya shiga Cikin gidan ya kara musu Taaziya.
Wannan auran ya bata ran Hajiya Zabba"u Fiye da na Farko ganin wannan karan an bataa mata yasa har Abba da maimartaba suka yi ta Tausanta sai dai bata Saki ba duk acikin Kissanta ne tasa Dole Sunaima Ta tare agidan yar"uwanta bayan auran da wata Daya Kimamin wattani Biyar kenan da Tarewar kuma ta kawo SAmira gidan Domin ta taimakamata Wajen Hanyar Cikar Burinta da Muradinta na Kulla auran Laila da Sulaiman.

*Wannan labarin ba na kudi bane Kyauta ne,ga masoya na wadanda na sani da wadanda bansani ba..Yanzu nake kan Rubutasa nima bani dashi Cikakkensa ga masu tambayanta ko bana kudi bane na Saida musu suyi Hakuri Mijin kanwata kyauta ne ga Masoyana..*


*Shakira*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now