12

636 88 14
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

_AFUWAN..!AFUWAN..!AFUWAN..!_

*Page 12*

Dalla Dallah cikin Natsuwar da Inna ta taimaka Sunaima ta samu ta shiga Zayyanemata duk abunda ya Faru Tundaga washegarin Zuwan Laila Gidan da abunda ya faru jiya da Daddare da mafarkin datayi Sunaima ta kalli Inna Idanuwanta sun cika da kwallah Tace"Inna Sunaira ta nagani acikin Mafarkina sai taki yarda tamin mgana ballatana ta Tsaya ta Saurareni Abu Daya take Fadamin Sulaiman Shine KADDARA TA kuma Duniyata ne ni kadai ce zan iya Fiddosa Daga Halin Daya ke ciki...Sannan ta Fadamin daman chan aro ta Rikemin yanzu Kaddaran tawa tadawo hannuna Gabadaya kaina ya Kulle Inna na rasa madafa da Tunanin wannan Wani irin mafarki ne Shiyasa nace bari nazo na sameki na Fadamiki yanzu nan Daga kai Wasin makaranta nake na Zarto nan..!
Ta karishe Fada Hawayen idonta na Gangarowa saman Fuskarta Inna da tagama Jinta da kunnen Basira ta Sauke Tagwayen Numfashi kafin tace"Inna Lillahi Wa"inna Ilaihirraju"un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma ka iya mana abunda muka gaza ka kuma Taimakemu adukan Lamuran mu Ina Fatan wannann mganar ni kadai kika Fadama ko Sunaima?
Inna ta fada tana kallonta Sunaima ta Gyada kai tana Share kwallarta kafin tace"Kema Inna Kinsan bani da wata kawa da zan iya wata mgana da ita..Sunaira ce kuma bata agidan Duniya sai ke Inna..!
Inna ta jinjina kai kafin tace"Kinsan Abunda ke Faruwa da Rayuwar Sulaiman..!?
Sunaima ta girgirza kai kafin Inna Tace"Ai kinsan Sihiri ko..!to shi aka yi mai kuma shi ke Dawaniya dashi..!
Sunaima ta saki baki Tana kallon Inna Kafin ta maimaita Cikin mamaki"Sihiri kuma Inna..?
Inna Tace"Tabbas..Kuma na Mallaka ne Sunaima..Laila bata shigo Rayuwar Sulaiman ba sai da tayi babban shiri akansa..Shi wannan Sihirin na mallaka da Namiji zai zama kamar bawan mace ne komai tace awajensa Shine Daidai yana mantawa da komai nashi indai tana gabansa bar batun Ya"ya ko mata ko iyaye harta karan Kansa ma yana mantawa dashi..Sannan Sihirin yana Sarrafa mallaka Hatta abunda Mutum ya mallaka yake Tare dashi kamar shi Sulaiman zata Mulki Ma"aikatan Gidan da kowa Dake karkashin sa Ciki Hardake Sunaima..!
Sunaima ta Zaro ido kafin tace"Hardani fa kikace inna..?
Inna Tace"Eh Hardake..Sai dai a bayananki na tabbata da Kin Tsallake wannan Sharrin Allah ya kareki abun bai yi Taziri akanki ba..kuma Gaskiya ne kece kadai Mabudin Rayuwar Sulaiman ayanzu..Ni bana Fassaran mafarki kuma bana Duba sai dai ayyada kika Fadamin wannan mafarkin Raina da Jiki na ya bani Yar"uwanki tazo miki cikin Mafarki ne Domin tasakaki ki Farka Daga Barcin Daya kwasheki Tana Fushi Dake Saboda har yanzu baki karbi Kaddaranki ba Sunaima tana so ne ki Mike Tsaye ki nuna ma Duniya Mijin kanwarki yanzu Shine Kaddaranki Domin Dake Dashi ku Rabauta Har gobe Kiyama..!
Ta karishe Fada Lokaci Daya tana kara Nazarin Sunaima wacce tayi kasake Tana kallon Inna kafin Tace"Ya akayi duk kikasan wadanan Inna..?daman kinsan Sihiri haka..?
Inna tayi Mirmishi kafin tace"Kinsan Kawuna Jafaru na Zuntu..?
Sunaima tace"Sosai ma Inna kawu Jafaru dai naki..!
Inna tace"Yauwa to shi..Ai Sana"arsa  kenan karya Sihiri Shima da ayoyin Allah sannan yana da Lakanin Shima wani abokinsa Bafullatani da sukayi zama tare a Lagos ya bashi awajensa duk nasan Sihiri da in aka Fadesa nake iya gane Wani iri ne..!
Sunaima ta Jinjina kai kafin tace"to yanzu ina Mafita Inna..?ko Hajiyarsu zamu fadamawa tazo taga Halin da ake Ciki..!?
Inna ta Dakatar da ita da Sauri tana Fadin"Kul kamar ki Fara..Wannan ba Fadan ki bane..ai Diyar tasu ce Saboda haka ki zura ido ki koma Gefe Fadan nan na Hajiya Zabba"u ne na Tabbata yadda take son D'an nan nata da kuma yadda take a Tsayen nan ko Yar"uwartace Uwa Daya Uba Daya bazata yadda yarta ta asircemata Da ba..Muna nan Dake in komai ya Kwabe zaki ji kansu..Kada ma ki Fara Ahali ne Daya ne su din ke kuma ai barece acikinsu Saboda haka wannan Fadan ba naki bane kada ki kuskura ki Saka bakinki..!
Sunaima tace"Inna to mganar yaranan fa?ina Tsausayinsu gashi wannan Satin mai shiga zan Fara aikin Daree fa hannun wa zan barsu?in abaya ga Magajiya yanzu ita kanta bata da Damar hakan..!?
Inna tace"Kada ki damu Babu abunda Zai gagara..Yanzu mafita Dayace Sunaima kuma Tana Hannunki ne..!
Sunaima ta kalli Inna Cikin Rashim Fahimta kafin tace"Yana Hannuna kuma Inna..?
Inna Ta gyara zama tana Fadin"Eh haka nace kuma haka nake nufi..Mafitan da gyaran komai yana Hannunki ne..!
Sunaima ta kasa mgana Ganin Haka yasa Inna ta Cigaba da Fadin"Kinsan meyasa nace haka..?
Bata bata Zarafin mgana ba ta Cigaba da Fadin"Saboda kece Duniyar Sulaiman ayanzu..Ki kauda mganar Mahaifiyarsa bata son auranku ke baki Fahimci Kaddaranki Auran Sulaiman Tundaga Launin MAhfuz bane..?abaya kin Taba Tunanin Sunaira Zata rasu har watarana ki Auri Mijinta..?
Sunaima ta Girgiza kai kafin Inna ta Cigaba da Fadin"To kamar haka nake so ki Auna hakan aranki. sai ki natsu ki Fahimci Shin Tsarin mune ko kuma Tsarin Allah ne..!
Sunaima ta Bude baki Zatayi mgana Inna ta Dakatar da ita da Cewa"A"a ba yanzu zaki bani amsa ba..So nake kije Gida ki Kulle kanki adaki Sunaima ki Fara Nazarin Rayuwarki Tundaga matakin Yarinta Har zuwa yau ki gani Duka Tsarim Waye..?meyasa tun abaya baki yi aure ba Har kanwarki ta Rigaki..?in har kika yarda kika kuma Gano Duka Tsarin Allah ne kuma Kaddaransa ne kece zaki ci gajiyan Auran Sulaiman in har kin yarda kin Amince Shi din kaddaran ki ne kuma da Allah ya Tsara kin Shirya zaman Gidan Mijinki ki Kwaci auranki Domin Samun Aljannah ki Dawo ki Sameni ki Fadamin Inna na yarda na Kuma Amince komai Tsarin Allah ne Sannan zan Rumgumi Mijin kanwata a mtsayin kaddarata ni kuma nayi Miki alkawarin bazAmu kauce Hanya ba kamar yadda wanchan ta Kauce ba da Izinin Lahi Indai jinin Zazzagawa na yawo acikin Jinina kuma yana yawao acikin Jikinki wlh lokaci kadan ne Sai Labarin nan sai Mu Tuna Sunaima komai zai zama Tarihi..!
Inna ta karishe tana kafe Sunaima da Ido tana kara Fahintar yadda ta ke Saurarenta da yadda mganganunta suka Samu Muhalli a wajenta ta gamsu Domin taga Tsoro da wani Sadaukarwa a idanuwan Sunaiman.
Ganin Haka yasa Inna ta kara gyara Zama Tana Fadin"Kada ki Damu kije kiyi Nazari a tsanake..!
Sunaima ta Runtse ido kafin ta Bude ta kalli Inna tana Fadin"Inna in na yarda da duka mganganunki Tayaya Zamu Fitar da Abban su wasim..Sihiri fa kikace Inna..!?
Inna Tace"Wannan ba mtsala bane..Nasanki baki wasa da addu"a da Karatun Qur"ani shima sun samu sa"anshi ne da kuma Kila yana Da Rauni Wajen azkar da Karatun Qur"ani kema ina kyautata Zaton Shi ya kwaceki Allah zamu gayama Sunaina sannan in kika amince Kece ai zaki Gudanar da komai kamar yadda na Fadamiki Tun Farko..!
Sunaima tayi Shuru ta kasa mgana Tagumi kawai ta Zabga wani Abu na Tsirgamata acikin Jinin Jikinta Gabadaya Tana cikin Tashin Hankalin Halin da Sulaiman yake ciki bata da natsuwa Mutun kamarsa ya Dawo haka akwai Tsausayi sannan Taya zata Fara zaman aure da Mijin kanwarta wanda suka Gudanar da Rayuwar aure harda ya"ya a tsakaninsu..?,gaskiya da kunya da Nauyi bama haka ba Tana ganin In Sunaira ta Chanchanta ai ita bata Chanchanta ba Shekarata Talatin aduniya Sulaiman kamar kaninta Take kallonsa Tataya zata Fara zaman aure na Hakika dashi..?
Wannan Nazarin sune suka Hanata ma kara mgana Inna bata matsa mata ba ta Fice ta barta ta koma Tsakar Gida taciga da Shara acikin Ranta Tana addu"an Allah yasa Sanadin haka Komai ya zama sai Labari Tsakanin Sunaima da Sulaiman.
Sunaima bata san Tsawon Lokacin Data kwashe Tana Tunani ba Har barci ya kwasheta bata sani ba sai Farkawa Tayi ta Duba agogon Wayarta Taga 12na rana ta Kusa ta makara a  afirgice ta mike Karfe Daya da Rabi Zata isa Wajen aiki Fitowa tayi a Hanzarce Hijabinta da jaka a Hannu a Madafi ta Samu Inna tana Dafa wake Har ta gama Sharan tayi wanki ta zo ta gyara wake tana Dafawa

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now