19

789 102 22
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 19*

Daganan Maimartaba ya sallame su,suka koma cikin gida saboda yadda Ransa yake bace ko Hirar da suke bata Lokaci suna yi tsakaninsa da Saraki babu,Shi yace su turomai Zaratan matan nashi Fulani da kilishi Cikin Takaichi da Tir ya kwashe komai ya Fadamusu Fulani sai da tayi kwallah abu Daya yafi mata zafi yadda Salame taci Amanar kaunar dake tsakaninta da yar"uwanta da ake yi ma kallon kamar yan Biyu saboda Shakuwa wanda ko su iyayan su basu san Tsakaninsu ba sun ba ma mijinsu goyan bayan Yin Hukunci bisa gaskiya da aldaci.
Sulaiman bai da lambar Sunaima Saifullahi ya kira sukayi mgana yace da Safe shi ya biya ya Daukota su magajiya kuma zai kira sani akan ya Daukosu Megadi kadai za"a bari saboda gadin gidan..
Ya kira Habib da kansa bayan gaisuwa da sauran bayanai ya fadamai Sakon maimartaba Habib yace tabbas zai zo dukda Sulaiman bai wani jawabi ba ya Tabbatar da koma menene yana da alaqa da abunda ya samu Sulaiman din.
Sunaima batasan su Hajiya basa gidan ba sai da Daddare da tafito ta gaishesu sai magajiya ke fadamata ai suna Kargi Harda sulaiman ta fara Tunanin Ko mganar Laila ne..!Sai da data tambayi magajiya Harda Laila aka tafi Kargin sai tace mata"a"a laila ita kamar gida tatafi tun ajiyan tana jin haka tasan koma menene zaifaru a Kargi ta Tabbata bamai Dadi bane abu Duka na gida ne  gashi Zumunci ne mai karfi Har takoma Dakinta tana addu"an Allah ya sausaauta al"amarin Domin bata son Auran Laila da Sulaiman ya kare tunda ita ba zama Zatayi ba Lokacin Rabuwarsu ya riga yazo gwara ya zauna da yar"uwansa mai sonsa domin tayi iya kokarinta Daga ita har shi sun kasa karban wannan Kaddaran nasu to da su zauna suna Cutar da juna Rabuwar ita tafi Su wasim kuma ko ta sake wani aure ko bata sake ba Tayi alkawarin Zata Rikesu tamkar ya"yanta Har gaban Abada.
Sai da daddare ta samu kiran Saifullahi sanda yake fadamata Sakon Sulaiman mamaki ya kamata da Faduwar gaba tana Tunanin meyasa ake nemanta cikin wannan lamarin sai dai bata da mai bata amsa Domin Saifullahi yana Fadamata Sakon bayan ya Jaddamata ta shirya gobe da wuri zai zo ya Dauketa Allah yasa bata da aiki Ranar sai Monday.
Bata Kira Inna ba sai da Safen take Fadamata Inna tayi Mirmishi cikin son kwantar mata da Hankali Tace"Ki kwantar da Hankalinki Sunaima..Babu abunda zai faru sai Alheri..horona dake shine duk abunda aka Tambayeki kika Fadi gaskiyarki kin ji ko..!
Da wannan mganar na Inna Sunaima taji ta Samu yar natsuwa da Wuri ta Shirya cikin Atamfa Riga da Sikat da Hijabinta sai wajen karfe 9am na Safe Saifullahi yazo Lokacin sani yazo Daukan su magajiya bakinsa har kunne Daga jiya Daya Samu wayar Sulaiman yasan komai ya kare,Domin Har ya fara Tunanin ya nemi wani Aikin da zai rike kansa da iyalansa Tunda Zama ahaka bazai yuyu garesa ba.
Tsakanin Sunaima da Saifullahi gaisawa kadai sukayi daganan suka Dauki Hanyar har suka isa Kargi Mgana bata Hadasu ba tana dai jin Suna waya da sulaiman din yacemai suna Hanya gasunan karisowa.
Da suka iso an fara zaman Fada shi nan Waje ya Tsaya wajen Sulaiman da Tunda yace sun kusa karisowa ya Fito Daga Cikin Fada yana jiransu duk nacinsa nason Hada ido da Sunaima bai samu ba Domin Dauke kanta tayi bayan ta gaishesa sawa yayi aka mata Jagora zuwa shashen Fulani.
Chan ta iske su Hajiya da Safiya da Hajiya karama ashe sun iso suma ba Dadewa Abba na Fada shima har kasa ta Duka ta gaishesu suka amsa mata Cikin Sakewa harda Safiya kasan Cafet din Dake Falon na Fulani ta zauna kanta na kasa kafin kace me hadiman Shashen sun cika gabanta da kayan marmari Fulani nata rawan Jiki da ita sai ga Kilishi itama ta shigo Daman Tsoffin irin Maimartaba ne soaai suke da karamci da Dattako.
Abun mamaki sai ga Hajiya tana Tambayan Sunaima su Wasim kanta na kasa tace"Suna wajen Inna..Dayake yau Ranar sati ne suna da Hadda..!
Kai kawai Hajiya ta gyada batace komai ba Domin Tun Faruwar abunda ya Faru ta daina yawan mgana Safiya ce ta kalleta Tana Fadin"Allah yasa dai yau baki da aiki aka taso ki..?
Sunaima ta Dago tana kallonta Cikin mamaki ammh sai ta Shanye mamakin da cewa"A'a sai Monday nake da aikin Dare..!
Daganan ta maida kanta kasa tana wasa da Gefen Hijabinta aran Safiya tace Mene illar Sunaima da Zuru"arsu..?babu Tsantsam Ladabi da Tarbiya tunda ga Kan marigayiya Sunaira Har ita Sunaimar.
Sunaima bata Dade da zuwa ba sai ga Hajiya Salame da Laila mijin Hajiya Salamen ya tsaya Fada wajen maimartaba.
Suna shigowa Kallo Daya Hajiya Zabba"u tayi ma Salame tatashi ta Shige Ciki batama kaunar Hada Zama da ita Laila kuwa goshi ya Suntuma da Plasta Sai wani kame kamen kai take yi Fulani tayi uwar iska dasu gwarama Kilishi ta Tarbesu Ballatana Safiya data Saki Tsaki tatashi tabi Hajiya,Hajiya karama ce kadai ta Tsaya suka gaisa Hajiya Salame sai ta Raina kanta Duk da ta gama Tsara yadda Zata wanke kanta ta kuma Tsarama Laila abunda zatace din Saboda ta Fitar da kanta.
Suna nan zaune su sulaiman suka shigo gaida su Fulani Harda Mijin Hajiya Salame duk da ta mai jawabin karya ne na wai Lailar batama Sulaiman komai ba ya kama Dukanta Har sai da ya fasa mata goshi kuma ya Korota gida bai yarda da ita ba,yasan Halinta shiyasa yazo Domin yaji Gaskiya sai da yasha Jinin Jikinsa da akacemai Hajiya Zabba"u na Ciki ammh Bata fito ba Alhalin ya sani ko ba Domin Salame ba ai yaya yake gareta kuma suna da kyakyawan Fahimta Tsakaninsu yana Tunanin koma meya faru to Ya taba wannan Zumuncin shiyasa shi tun farko bai Matsama kansa sai anyi wannan auran ba yaso ta samu wani ta aura Salame ta Dake kan hakan.
Karfe goma da yan Mintina Maimartaba ya bar Fada da Uzurin wani abu ya taso daga cikin gida yabar Wazirin ya cigaba da Zaman Fada da kuma karban koken takalawa.
Ababban Falon maimartaba na cikin Gida inda yakan Huta Daddare kafin ya shiga anan aka Taru gabadaya Harda Habib Daya iso ba Jimawa.
Sunaima tana chan karshe kusa da Safiya Hajiya tana tare da Hajiya karama da Sulaiman Dake gefen Maimartaba shi da Abba dasu Saifullahi da Mijin Inna Salame wacce ke Zaune gefe ita da yarta Inda tasan kunya data kamata sai dai Ina sai ma Kokarin nuna komai ma bai Faru ba Daga kwayar idanuwanta.
Fulani da Kilishi na Chan Daga gefen Daman maimartaba Sulaiman Maimartaba dake kan kujeransa Cikin Rawaninsa yace ya Bude Taron da addua ba bata Lokaci yayi addu"a suka Shafa Takawa ya Dade Shuru ta Cikin rawaninsa yake karema Kowa kallo cikin Farin rawanin Daya Rufe Har Bakinsa zuwa Karan Hancinsa.
Sai da yayi gyaran Murya kana ya Kalli Sulaiman Lokaci Daya yana Fadin"Saraki kai zaka Fadamana abunda kukazomin dashi jiya ko kuwa Ita Zabban"u zata fara mana Bayani..!?
Kan Sulaiman na kasa yace"Hajiya zatayi bayanin komai Ranka ya Dade..!
Ba musu ya maida kallonsa kanta yana Fadin"Muna Sauraranki Zabba"u ki Maimaita mana bayaninki da kika zo kikamin Jiya da yammah..
Hajiya ta gyara zama ta maimaita abunda ta Fadamai Jiya da komai da komai bayan ta gama maimartaba yace Safiya tayi mgana itama ta Fadi Abunda ta sani da duk Abunda ya Faru Jiya da abunda laila ta Fada da Rashin Mutumcin Datayi ma Hajiya Data gama ba Maimartaba yace Saraki ya Fadi gaskiya Kansa na kasa yace"Hakane Ranka ya Dade..Duk da Wasu abubuwan ina ganinsu kamar mafarki sai dai da gasken sun Faru Duba da mganganun mutanen Dake Tare dani..!
Mijin Hajiya Salame ne gabadaya kunya ta kamasa da wani Takaichi kansa na kasa ya kasa ma Dagowa,Salame data ga kowa sai Jifanta da wani kallo yake harda Abba sai ta karkace ta fara kuka tana Fadin"Ranka ya Dade wl..!
Hannu maimartaba ya Daga mata Cikin Bacin rai yana Fadin"In kika kara sakamin baki Salamatu ban baki Izini ba zan ci mutumcinki..!
Yafada Cikin Kaushin Muryar da Dole ta sanda kai tana bada Hakuri Maimartaba Abba ya kallah kafin yace""Zabba"u tace kasan komai Daga bakin Abokin Saraki meyasa baka Fadamin Tunda fari ba..?
Abba ya gyara zama ya shiga bayanin Duk sanda suka Daina Jin Sulaiman a waya da Halin da Hajiya ta shiga da Binciken da yayi da abunda aka Fadamai sannan daga karshe ya Fadi zuwan Habib wajensa da kuma Ciwon Hajiya dayasa bai zo ya sanar dashi ba Maimartaba ya gyada,kai kafin yace Habib yayi jawabi shima ya gyara Zama ya Fede duka abunda ya Faru Tsakaninsa da Laila Daga karshe yace"Ranka ya Dade in akwai Bukata zan kunna Sautin dana nada na ita Amaryan Sulaiman din sannan akwai Shedun ma"aikatan gidan tunda Duk agabansu akayi..!
Maimartaba yace"In da Bukatar hakan za"ayi..!
Wajen Saifullahi ya juya yana fadin
"Kai aboki ne ga Saraki zaka iya mana bayanin Abunda ka sani kan wannan lamarin sannan Dalilinka na Boye ma Ahalinsa Halin dayake Ciki..!?
Saifullahi shima ya gyarama zama Lokaci Daya yana Fadin"Wato Ranka ya Dade ni bansan Abunda ke Faruwa ba nadai kira wayar Sulaiman ana Kwana Biyu da auransa Saboda akwai Tattaunarmu da wani kamfani da shi da kansa Sulaiman din ya sanya Lokacin saboda nasan baya Saba mganarsa da bai zo aiki ba Ranar sai na Kirasa nan ya fadi yadda suka kare da Laila da yadda yayi ta Zaryan Gidan baya ganin Sulaiman da Kiran da yayi ma Sani da jawabin Daya Fadamai Daga karshe yace"Ranka ya Dade SUNAIMA ita naje nema sai ban sameta ba tana wajen aiki Shine bayan taji sakona tazo Ma"aikata ta Sameni ita ta fara Fadamin Sihiri akayi ma Sulaiman sannan ta Rokeni kada na bari wani Daga cikin Ahalin Sulaiman ya sani.!
Daganan ya cigaba da fada musu Kokarin da Sunaima tayi ta Dalilin Uwa mabada Mama inna Inda taje Chan Zuntu ta Samu kawunta yana karya Sihiri tamai bayanin komai da mganin Dayabama Sulaiman da yadda Sunaima take kokarin ganin Sulaiman ya Dawo Cikin Hayyacinsa Har satan zuwansa Dakinta sai da ya Fada bai boye ba da komawar su Wasim Hannun Inna Dalilin Yadda Laila batama barin Sulaiman ya Tuna Dasu!
Mamaki da Al"ajabi ya kama kowa Hajiya sai kallon Sunaima take take Nadama ya kamata Allah Sarki ashe ita ta Rika Fadi tashi ta Hana afadamusu Saboda kada Hankalinsu ya tashi,Hakama Abba Tuni girma da Kimarta suka karu Wajen su Fulani dasu Hajiya karama Sulaiman kuwa jinsa yayi wani iri kansa yayi girma Duk da yasan wasu abubuwan ammh bai san haka Sunaima tayi wahala Dashi ba,Baisan ta ina abun ya Fara ba sai dai yaji kamar an Bude zuciyarsa ana kwararamai Kima da Soyayyar Sunaima da Duka Ahalinta
Yana ta kallonta sai dai ita kanta na kasa Tunda ta gaida Maimartaba bayan Shigowarta bata kara yarda ta Dago kanta ba
Hajiya Salame kuwa Cikinta ya gama Duran ruwa ai bata da wata Tsumi ballatana Dubara Laila ta gama bata komai kuma.
Maimartaba Sunaima ya kalla yana Fadin"Kinji Abunda Abokin Mijinki ya fada Shin hakane..?
Kanta na kasa ta gyada kai kafin itama ta fara mgana cikin Sanyinta na Koda yaushe ta sanar dasu Yadda sukayi da Inna sai dai ta Boye yadda akayi ta yarda Bayan inna ta Fadamata Sihiri ne ajikin Sulaimam da Duka yadda Sukayi da Laila Lokacin Dataje yima Sulaiman mgana kan su wasim da komai da komai bata Boye ba Zuwa mganin da Inna ta karbo Wajen kawu Jafaru.
Falon gabadaya yayi Shuru bakajin komai sai kukan Hajiya Salame maimartaba ya Dade yana kallonta kafin yayi gyaran Murya yana Fadin"Salamatu kin ji Duka Zargi da bayanan daya Tabbata kan abunda kika aikata kan Dan yar"uwanki kika kuma Dora yarki akai shin Hakane ko ba Haka bane..?
Sai ta kara karfin kukanta Tana Fadin"Ranka ya Dade wlh ni duk bansan anyi haka ba Ina jos Laila na Kaduna ni kaina bana samunta awaya ai na fadama Zabba'u..In zaku lura ba Komai bane sai yarinta Dake Damun Laila ammh nidai nasan ban kai Sulaiman an mallake ma Laila shi ba Ranka ya Dade..!
Ta karishe Fada tana Sharan Majina da jan Hanci kowa baki sake ya kalleta Maimartaba yace"Abunda ita Lailan ta fada kin sakata aikatawa fa..?Shima karya ne..!?
Da Sauri tace"Allah ya taimakeka Tayaya bazata Fadi komai don ta kare kanta ba Zabba"u bata Duba itama Laila yarta bace in tayi mata wani abu ai itama me sakata Daki ne ta daketa ammh sai ta Dauki yarta suje su kama karamar yarinya kamar Laila da Duka Ranka ya Dade?Kaima kasan Zabba"u akan Yayanta Tun Sunaira nada rai Saboda ma Tana da Hakuri ne ita kanta Sunaimar inzata Fadi gaskiya ai bata taba mata kallon Arziki ba Ita Laila yarinta da Zafin Tozarci yasa ta Fadi haka Cikin Rashin Hayyaci ko ba Haka ba Laila kalli goshinta Ranka ya Dade ko da tazo Gida bata gani Jini duk ya wanke mata Fuska ba Tsausayi Zabba"u tasaka Saraki ya koreta in ma Haka take ji ai Tsakanina da ita ya wuce wasa sai ta Kirani muyi mgana mu Sami mafitar da basai ma mganata tazo kunnan ka ba Ranka ya Dade..!
Lalle Hajiya Salame ta iya Tsara Zencen ba wanda ya yarda da ita kai Tsaye Maimartaba ya bada Izimin shigo dasu magajiya Daya bayan Daya sukayi ta bayani Tiryan Tiryan ai sai bakin Salame ya mutu kuma Sarki ya Umarci Habib ya kunna muryan Laila Daya Nada Ai sai Salame taji kamar Zata Nutse zufa na keto mata ta manta Fadar Hukunci maimartaba ne ko"ina Sheda yake sai ya saka an zomai dashi kafin ya yanke Hukunci.
Laila ita ta karshe da Maimartaba ya jefama Tambayar"Shin zaki Fadamana Dalilinki na aikata abubuwan da duka Shaidu suka Tabbatar kin aikata..?miye gaskiya abunda kika fada kan Salamatu..?
Laila bata da wani Zabi Daman jin Mommy kawai take yi ita fa tayi Nadama Kuma tayi alkawarin Fadan gaskiya ta amsa mata ne da Zata Fadi yadda tace ba wai don zata Fada ba din.
Kanta na kasa cikin kuka tace"Duk Abunda suka Fada gaskiya ne..Sannan gaskiya ne Mommy ta karbo min mganin mallaka ita da kawarta Anty Zaliha nima bansani ba sai aranar da za"a tafi dani Daganan..nan ta Shiga Zayyanemusu komai da komai da yadda tayi amfani da mganin ya Fara aiki da Duka abunda ta sani..!
Gabadaya aka Dauki Salati da Salallami Ita kuwa Salame tunda Laila ta Fara mgana Jikinta ke rawa ta gama Sanin yau kwananta yagama karewa.
Mijinta ya kalleta yace"Tir Dake Salamatu kin bani kunya..Yata ba Halinta bane ke kika sata aikata koma me yafaru..Don Allah Zabba"u da Saraki da kai Aliyu amadadin Laila ina Neman gafarku..!
Maimartaba nan take ya kallesa yana Fadin"Ka saketa Saki Biyu Isa..!
Gabadaya sai kowa yaji Dam gabansa ya Fadi Salame ta Daga hannu ta Dora akai zata tsandara Ihu Maimartaba ya Daka mata Tsawa yana Fadin"In kika ce tak..Wlh sai kin Shekara agidan yari Mutuniyar banza kawai..!
Sai ta Rufe bakinta da Hannunta tana Hawaye Ya sake kallonsa yace"Sauta saki Biyu nace..!
Ba musu ya kalleta yana Fadin"Ni Isa na Saki matata Salamatu Saki Biyu..!
Hajiya Tana girgiza kai tana kuka Laila ma haka Maimartaba Sulaiman ya kalla kafin yace"Saraki itama Lailar ka Sauta ta Saki Daya wannan Umarnina ne..!
Bai yi musu ba Daman Abunda yake jira kenan ya kalleta yace"Ni Sulaiman Aliyu na saki matata Laila Saki Daya..!
Ai sai Salame taji Numfashinta na sama da kasa Maimartaba yace"Madallah zaku basu dukkansu arubuce..Kai Isa ka Dauki Yarka ka tafi da ita kai keda Alhalin yimata Kowani Hukunci Salamatu kuma Hukuncinta shine Zaman Shekara Daya ashashin Bayi da aikin Wahala da Dukkan Hadimai keyi Sakamakon Yin Zamba cikin Aminci da kuma aikata Shirka ga d'an yar"uwata akiramin Danatu Shugabar Shashen Bayi tazo ta Daukemin ita agabana..!
Salame ta Fara rarrafawa gaban Sarki Tana kuka da majina da rawan Murya Fulani ta Dakatar da ita da Tsawa tana Fadin"Ki Tsaya Daganan..Komai ya Faru ke kikaja ma kanki..Wnnan Hukunci yayi Daidai..!
Daidai Lokacin da Sarkin kofa ya Bude ma Dinatu wata katuwar mata ta Shigo tayi gaisuwa ga Sarki Salame ya Nuna mata yana Fadin"Ki kaita Shashen bayi..Arika bata ayyukan Daidai da aikin kowani bawa..Zata Zauna daku na tsawon Shekara Daya kada na ganta ashashen masu Gidan..!
Daga haka ya kauda kai Dinatu najin haka tasan Laifi Salamatu tayi mai Tsananin da aka yanke mata wannan Hukunci Haka Maimartaba yake da Bare dana gida in kayi Laifi sai ya Hukuntaka.
Riko Hannun Salame dake kuka Tayi Lokacin Fulani tace"Dinatu kada ku Ragamata Domin tana Diyar Sarki..Kada ki manta Hukunci yana Hawa kan kowa da kowa..!
Kai ta gyada tana Fadin"Angama Ranki ya Dade..!
Haka aka tasa Salame tana kuka Laila na kuka wacce tatashi Babanta ya Daka mata Tsawa Dole ta koma ta Zauna har aka Fice da ita.
Alhaji isa ya Duka yayi ma Sarki Godiya da Sallama ya tasa Laila suka Fice Daganan maimarta ba ya kalli zabba"u yana Fadin"Ina Fatan yanzu kin gane Dalilin Dayasa Allah ya Nuna Miki abunda kika aikata abaya da wanda,kika aikata yanzu  kin yi ma Allah Shishigi ne..?
Hajiya na Hawaye tace"Ranka ya Dade nayi nadama sosai na Fahimci Abunda kaso wani Lokacin ba Alheri bane..Ina So ku tayani Rokon Gafaran Sunaima kuma ku yafemin Don Allah Musamman Sulaiman da Abbansu..!
Tafada Cikin kuka Maimartaba yace"Alhamdulillah..Naji Dadin jin haka..ki Roketa ai Surukarki ce..Ni kuma Daman godiya zan mata Sunaima mun gode kwarai Tun Lokacin da Sulaiman ya kawomin mganar auran yar"uwanki Haduwata da Mahaifinku nasan kun gaji Ddattako ga Tarbiya Allah yayi muku albarka Dake da abokan Saraki kun cika abokai nagari..!
Gabadaya aka amsa da Ameen Hajiya ta Juya tana kuka tana Rokon Sunaima Gafara wacce ta rike hannunta tana Fadin"Bakomai Hajiya..Wlh banta rike ki araina ba..!
Safiya ma ta Roketa duka tace bakomai ta yafe musu Maimartaba yace"Na saka Isa ya saki Salame ne saboda tagane Kuskuranta...Itama kuma Laila na Haramta aure Tsakanunta da Saraki Taje in Tayi hankali Sai Allah ya bata wani mijin..!
Kowa ya gyada kai Hatta Abba ya gamsu sosai.
Maimartaba yayi Nasiha sosai Daga karshe ya sallami kowa sai dai kafin Atsahin Sunaima tadaga hannu Tace Tana son tayi mgana da Maimartaba.
Maimartaba ya kalleta yace"Ni kadai kike son mgana dani..?
Kanta na kasa tace"Da kowa da kowa Ranka ya Dade..!
Sulaiman ya fi shiga Rudu sosai yana Tunanun kuma me yafaru Kowa ya koma ya Zauna sannan aka natsu ana Sauraranta kanta na kasa tace"Ranka ya Dade ina so ka saka SULAIMAN ya sakeni...!
Dam.!gaban Sulaiman kowa da mamaki ya Dago yana kallonta Shima haka yake kallonta Maimartaba ya kalleta kafin yace"Meyasa kika neman Saki Sunaima..?
Kanta na kasa tace"saboda Dalilai Dadama Ranka ya Dade..Tundaga Lokacin da na maye gurbin yar"uwata Abubuwa basu koma Daidai ba Sulaiman bai karbeni a mtsayin kaddaransa ba nima na kasa karbansa Ranka ya Dade Shiyasa naga da mu zauna muna Cutar da kanmu ga Zunuban kasa sauke Hakkokin juna Naga dacewar Rabuwar tafi Ranka ya Dade..Indai su Wasim ne na Yarda Zan Rokesu mudim rai in na samu wanda ya Dace dani na aura ina Fatan mganata bazai saka Sarki yaki Fahimtata ba..!
Kowa awajen kallonta yake cikin mamaki banda Sulaiman dayake Hasko wasu abubuwa Maimartaba ya Dade yana Nazari kafin yace"Naji Duka bayananki kuma na Fahimta..Saraki kaji abunda matarka tace zaka iya Sakinta abisa Dalilanta.?.!
Kai Tsaye kuma yana kallonta yace"A"a Ranka yadade...Bazan iya Sakinta ba..Naji Duka Hujjojinta sai dai ina so ta sani kowa ya sani NI bazan saketa ba har Abada Saboda INA SONTA..!
Da sauri Sunaima ta Dago tana kallonsa Shikuma sai ya Daga mata Gira kuma har Hajiya ta gani kowa yayi Fuska yana yar Dariya.
Maimartaba yace"To ke kin ji Abunda mijinki yace yana sonki bazai iya Sakinki ba..!?
Kan sunaima na kasa ta kasa mgana Gabadaya kalaman Sulaiman sun kashe mata jiki.
Maimartaba yayi mirmishi yace"Sunaima kin yarda ni Uba nake gareki..?
Da Sauri ta Daga kanta Cikin Dattakonsa yace"To bari na yanke ma Surukina Hukunci a mtsayina na Uba gareki..Saraki kana son matarka kuma ita da alamun Hallayarka ta baya yasa bata sonka..Zan baka Wata Biyu kachal kaje ka Daidaita da matarka naji Labari mai Dadi In har alokacin Yata tana nan akan bakanta To nayi miki alkawarin da kaina Zan saka Saaraki ya Sautaki Domin karya yake baya sonki..In kuma yana Sonki lokacin dana Dibarmai ya isa ya Tabbatar da hakan yayi hakan..?
Kanta na kasa tace"Eh yayi..Allah ya kara Nisan kwana Ranka ya Dade..!
Maimartaba ya jinjija kai yana Fadin"Saraki kaji dai Sharadina ko..?
Yafada cikin Zolaya da Sauri yace"Maimartaba kada ka damu..Zakaji Labari mai Dadi..!
Cikin Fara"a yace"Allah yasa..!
Daganan ya sallamesu shi kuma ya koma Fada Sulaiman da su Habib Suma wajen Masauratar suka Fita yayinda Sunaima dasu Hajiya suka Shiga Cikin gida.




*Janafty*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now