6

698 78 6
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 6*

Har suka iso gidan ba wanda ya kara mgana acikinsu sai dai Wasim ne da Wafiyya ke ta garancinsu,Sulaiman ya kasa koda kwakwaran Motsi gabadaya Baya cikin Natsuwarsa.
Saifullahi ya gyara parking a Haraban Gidan,Sulaiman ya kallesa yana Fadin"Zaka wuce ne..!?
Kai ya girgizamai kafin yace"Zan shiga na gaida su Hajiya..!
Daga haka ba wanda ya kara mgana gabadayansu suka Fito Daga Motar sulaiman yana Rike da Wafiyya ajikinsa da Jakar makarantar ta da Luch Box dinta yayinda Saifullahi ya Riko Hannun Wasim shima da Tarkacensa megadi ne ya sheko yana musu barka da zuwa Saifullahi ne kadai ya Kallesa ya amsa mai,Sulaiman gaba yayi bai ma Tsaya bi ta kansa ba.
Suna shiga Falon gidan suka ci karo da su Hajiya Zaune su Samira na gabansu kamar  masu neman gafara Hajiya waya take yi Shiyasa suka Zube suka Fara gaisawa da Hajiya Karama ta amsa Cikin Fara"a tana Mikama Wasim hannu Tana fadin"Sabon Megidana idon ka kenan..?
Bakinsa ya wangale yana Fadin"Hajiya...!
Dariya tayi tana Fadin"Kaji shi baki Zau ba Cefane..!
Tafada Lokaci Daya tana Daukansa bayan ya iso gabanta,Wafiyya na Jikin Sulaiman tana kwaikwayon sunan da Wasim ya Kira"Ahjiya..!
Hajiya karama tace"Ah lalle Wafiyya manya kema bakin ya Bude..?zo nan Allah yasa kin Daina kiyuwa..!
Miko mata ita Sulaiman yayi ta Noke taki zuwa ganin tana neman kuka yasa Hajiya karama tace"Kyaleta..Ni megadina ya isheni..Bazan gayyato Rigimammiya ba..!
Yake sukayi gabadayansu Sulaiman dai kansa na kasa ganin Hajiya ta gama wayar ta juyo Tana kallonsu
Sai Sulaiman yasha Jinin Jikinsa,kansa na kasa yace"Hajiya sannun ku da zuwa..!
Cikin Nazarinsa ta amsa mai Lokaci Daya Tana kallon Saifullahi Dake gaishesata ta amsa mai Cikin Sakin Fuska kafin tace"Saifullahi ya wajen Su Hajiyar taka..?ina Fatan Tana Lafiya..!?
Kansa na kasa yace"Lafiya lau Hajiya..!
Zama ta gyara Tana Fadin"Har wajen itama iyalan naka..!?
Kansa na kasa yace"Duk suna nan Lafiya Hajiya..!
Kai ta gyada kafin yace"Masha Allahu ka gaishesu ai zan samu Lokaci naje nu gaisa Rabona da Ita tun Tarewar Saraki da tsohuwar yarinyar nan..Kai kam Saifullahi kayi Tunani mai kyau ka auri yar"uwanka asirinka yana Rufe bamai jin Sirrin Gidanka..!
Tafada Tana bayyana Bacin Ranta Tsakaninsu ba wanda ya iya cewa komai itama bata kara ba illah Alamun Tafiya da tayima su Magajiya suka Mike zasu Fice daga Falon Samira ta Rankwafa Tana Fadin"Ranka ya dade wani barayi zamu sauki Su hajiya..!?
Kafin yayi mgana Hajiya ta kalleta Cikin Ikonta tace"Ki gyara mana Dakunan Sama Samira..!
Kai ta gyada kafin ta Ramkwafa tabi bayan Magajiya.
Bata kara kallonsu ba illah barayin Hajiya karama data kallah Tana Fadin"Kice ke kina Mijin dashi..?
Hajiya karama Tace"Ina Laifi..!
Hajiya ta tabe baki tana Shafa Kumatun Wasim tace"Ai gwaramin Tsohon Mijina mai Cefane ba wannan Yaron da baisan kowa ba sai Ubansa..!
Tafada tana Shafa kansa Ganin haka yasa itama ya Fara washe baki yana Kiran ta Hajiya kamar yadda ya iya baro Jikin Hajiya Karama yayi ya Dawo nata yana Kiran sunanta Cikin Dariya tace"Ah lalle nima yana Matar dani.!
Dariya suka saka ita da Hajiya karama,Kafin ta kalli Wafiyya Dake Jikin Babanta Tana ta Fama da Bicuit din da Ahmad ya siya musu hannu ta mika mata alamun tazo taki zuwa ta makale Cikin Babanta Dan saukota yayi yana fadin"Hajiyata jike wajen Takwaranki mana..Jeki.!
Yafada yana Tura mata ita ai sai ta saka Kuka da Sauri Hajiya Tace"Dauki y'arka..Yarinyar nan ta cika Rigiman banza..!
Sake Daukanta yayi ya rike yana Lallashinta sannan tayi Shuru Hajiya ta kallesu yadda suke Durkushe gabansu kamar masu neman gafara,kafin tadan Murmusa Tana Fadin"Saifullahi ina Fatan dai kana Lekawa gida lokaci bayan Lokaci ko..!?
Dagowa yayi kafin yace"Eh Hajiya Duk bayan Sati biyu zuwa uku nake Tafiya gidan..!
Kai ta kada kafin tace"Dakyau..Allah yayi albarka..!
Suka amsa da Ameen atare Sulaiman ta kallah Cikin dan Lokaci kafin tace"Saraki ina Matarka..?munfi Awa Daya agidan nan ban ganta ba..!?
Mganar a bazata tazomai yasa ya Dago kansa yana kallonta ido ta Sakamar yasa ya kasa jurewa ya Maida kansa kasa Cikin Sanyin muryansa yace"Taje wajen aiki Hajiya..!
Kai Tsaye tace"Da zata fita ta tambayeka..?kokuwa haka nan take saka kai ta fita don ta isa..?ai ko aiki ne Kana da Hurumin Sanin Lokacin Fitanta da Lokacin Dawowarta..!
Kansa na kasa ya kasa Dagowa Hajiya ta kalli Saifullahi tana Fadin"Saifullahi kai abokinsa ne ka rika mai Fada..In ya Zauna haka..To wlh haka Rayuwarsa zata kare ba amfani..!
Tafada tana Kokarin Saita Fushinta Daga Saifullahi har Sulaiman basu ce komai ba kansu na kasa Daman sun Tsamnani haka Daga bangaram Hajiyan.
Tana shirin kara mgana Sukaji Sallamarta Cikin Siririyar Muryanta Kamar koyaushe gabadayansu suka Dago suna kallonta Harta Sulaiman da Saifullahi da kansu ke kasa.
Tana Sanye da Hijabi mai Ruwan kasa iyakarsa Gwiwanta ana ganin Farim Wandonta da Takalmin kafarta Baki Sau ciki na mata,Karamar Jakarta na Rataye a gefenta sai wayarta Dake hannunta,Hijabin mai irin Daurewan nan ta sama ne ta Tamke kanta karamar Doguwar Fuskarta mara yalwar Fara"a ce kadai ke waje ake gani Hatta Hannunta tana Sanye da Safan Hannu ne.
Lokacin DAtayi sallaman Farko basu amsa mata ba itama alokacin bata Lura dasu ba sai da ta kara yin Wata Salamar taji Muryan Hajiya karama ta amsa mata sai Lokacin takai idonta kansu Gabanta sai da ya Fadi Lokacin Da suka Hada ido hudu da Hajiya Zabba"u batasan Dalili ba Kwata kwata matar batayi mata ba ko domin Duk karon su da juna bamai Dadi bane,Ta Fara shaidata ne Sanda suka je Gidansu sukaci musu Zarafin ita da Hajiya Salame Lokacin Auran Sulaiman da Sunaira,sai kuma itama Dawowarta bayan taji an Daura mata aure da Kaddaranta Dole ta Shaidata kuma Dole ganinta ya Fadar mata da gaba sam matar bata da Mutumcinta da ganinta zai zama alheri gareta
Cikin Lokaci Daya ta kare ma Wadanda ke Falon kallo nan kuma Take ta dauketa kanta har ga Allah taso ta wucene saboda ita bata Tusa kanta inda ba"a Bukatarta sai dai kuma in Tayi haka bata kyauta ba taci Amanar Tarbiyan Inna da Baba kuma ko banza Uwa uwace koyaya aka Ki Daraja naka ranka zai baci,bata da yadda Zata Gujema Kaddaran data Ratso matar nan cikin Rayuwarta sannan taci Darajan Hajiya karama Saboda tasanta Lokacin Tarewarta su Inna Tanin Zuntu Kargi suka kaita sai da Maimartaba ya saka mata albarka aka saka mata alkyabba,kana Ita Hajiya karama da sauran manyan ya"yan Sarki su Hajiya Uwani suka kawota nan gidan matar tana da Kirki ba Halinsu Daya da Mahaifiyar Sulaiman ba.
Tuna haka yasa ta fasa wucewar ta karkato Cikin Takunta Daga nesa ta Tsaya ta kwabe Takalmin kafarta kafin ta Fara tako Doguwar kafarta Cikin Safa ta kariso nesa da Su Sulaiman ta Duka Tana Fadin"Sannunku da zuwa Hajiya..!
Tafada Cikin Amonta na koda yaushe ba Sakewa,Hajiya karama ce kadai ta amsa Cikin Fara"a banda Hajiya zabba"u dake mata kallon Sama da kasa Cikin kaskasci.
Jin Muryanta da Wasim yaji yasa Hankalinsa ya koma kanta Har yana Kokarin Faduwa daga Hannun Hajiya wajen sauka Cikin Murna yake Fadin"Anty...!
Da dan amon,Wanda yasa Wafiyya Dake Lafe jikin babanta ta Dago ai tana ganinta ta fara Zillo Daga Jikin Babanta Tana fadin"Anttyyy...!
Da Yar siririyar Muryanta Sauketa Sulaiman yayi tana Dagwa dagwa ta isa ga Sunaima wanda ta Saki Fuskarta sosai ta Bude musu Hannayenta suka Fada ta Hadasu ta Rumgume Cikin Farincikin Data ke shiga duk Sanda Take tare da ya"yan yar"uwanta.
Baki Hajiya ta saki tana kallon Ikon Allah Hajiya karama kuma abun ya bata Sha'awa yasa tace"Allah Sarki..Ko yaro akace yasan nashi da mai kula Dashi.!
Kamar Hajiya ta mangareta Takeji Da mganarta,Hararan Sunaima kadai Take yi wacce batasan tana yi ba Hankalinta na wajen su Wasim tana Jin Hiransu Wafiyya sai nuna mata Biscuit  din hannunta take yi tana gaurancinta Wasim ne yace"Anty Uncle na gidan Inna ya siyamana..Inna yau ita tamana wanka ta Saka mana kayan nan...kuma kuma ta goya Wafi..!
Sunaima tana Shafa kansa Tace"Ah lalle ku yan gatan Inna ne..La muga Abun dadin da Uncle din naku ya siya muku ko Wafiyyata..!
Ba gaddama ta mikamata hartana Kokarin Tusa mata abaki Sulaiman tana Gefen idonsa yake kallonta bai Taba zaton haka take da kyakyawan alaqa mai karfi da yaran nasa ba Duk da Suna yawam Kiran sunanta Koda bata wajen
Karba tayi ta rika Binsu Daya bayan Daya tana Saka musu abaki itama Wafiya ganin haka yasa ta Dauka ta Nufi bakin Sunaima dashi Dole ta Bude ta sakamata shima Wasim haka ganin ta karba ta Tauna tana Fadin"Kai so sweet...!
Yadda tayin ne kamar na yara yasa Wasim ya kyalkyalce da Dariya ganin haka yasa Wafiyya ta tayasa akaron Farko sai alokacin ya Taba ganin Dariyarta har Fararan Hakoranta na Gaba masu Dauke da Wushirya suka bayyana,sai dai ba Dariya gabadaya ba Fara"a dai da Sakin Fuska.
Saifullahi ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Antyn yara mun wuni lafiya..?
Sai lokacin ta Dago suka Hada ido da Sulaiman Daya Dago yana kallon Saifullahi gabadayansu atare suka Janye Daga Kallon juna kamar Wasu makiyan juna.
Tasan Saifullahi tun Sunaira Nada rai in Sulaimam zai zo gaida su Inna Tare suke zuwa saidai batajin ko gaisuwa ya Taba Hadata da shi,Batayi mai Wulakanci ba ta amsa da Lafiyalau tana maida Hankalinta kan yaran ganin Har Lokacin Hajiyar batace mata komai ba yasa ta Mike ta gaji da Tsuguunawa Tana mikewa Wafiyya ta Daneta Dole ta Dauketa Hakama Wasim ya kamkame hannunta yana Fadin"Anty bum bum..nidai kimana bumbum..!
Kumatunsa ta shafa Tana Fadin"Shikenan my son..Ammh sai anyi Homework anyi sallah mun ci abinci mun koshi sai mu samuMore Power ko..!
Baki ya washe kafin ma ta kara mgana ya rarumi jakarsa da Luch box dinsa ya Nufi Dakinta ita sai ta Dauki na Wafiyya Dake gefen Sulaiman ta Mike Tana kallonsa Kadan kafin Tace"Wani Daki za"a gyara musu Hajiya..?
Mgana take yi mai ammh bata kallon Barayinsa shima bai Kalleta ba sai ma yayi kamar bai jita ba..
Hajiya karama ce tace"Ki barshi kawai Sunaima..su Samira zasu gyaramana indazamu sauka..!
Kai ta gyada kafin tace"Abinci fa Hajiya..!
Kai ta girgiza mata tana Fadin"Munci Abinci da muka iso..Yanzu Sallah kadai ya Ragemana sai barci..!
Kanta na kasa tace"Allah ya Huta gajiya Hajiya..!
Ta amsa mata da Ameen daga haka ta Juya Dauke da wafiyya a Jikinta Hajiya Zabba"u Dake binta da wani kallo Ta Dakatar da ita ta Hanyar kiranta da.
"Ke...!
Sunaima kamar bazata Tsaya ba sai kuma ta Tuna wani abu ta Tsaya Kyam kafin ta Juyo Idanuwanta Tar cikin na Hajiya zabba"un Data mike Cikin Isarta da Izzarta ta fara taku zuwa gabanta,sai da ta kalleta Daga sama har kasa irin kallom kaskastun nan kafin ta nunata da yatsa tana Fadin"Ke diyar Talakawa mara Tarbiyan..ko kin ki ko kinso ni Haifi Saraki..nan gidan Da"ana ne,saboda haka baki da Hurumin da zaki zaban inda Zan Sauka kin gane..?ki tsaya iya matsayinki Tsohuwa kawai...!
An cuceni Saraki..su Maimartaba basu mai adalci ba Wlh..!
Tafada Tana wani juya Jikinta Cikin Bacin rai kafin ta bar Sunaima nan Tsaye ta wuce ta Fara haura Stair kamar irin matar gidan gabadayansu da kallo suka Bita har ta kulema ganinsu,Hajiya Falmata ta Dafe kanta kafin ta Dago tana kallon Sunaima Data Zugum tana Kokarin Daidaita kanta Ta mike tana fadin"Kiyi Hakuri Sunaima..!
Sunaima da idanuwanta suka Tara kwallah tace"Laa..Bakomai...itama din ai tana Kokawa da Kaddara ce..Kaddaran data Dauki Rayuwar Yar"uwata ta kuma kawoni wannan Mtsayin da nike kai..!
Daga haka ta juya ta wuce Dakinta suka Bita da kallo Har Sulaiman bai ji Dadi ba ba kyau cin Fuska ammh waya isa yace ma Hajiya bata kyauta ba ko Hajiya Falmata bata isa ba Wannan Daga Abba sai Maimartaba.
Saifullahi mikewa yayi yayi ma Hajiya Karama Sallama Sulaiman ya Tafi rakasa suna zuwa Jikin Motarsa ya Dafe kai ya kasa mgana Saifullahi ya Dafasa yana Fadin"Ka kwantar da Hankalinka..Insha Allahu alheri ne zai Faru..!
Baice komai ba illah hannu daya mika masa sukayi musabaha Daganan sukayi sallama Saifullahi ya shiga Motarsa ya Fice daga gidan zuwa Falt din Daya kama yana zaune anan anguwan Mu"azu.
Koda Sulaiman ya Dawo Cikin Gidan Hajiya Karama ma ta Haura sama Inda Jerin Dakuna Suke kawatattu Shashen Sunaira Dataki zama shi Samira ta gyara musu mai Dauke da Falo da Bedroom guda Biyu ta gyara Musu kowacce bedroom dinta Dabam
Hajiya karama koda ta Haura Har Hajiya Zabba"u ta shiga wanka yasa itama ta Shiga Domin tayi wankan tayi Sallah agajiye take so take ta samu ta Huta Tunda Gobe tun safe zasu Dauki hanya.
Shima Sulaiman Dakinsa ya wuce yayi wanka ko Sallar mangariba bai yi ita agida yayi ta Tunda ta Kwacemai sai fita Sallar Isha"i daganan ya dawo ya Dauki Mota ya je siyo musu gasasun kaza Hajiya kuma Kilashi Saboda yasan Tana so Habib ya Kira adaran yace gobe da Sassafe ya aiko Agent dinsu da Madara da Fura da yawa Hajiya zasu tafi dashi Abuja.
Sai wajen 9pm ya shigo Gidan da Magajiya yaci karo ya bata Leda Biyu Daya yace su Dauka Dayan ce mai Tarkacen su Ice cream yace ta Mika Dakin Sunaima na yara ne Leda Biyun ya Haura dasu sama
Yana Shiga yaga Hajiya karama afalo Tana shan Ruwa Dukawa yayi ya mata sannu da Hutawa ya tura mata Dayam Ledan yana Fadin"Hajiya ga Kaza nasan kina sonta sosai..!
Hajiya karama taja Ledan Tana Fadin"Barin ma gashin Yahuza Saraki Allah yasa ya saka Cabeji sosai..!
Yana Dariya yana kallonta Tana Budewa Ta Dago tana kallonsa tace"Saraki Allah yayi maka albarka..Har Miyauna ya Tsinke kuma Wlh na Koshi ammh ina ganin Kazan nan naji cikina kamar ban ji komai ba..!
Yana Sosa kansa ya amsa mata da Ameen yana fadin"Fura da Madara sai gobe nasa akawosau ku Tafin ma Abba da su Sadiya dashi..!
Hajiya karama na Faman cin kazanta Tace"Ka Huta gori kullum sai Abbansu yayi mana Gorin Danmu yana mai Rowar Madara da Fura..!
Dariya kawai yayi sanin halin Abba Tun wani kai Ziyara daya taba yi Kamfanin nashi aka shakomai Bayan Mota da Madara da fura ya koma Abuja yaji Dadi kullum sukayi waya da  shi sai yace Ina Madara da Fura Saraki..?shikenan kamar kamin asiri Tunda na Fara shan Furanka da madaran ma"aikatanka shikenan ban iya shan wata fura sai naka Musamman nake Biyan kudin Agent Daga Kaduna zuwa Abuja..!
Shidai sai dai yayi Dariya kuma fa Duk wata in aka samu Riba yana aika musu ammh Daga yaran har Abba sun mayatan son Furan nan da madara ko shi waya sukayi da kannen nashi sun Rika Magiyan Ya Saraki Fura da madara..!
Nan ya bar Hajiya karama ya Shiga Dakin da Hajiya ta Sauka Da Sallama ya Shiga Tana Zaune gefen gado tana mgana a waya da Hajiya Salame tana jin Shigowarsa sai tace ma Salame"Zan kiraki zuwa gobe..Saraki ne ya shigo..!
Jin haka yasa Hajiya Salame ta Datse Kiran Murna ya kamata Domin abayanin Hajiya Zabba"u akwai Nasara a wannan karon Laila ZAta samu Cikar Burinta.
Kan Cafet ya Zauna Yana dan Jan Jallabiyam Jikinsa ledan Hannunsa ya Mikamata yana Fadin"Kilishi ne Hajiya na siyo miki..!
Daukan Ledan tayi tana Fadin"Ah..Allah yasa albarka..!
Tafada tana Budewa ta Gutsro ta Faraci sun zauna shuru bamai mgana sai wayar Saraki Dake gaban Aljihunsa ne ta Katse Shirun nasu ta Dauki kukan neman agaji yana Fito da ita yaga sunan Abba ne mai kiran Da Sauri ya Kalli Hajiya Sanda Tace"Hala Abbanku ne..?
Kai ya gyada mata baki ta Tabe Tana Fadin"Ya kirani yana Fadan meyasa zamu kwana agidanka..Saraki ni da Gidan D"ana sai ace sai naje wani Waje Sauka..!
Bai ce komai ba ya Daga Kiran suka Fara gaisawa kafin Abba Dagachan Bangaran yace"Saraki yanzu bada Dadewa ba Zabba"u ke fadamin gidanka suka sauka ko..?
Kai ya gyada mata kafin yace"Eh Abba..!
Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Na mata Fada daga ita har Falmatan Duk da Sai abunda Zabba"u ta Zaba shi Zatayi..Gotai gotai dasu suna Iyaye suje Gidanka kwana..?meyasa bazasu Tsaya su kwana akargi ba in ma Kadunan ne su sauka Gidan Hajiya Giwa mana(Jamila)..!
Shidai Sulaiman bai iya cewa komai ba Ganin Hajiya na gabansa Abba yacigaba da Fadin"Ka yi Taka Tsantsan..nasan Halin Zabba"u sarai ko Zuwanta Kargi ba"a banzaba..Bata son auranka da yarinyar nan kada ta Wulakantata kasan Halinta bata da Girma sai na Shekarunta..!
Sulaiman ya gyada kai yana Fadin"To Abba..!
Daga haka sukayi sallama suka Kashe Wayar ta kallesa Kafin tace"Mganata yayi maka ko..?
Kallonta yayi kafin ya Sanda kansa kasa bai ce komai ba Tabe baki Tayi tana Tura Kilashinta acikim Baki Lokaci Daya Tana Fadin"Daya kwantar da Hankalinsa yanzu zan gama abunda ya kawoni..Gobe Zamu koma Gida bsshikenan Fadan ba..!
Shidai bai ce komai ba gabansa ne ya Fadin jin abunda tace sai dai bai Motsa ba Har sai da yaga tana ta Cin Kilashinta yasa yadan Muskuta zai Mike da Sauri tace"Ina zaka..!
Koma ka zauna mgana zan yi dakai..!
Kamar wanda ya samu Shanyewar barin Jiki haka ya koma ya Zauna kansa na kasa,akwai sansayar madaran Holladian aciki ita ta Dora Dashi bayan ta gama cin Kilashin ta Maida Ledan ta Kulle ta Dorata saman Gado tana dan gatsa Lokaci Daya tace Alhamdulillah.
Saraki ta kallah kafin tace"Sulaiman...!
Tafada Cikin son nunamai Muhimmamcin mganar bata Kiran sunansa kai Tsaye sai wani abu ya Faru yasa ya Dago yana kallonta kafin yace"Na"am Hajiya...!
Kara Kiran sunan nasa  tayi ya amsa mata yana kokarin Boye razanarsa.
Cikin Kaushinta tace"Wacece ni a gareka..?
Cikin mamakinta ya Dago yana Fadin"Ke uwace...Mtsayin Mahaifiya..!
Ajiyar rai ta sauke kafin ta Mike ta gabaansa ta wuce zuwa gaban Wardrope din Dakin kafin ta Cigaba da Fadi"indai ni uwace..Mahaifiya gareka Sulaiman ina Umurtanka..Duk Sanda Maimartaba ya Kira ka Domin ya tambayeka kan wasu abubuwa kada ka amsa mai da A"a ina so a duk Abunda Zai Tambayeka ko Zakaji Daga garesa ya zama amsarsa Eh Saraki..!
Cikin mamaki yake bin bayanta da kallo kafin yace"Hajiya koda Eh din yana Nufin A"a ne..!?
Kai Tsaye ta Juyo tana Fuskarsa Lokaci Daya tace"Ina Nufin haka saraki...Umarni ne ba Shawara nake baka ba In har ka Daukeni da Mtsayin da kace na Mahaifiyarka..!
Tsareshi Tayi da idon Dayaji kamar ta gama Dauresa da Jijiyn Jikinta Yasa kansa na kasa yace"Insha Allahu Hajiya Zan yi yadda kikace..!
Yafada cikin SAnyin Murya Baki ta Washe Tana Fadin"Allah yayi maka albarka..!
Saboda tana ganin ta gama da komai ba kuma ai ta jira jin Karban auran Laila wajen mgabatanta Domin tasan Shurun maimairtaba abunda yake Nufi,takuma san yadda Shakuwa da kauna ke tsakaninsa da Saraki bazai Taba mai Dole ba zai yanke Hukunci ne da Abunda Saraki ya Fadamai Shiyasa ta Fara ma abun Tufkar Hanci ta Riga Maimartaba Nuna ikonta kan Abunda ta Haifa.
Haka ya Fice ya barta Cikin Farimcikin yayinda shi kuma ya fice cikin zullumin yagama Sarewa wannan karom Hajiya ta Shirya koma Memene take shirin aikatawa wanda bazai wuce kakabamai auran Yarinyar da bai taba mata kallon zai iya auranta ba to yayama ya kare da kaddaran auran yayar matarsa ai bai gama ma Cike Raunin rasa Sunaira ba Ammh ana neman a Rikotomai Bala"i acikin agidansa.
Kuma awannan karon in yaBijirema Hajiya Tsab sai ta Dagamai Nono ya lura tafi Girmama Mama salame da Ra"ayinta kan komai shifa Kanwar Abba ne ammh sam batamai ba ta Cika Hade Haden Munafunci Ya Tsaneta Tun lokacin da suka ja Sunaira tace ta Fasa auransa.
Ranar rabi da Rabi yayi barci asuban Fari yayi wanka ya Fice sallar asuba amasallaci yayi Zamansa sai 7am na Safe ya dawo shima Habib ne ya Kirasa yace Agent yazo baya gida Shiyasa ya Dawo Direct Booth din Motar su Hajiya aka saka manya packeg din Fura da Madaran da Sulaiman yasa aka kawo Daga Kamfaninsa.
Koda ya shiga Falon Magajiya ya gani Tana ta Faman Shirya Dining Samira kuma na gyaran Falon Dukawa sukayi suka gaisheshi ya amsa sau Daya ya Haura sama Masaukin su Hajiya ya Fara Shiga yayi mamakin ganin su Da ga ita Har Hajiya karaman duk sun Shirya suna ma Shirin Saukowa ne.
Har kasa ya Duka ya gaishesu yau kam Hajiya Cikin da Fara"a ta amsa Yana Sosa kansa yace"Hajiya da wuri haka..?na zata sai an juma zaku tafi..!?
Hajiya tace"Hajiya Karama Fadamasa irin yadda Abbansu yayi ta Kiranmu Tun asuba kamar ba gidan Dan"mu muka kwana ba..!
Hajiya karama na Dariya tace"Barmu mu mika yanzu Saraki kada Abbanku ya Biyomu kuma..!
Bai ce komai ba sai yake domin ina shi ina Dariya bai ga yadda Hajiya Zata kaisa ba kasa suka Sauko gabadayansu Daidai Lokacin Magajiya ta Dauko su Wasim Daga Dakin Sunaima Cikin Shirin makaranta Taab Dasu,Sulaiman suka Dafe ma wa Wasim ne ma yaje ya gaida su Hajiya Wafiyya kuwa Sarkin Rigima Kan Dining Su hajiya suka zauna zasu karya Datayi mgnan yaran Magajiya Cikin Ladabi ta Fadamata Hajiya ta basu abun karyawa.
Baki ta tabe ta Fara karyawa Lokacin Sani ya iso ya shigo suka gaisa dasu Hajiya ya kwashi su Wasin zuwa makaranta Umarnin Yallabai Sulaiman yau batare zasu fita ba sai ya Dawo kai su Lokacin su Hajiya sun mika.
Shi Tea kadai yasha Saboda Kada Hajiya tayi mgana,ga mamakinsa Hajiya na gamawa ta Mike Tana Goge Bakinta da Tissue ta kallesa Tana Fadin"Bari naje na gaida Matarka Tunda ita masu Dattin hula basu koyamata Fitowa ta gaidamu ba..!
Daga haka ta wuce suka Bita da kallo Shi da Hajiya Falmata ba kuma wanda yace mata ta dawo Sanin bazata Dawon ba..
Daman ai tasan Dakin Domin an Fadamata Dakin Sunaira na Baya aka Sakata itama kuma alokacin ita ta Hana Sulaiman ya bada Samansa kamar yadda taji Abbansu na mgana da Farko Sama ai na yar masu abun ne Wato Laila.
Sunaima na kishingide kan gadonta Tana Sanye da Bakar Abaya ne Kirar Armani ta Daure kanta da karamin Vail din abayan baki,bata yi kwalliya ba ammh Karamar Fuskarta ta Boye Shekarunta sosai.
Novel din Hausa ne a Hannunta Masarautarmu na Sumaiyya Takori Jiya a asibiti Aneesa ke bata Labarinsa Taji tana son karantawa sai tace ta aro mata ta karanta jiya ta gaji data dawo ga Hidimansu Wasim bata samu natsuwa ba sai yanzu da suka Tafi makaranta yunwa take ji Tun jiya bataci komai ba,kuma bata son Fita Saboda su Hajiya bata kaunar ta kara kai kanta inda za"a kara Cin Zarafinta Shiyasa ta Nannade yunwarta ta Zauna adaki gashi sai karfe Daya Zata Tafi asibiti.
Ko Sakon Sulaiman na Jiya bata ci komai aciki ba su Wasim sukaci gazan Wafiyya tayi ta barna da Ice Cream din Sauran ma ta bama Magajiya ta Saka musu Fridge.
Batasan da Shigowar Hajiya ba Domin ai batayi sallama ba kuma Kofar Daman tana Bude ne Hankalinta yayi Nisa Cikin Karatunta taji Muryanta asama.
"Sannu ishashiya wacce bata gaji Tarbiya ba..!
Taji Hajiyar ta Fada asaman kanta kana ta Dago Da sauri suka Hada ido,
Da sauri ta dan Tashi Zaune tana gyara Gyalen kanta Tace"Ina kwana Hajiya..!
Cikin Fusata ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Rike ina kwananki..Da ban kwana ba zaki ganni..Wato ke kin isa har muka kwana muna Shirin Tafiya bamu ci Darajan da zaki Fito ki Gaishemu ba ko..?saboda ba Uwarki bace tazo ba ko..?
Da Sauri Sunaima ta Dago tana kallonta Cikin kananun idanuwanta Hajiya tace"Eh nace saboda ba Uwarki bace ko Zaki Rama ne..?
Sunaima sai ta Sadda kanta kasa batace komai ba Tana Kokuwa da Bacin Ranta Hajiya ai taci Darajan mai Daraja da Tuni ta Raina kanta datake kokarin Zagin mahaifiyarta.
Ganin tayi mata Shuru kanta na kasa kuma Taki bata Hakuri batasan kafinyan Sunaima bane shiyasa
Dakin ta karema kallo kafin tace"Bansan wata kaddarace ke Bibiyan Saraki kan ahalin ku ba..Da Fari kanwarki in ita ta Chanchanta na Ragamata ke baki Chanchanta da D'ana ba Wlh..Shiyasa nan da wata Daya da yardan Allah zan kawo wacce Zata Ingata rayuwarsa data ya"yansa..!
Daga haka ta juya zata Fice Sunaima ta Dago kanta Cikin sanyinta tace"Ni kuma don Allah ki Taimakeni Hajiya da Ikon da kike dashi kan D'anki ki Saka ya Sakeni...Domin ni kaina nasan ban Chanchanta ba Shiyasa akullum nake kukan Kaddaran data Dauke yar"uwata mai kwarin zuciyan da Zata iya Daukan wannan yakin ya Ratsoni Cikin wannan Kaddaran..Kadarran Auran Dan"ki da kokuwar da Har Abada Ni Sunaima bazan iya Shanyeta ba Duk Karfin Zuciyata kuwa..Mganar ya"ya kuma kada ki manta Hajiya Duk inda  Jini yake yafi Ruwa Amfani ajikin Dan adam..!
Tana gama Fadin haka ta Sauko Daga kan gadonTa kalleta ido na Cikin Ido kafin Tace"Allah ya kiyaye hanya..!
Daga haka ta Tura Kofar Tiolet din Dake Dakin ta shige saboda jin kuka ya Taho mata batasan Hajiyar taga Rauninta ko kadan.
Hajiya Zabba"u ta Ciji yatsa Lalle ma yarinyar nan wato haka take da Tsauri ido Lalle suna da bambamci Domin abaya Sunaira ko marinta Zatayi bata iya Daga ido ta kalleta ammh yau ji yadda wannan yar iskar ta Tsaya Tana Fadamata mgana son Ranta Wlh sai tayi mganinta.
Ranta bace ta Fito Daga Dakin ta Iske Saraki da Hajiya karama suna Jiranta Samira ta mikama Jakarta Tana Fadin"Muje Mota..!
Daga haka ta wuce suka bi bayanta Sulaiman kansa kawai ya Girgiza yakasa mgana
Sai da Motarsu ta Fice Daga Haraban gidan ya samu salama komawa yayi Cikin Gida ya Shirya Cikin manya kaya yau Sani ya dawo alokacin suka Fice zuwa Ma"aikata ammh duk wanda yaga Sulaiman yasan baya Cikin Natsuwarsa kamar ko yaushe.




*Shakira..*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now