9

662 79 24
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 9*

Inna tayi mata fada sosai da Nasiha Cikin Tarin Hikima inna ba Fada ba Hayaniya cikin Ruwan sanyi tamata Fada sosai ta ankarar da ita Kuskuranta,bawai domin bata gane hakan bane tana sane sai dai bata Shirya karban kaddaran nan tata acikin Lokacin nan bane tana ji tana gani kamar komai amafarki kamar Zata Farka taga Sunaira ta Dawo duniyar nan tace mata komai Daya Faru wasa ne mafarki ne.
Yau taga Hawayen Inna Sanda ta kalleta bayan sun natsa acikin Daki jiya da dadddare tace"Sunaima Don Allah ki Kula ki kuma natsu ki karbi Kaddaranki Hannu Biyu..mijin kanwarki ai ba Haramun bane don ki auresa Sunaima Daga ke sai yar"uwanki Sunaira na Haifa Mata Sulaiman ya Shigo Rayuwar Sunaira ashe Allah ya Fadada kaddaranku Sunaima Rayuwar Duka ya"ya na zai shigo...Kinsan danginsa basa kaunarmu Tun marigayiya yar"uwanki Ballatana yanzu da bata Raye aka maye Gurbinta Dake  kinsan yadda abubuwa suka lalace har nan Gidan Mahaifiyarsa tazo ta karemana cin Mutunci bayan wanda Tayi mana Lokacin Farko Meyasa ke bazaki zama kamar Sunaira ba..?bata bama makiyan ta Daman ganin gazawarta ba Har ta bar Gidan Duniya bamu taba jin kanta da Sulaiman ba Sunaima meyasa kema bazaki kama Kaddaranki hannu biyu ba..?ki rike auranki Sunaima Domin kaddaran Data Hadaku bazata warware kanta ba Ina ji ajikina kece Zahirin Sulaiman Kinga tun kina ke kadai yanzu gashi an auro masa yar"uwansa in baki San kinayi ba Sunaima Wlh zakizama yar kallo sai dai kiga anayi..Yau bazan miki Fada ba sai dai zan Lallasheki da kalmomin Bakina ni Mahaifiyarki don Allah ba Domin ni ba Ki yi Domin Allah ki natsu agidanki ki Rumgumi mijin kanwarki Domin ayanzu Shine KADDARANKI..!
Lokacin da Inna ta gama Fada mata haka kuka ne ya kwace mata Ita kanta Sunaima Kukan take alokacin sai dai bai kwace mata ba sai yanzu Datake Tuna kowani gabar mganar Inna.
Gefen gado ta zauna Hawayenta suna Shatata aduka Idanuwanta Biyu,Mikewa tayi ta Isa gaban makeken madubin dake Dakin ta ja Dirowan ta Dauko wani Hoto karami Daga ganinsa yadan kwana Biyu.
Hoton ita ne tana Sanye da Kayan makaranta baki da Fari sunaira Tana Gefenta sanye cikin kayan gida Sai Ahmad sai Inna sai Baba itace a Tsakiyarsu tana Rike da kyautar da aka bata na matsayin shugabar Dalibai na makaranta Secondary gwannatin data gama alokacin wato Headgirl ranar Candy sune duka yan"uwanta suka zo mata bazata taba mantawa da Ranar ba sanda zasu yi Hoton bata saki Fuskarta ba Sunaira alokacin bata Wuce shekaru15 ba,Ta kalleta Tana Fadin"Antynmu Don Allah kiyi Mirmishi..In kikayi Mirmishi kin fi kyau..!
Alokacin bata Dauki mganar da Muhimmanci ba Sai da inna tace"Gayamata Koda yaushe Fuskar a Murtike kamar Kunin kanwa..!
Gabadayansu suka Tsintsire da Dariyan Dayasa Dole itama ta Saki Hakoranta Caraf mai Hoton ya Dauka Daidai Ahmad da Sunaira sun Kwanto mata akan Duka Kafadunta suna Dariya Harta Baba Dake gefe shima yana Dariyan aka Daukesa wannan Hoton bazata iya rasa ba Shiyasa har yau take Tare dashi Wani irin Gunjin kuka ne ya Sarketa Dayasa ta Durkushe nan ta Fashe da kuka kan Kirjinta ta Saka Hoton ta Kamkame Tana Kuka Cikin Dan Sauti take Fadin"Meyasa kika min haka..?
Meyasa kika Tafi kikabar min Kaddaranki Alhalin kinsan bazan iya Jmarin Daukanta kamar yadda kika Dauka ba..!?
Ta ke Fada Tana kuka kuka mai Cinrai wanda ke Fitowa Daga karkashin Zuciyarta sosai da sosai tana Rike da Hoton Duk duniya ba wanda ta Shaku Dashi Sama da Sunaira Duk da akwai Tazaran Shekaru Biyar atsakaninsu Sai dai ita Tana kulafuncin yan"uwane Ita Tsakaninta da kawa Sallamar Musulunci,bata sakin Fuskar da wani alaqa zai shiga Tsakaninta da Mace ma ballatana Namiji akwai sa"anin Haihuwanta a Zuntu Wlh gajiya Inna Tayi ta Kyaleta ko auran su ya Tashi sai dai Inna taje bata zuwa Inna Tani kanwar Inna ce Uwarsu Daya Ubansu Daya Lokacin da zata aurar da Habibanta ba yadda Inna batayi ba Taki zuwa Habiban har nan Kaduna take zuwa ta kwana Saboda Sunaima ammh sai dai taBige da Kawance da Sunaira Gabadaya Kaawaye da yan"uwa sai dai kaji Suna Fadin Sunaira mai Harka da son Jama"a banda Sunaima da ba kowa ke gane yanayinta ba Koda Inna tazo Tan Fada Baba keTare mata Saboda ai Halittace ba wai ita saka ma kanta ba Tun Lamarin na Damun Inna Har ya zo ya Daina ta sakama Sarautar Allah ido.
Bazata taba manta Watarana ba Lokacin tayi Candy kafin ta Samu Gurbin karatu anan Barau Dukku Dake Zaria Suna zaune atsakar gida Ranar da yammah Sunaira na wanke wanke Sunaima na ma Inna Tatan nikan Gero ita kuma Inna na Girki a madafa jefe jefi suna Taba Hira,Tsakanin Inna da Sunaira ita nata sai dai ta kallessu in Sunairan ta Tabo inna sai tayi dan Mirmishi wani yaro yayi sallama yace wai ana Kiran Sunaima awaje nan da nan Sunaima ta kara Hade ranta Tace yaron yace batanan Inna tayi Zaraf tace ace gatanan zuwa alokacin kallon Inna Tayi tana Fadin"Kikace gani nan zuwa..?
Ni fa ba zuwa zan yi ba Inna..!
Inna ta aika mata da Dakuwa Tana Fadin"Kinga naki nan...kada Allah yasa kije..Ke wai yaushe zaki hankali Sa"anikki yanzu duk suna Dakin kansu..Ammh ke ko Tsayayyen Saurayi baki dashi to yaushema kika Sakarmusu Fuskar da zasu Tunkare ki Shifa Namiji yafi son mace mai Fara"a da Sakewa ba irin ki ba Kullun Fuskar a murtuke kamar Kunun Daya kwana bai ga Siga ba..!
Alokacin Sunaima Baki ta Tura batace komai ba Sunaira ce ta saka Dariya Tana Fadin"Kai Inna..Ke daina cewa haka..Antynmu don Allah ki je..Kuma gaskiyan Inna ne ki Rika dan Fara"a na Rantse Ranar da muka Dawo daga Islamiya Inna inajin Wasu Samari a bayan mu suna Gulmarta wai bata da Fara"a Daya Daga cikinsu har yana Fadin in ya ganta ma Wlh tsoron Giftawa ta Hanyar data Biyo yake Kuma fa itama taji kuma alokacin saima ta kara Hade ranta..!
Inna Tayi kayfci kafin tace"Rabu da ita..In taga kema kin samu miji kin Tafi kin barta ai sai ta shiga Taitayinta babban kobo..!
Alokacin Inna abakin yan Amin ta Fada Duk da Sunaira alokacin tace ba Ameen ba Sunaima batace komai ba,Inna bata kyaleta ba ta Fattaketa sai da ta Dauraye Jikinta ta Fita Tana Fita Taga Saurayin yana ganinta sai ya Duka yana gaisheta bakinsa na rawa yace Sunaira yake nema yaron ne yayi Shirme alokacin Dadi taji ta koma Gida Tana Fadama su Inna,Alokacin Inna kala batace ba sai ma Kallon tsausayi da rashin Lafiya Datake ma Sunaima.
Gama wannan Tunanin yasa ta kara Fashewa da kuka Ta Dago Hoton tana kallon Fuskar Sunaira tana Fadin"Meyasa kika tafi kika bar ni da Kokowar wannan kaddaran naki..?alhalin ke kadai kika Farota kuma ke kadai zaki iya kawo karshenta..Kinsani bazan iya ba..Ba zan iya ba..!
Kamar daga sama kamar kuma amafarki ko azahiri taji amon Muryan Sunairan tana Fadin"Zaki iya...Zaki iya Domin Kaddaranki ce Sunaima...Sulaiman da komai nashi kaddaranki ne ni aronta na kaarban miki..!
Waigewaige ta Farayi Cikin mamaki da Tsoro domin ita dai kamar taji muryan sunaira ganin ba kowa yasa ta Dauka Damuwar Datake Ciki ne Kuka take yi bamai jinta ballatana ya Rarrasheta.
Tana Tsaka da kukan ne taji ana Mata Knooking Lokaci Daya da Kiran Sunanta da Sauri ta Mike ta Fada Tiolet har ta neman Faduwa ta Wanke Fuskarta da Sauri tana Fitowa ta saka mayafinta Dake nan saman gado ta Goge Fuskarta Saboda Kada akarom Farko a Fahimci Rauninta.
Saida ta kalli kanta amadubi taga ta natsa kana taje ta Bude Kofar Hajiya karama tagani da Hajiya Uwa da Sauri tadan Rankwafa tana gaishesu
Suka amsa mata Cikin Fara"a Hajiya Karama tace"Muna son mgana Dake Ina Fatan ba damuwa zamu iya Shigowa..!
Da sauri ta basu Haanya tana Fadin"Ku shigo bakomai..!
Cikin girmamawa suka shigo Ciki Hajiya uwa tace"Rufe kofar Sunaima...!
Ba Musu ta Sakaya Kofar ta dawo nan kasa ta zauna su kuma suka zauna Nan gefen gado,Har Hannun Hajiya Uwa tataba Hoton nan da Sunaima ta Dauko,Dauka tayi ta Duba tana kallon kafin ta kalli Sunaima Dake kokarin zama nan Kasa kan Cafet din Dake Gefen gadon
Hajiya Uwa tace"Allah sarki..ga mahaifiyarsu Aliyu Allah ya jikanta da Rahma..!
Jin haka yasa Hajiya karama ta karkato itama tana kallon Hoton Cikin wani yanayi kafin ta Numfasa ta amsa da Ameen Hoton Hajiya Uwa ta bata tana Fadin"Ki rika mata addu"a ne in kin Tuna da ita ba Kuka ba Sunaima..!
Mamaki ya kamata ya akayi tasan tayi kuka..!
Koda yake ai Hajiya Uwa ta yi jika da ita Domin Jikiokinta ai sunyi aure suma Sun Haiyayyafa kanta ta Sanda kasa tana karban Hoton Hajiya uwa Tana gyara Mayafinta gefen kanta gashinta dake fari duk ya bayyana sai dai kudi da kuma Mulkin yasa Tana da karfinta Har yanzu Cikin wani yanayi tace"Meyasa Zaliha taki bari mu hada Laila da Sunaima musu Fada..?ko ta manta al'ada ne mai karfi yin hakan..?
Hajiya karama Tace"Nima nayi mamaki Wlh bakomai mu yi mata namu amtsayin mu na manya..!
Hajiya uwa ta Kalli Sunaima Tana Fadin"Sunaima kiyi hakuri bamu Hadaku keda abokiyar zaman naki ba..Ammh zamu yi miki Nasiha Tunda kece Babba itama zamu mata namu Insha Allahu..!
Sunaima dai kanta na kasa batace komai ba Sai dai ita abu Daya ke bata mamaki Yadda Take da Zafim Kishi ammh kwata kwata bata damu kan auran Sulaiman ba Domin ita kanta bata gama Sanin makomanta ba ballatana tasan wani abu wai kishi.
Ganin haka yasa Hajiya uwa ta fara ma Sunaima Nasiha sosai kamar yadda Zatama yarta ko Jikarta Daman ai Tun Sunaira na Raye tana Fadan karamcin matar ita da Hajiya Jamila.
Bayan tayi nata Hajiya karama ma Tayi mata Daga karshe suka karshe da ce mata"Daga ke har Laila Duka Dayane awajen mu..Domin maimartaba ya Nuna mana Rumguman wanda yake namu da wanda ba namu ba..Ku hada kanku ku Zauna Lafiya baki da mtsala min sani Tun ZAman yar"uwarki da Saraki musan Tarbiyan Gidanku msu Daraja ne don Allah kada ki bari wannan Darajan ta sauka itana Laila Tamu ce musanta sosai Musan zaku zauna Lafiya da juna..Allah ya baku zaman Lafiya Shima Sarakin mun kirasa yace suna da baki ne office in ya kariso kafin mu tafi zamu masa nashi shima insha Allahu..!
Kanta na kasa take Fadin"Insha Allahu baza ku samu mtsala Daga bangarena ba..Nagode.!
Mikewa sukayi Lokaci Daya Hajiya karama Tace"Allah yasa zamu harama
Akwai kayan gara Daga maimartaba suna Babban store dinku..Zamu haraman tafiya Akwai masu komawa Kargi wasu kuma Gidajensu zasu koma..!
Sunaima ta Mike tana Fadin"Na zata sai gobe..!?
Hajiya karama tace"A"a kowa yau zai tafi..!
Daga haka suka Fice bata bi bayansu alokacin ba sai da ta adana Hoton nan ta Dauko Hajibinta Marun Dogo ta saka kana ta Fito koda ta Fito Duk suna Saman Laila sai Daidaiku ne nan Falon irin su Safiya sai dai suna ta Fita Haraban gidan daga  gani suna Haraman Tafiya ne Cikin kannen Sulaiman banda Radiya ba wanda ya gaisheta sai Raliyan Hajiya karama Sauran sai kallon banza itama batama matsa ma kanta ba Ta koma Gefe Tana Kallonsu Saboda Hajiya uwa da Hajiya karama ta fito tayi musu sallama ammh ita ba wanda ma ya Isheta gani acikinsu.
Zuwa chan sai gasu Hajiya Uwan sun Fito Gabadayansu Daga saman Laila Harda Hajiya Zaliha wacce ta hana ahada Laila da sunaima Waje Daya Domin ba"a son ta Fara haduwa da kowa sai aikin nan ya gamu kan Sulaiman sai dai sun ja kunnenta sosai kamar tajisu nan kuwa Tana Tsara yadda daga gobe zata fara Mulki ne acikin Gidan Muradin ranta.
Su magajiya ne ke ta Hidima da yara da sun bata waje su gyara tare da Hadiman da aka bama Laila,Sunaima tana Bin bayansu zuwa Haraban gidan Batare datace ma kowa komai ba itama ai bama su nuna sun ganeta ba su Wasim suna Hannun su Safiya Bama su kalleta ba sun ga iyayensu.
Suna Fitowa Haraban gidan sai ga Motar Saifullahi ta shigo Sulaiman na Gidan Gaba suka Firfoto suna gaisawa dasu Hajiya Uwa kannensa suna Gaishesu Wafiyya tana ganin Babanta ta Dafemai sai da ya Dauketa Gefe Hajiya Uwa da Hajiya karama da Hajiya Jamila da Hajiya Bilkisu suka jasa sukayi mai nasiha amatsayinsu na mamyan Iyayensu Duk da ba alokaci Alokacin La"sar ta kawo Jiki suna son su tafi da wuri ne.
Sai da suka gama ne ma ya Hangi Sunaima tana dagachan Gefe mamakinta yake yi koda yaushe bata Fara"a kamar wacce take cikin wani Bala"i,Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba itama Tana dagachan gefe bata Tusa kanta ba dasu Hajiya uwa kadai tayi sallama ta koma Cikin Gida bata Tsaya batama kanta Lokaci inda ba"a Bukaratata ba.
Tana komawa Daki wanka ta Sake yi Ta Dauro alwala tazo tayi sallan La"asar Tana kan Sallaya Taji Shigowar Mutum bata waigo ba Sulaiman ne ya kawo mata Wafiyya sai dai taji kamshin Turaransa da Tunda ta Fara saninsa Dashi ta sansa.
Gefenta ya ijiyemata Wafiyya wacce ta Rarrafa ta Lafe mata abaya ya Fice Wasim na Tare da Saifullahi su magajiya Nata aikin gyaran Gida Samira da Sauran Hadiman suna Ta gyaran Kitchen Dayan Hadiman na Laila tana samanta itama tana kara Gyara wajen da aka bata.
Sunaima bata kara Gigin Fitowa ba ta kame kanta adaki sai dai Da mangariba datafi tace ma Magajiya ta Hadoma Wafiyya Madara ta bata sai kuma ta Tambayi Wasim tace mata yana Tare da Yallabai bata Damu ba Sai dai fa Gidan yadau kyau da kamshi ko"ina Tsab ga Dining sun kawata shi da abinci kala kala kamar wata Gimbiya zata zo baki ta Tabe ita batama jin yunwa ko tana ji tana da Cake adakinta zataci Tundaga Lokacin suka Shige Daki ita da Wafiyya bayan ta bata madara ta mata wanka sai ta Fara Rigima sai ta Goyata ta Fara Jijjigata Har tayi barci.
Karfe 8:30pm na dare Saifullahi ya kawo Sulaiman da Wasim gida,da Ledoji biyu a Hannunsa Shake da kaji saiMadaran Holladian mai sanyi Shima Saifullahi ya matsamai sai da ya Siya Hankalinsa ya kwanta jin kowa ya isa gida Lafiya yan kargi sun koma yan Abuja ma da kuma yan Cikin gari.
Sallama sukayi ya nufi Cikin Gidan koda ya Shigo Falon ba kowa Magajiya ya kwalama Kira sai gashi sun Fito su uku da samira da Daya Daga Cikin Hadiman da Laila tazo dashi Cikin mamaki yake kallonta Kafin yace"Wannan fa..?
Yafada yana kallonta da Sauri magajiya tace"Ranka ya Dade ai Cikin Hadimai Biyun da Maimartaba yabama Hajiya Laila ce sunanta Mariya...!
Kai yadan Girgiza aransa yana Fadin an cukamin gida da yan aiki kamar nine Sarkin sai afili yace"Ina waffiya..!?
Ya tambaya duk da yasan Inda take Da Sauri Magajiya tace'Tana wajen Hajiya..Antynsu ranka ya Dade..!
Kai ya gyada kafin ya wuce ya barsu nan Duke kamar masu neman gafara Dakin Sunaima ya Nufa Samira ta juya tana kallonsa aranta tana Fadin bama Shashen Gimbiya Laila ya Nufa ba.
Tana Tsaye aharaban Dakin tana Dan Zagayawa da Wafiya yau Rigiman nata ya tashi ne sai zata kwantar da ita sai ta Farka daga alamu bata so ta Sauketa ne Sanye take da Rigar barci Iyakarta Gwiwa,kanta ko Dankwali babu Saboda Goyon Dake bayanta gashin kanta na Daure da band,Bata taba Tsammanin zai iya shigowa ba kuma Kofar tana Budene yasa kansa Tsaye ya shigo kuma sai da ya shigo yayi sallama Da Sauri ta Juyo suka Hada Ido Hudu alokaci Daya sai da gabansu ya Fadi haka kurum take jin Wani abu na mata Nauyi yau dingame da Sulaiman ganinsa Cikin Boyel Fari Riga da wando da Hula Zatinsa da Haibansa ya kara Bayyana acikin kwayan Idanuwansa sai take ganin kamar Taruwan wani Ruwa ruwa Daya kashe mata Jiki sosai,yasa ta Dauke kanta da Sauri gabanta na Cigaba da Fadi.
Shi kuwa Tundaga samanta har kasanta yake kallonta Siraran kafafunta Dake waje sun nutse saman Cafet,Shi dai yasan Siririyace ammh baisan haka take da rama ba sai yau Daga ganta Zahirinta sannan Goyon ya Bala"in yi mata kyau sosai Kamar itace ainihin wacce ta Haifi Wafiyya din..
Wasim Dayayi barci saman kafadansa ya isa kan gadon ya kwantar dashi Lokaci Daya yana ijiye mata leda Daya saman Madubi kafin ya Fara Takowa sai da yazo gabanta kana ya Tsaya itama da Sauri ta Ja baya Tana Mikar da gashin Idanuwanta Cikin kankanesu Dariyama taso bashi sai ya kanne Cikin Sanyin sa yace"ki Sauketa mana Tunda tayi barci..!
Kai Tsaye tace"Ai bazata kwanta bane..!
Ledan hannunsa ya ijiye yana Fadin"Injiwa..?saukota mu gani a Hankali..!
Yafada yana mika hannu a bayanta ba Gaddama Dole ta juya bayanta Ta Kwanto Towel din,tana Dan waigowa kada Ta subucemai a hannu ganin haka yasa yace"Ki natsu...in ba so kike ta Zamemin ba..Saukota a hankali kada ta tashi..!
Jin haka yasa ta kwance goyom Sulaiman ya Cafe Wafiyya wacce ta Motsa Hannunsa yayi kasa kamar Zata Fadi yasa da sauri Sunaima cikin Zafin nama ta Saka Hannu ta Tarota sai gabadaya da Wafiyya da Hannun Sulaiman zuwa Jikinta Gabadaya saboda Tana tsoron kada Wafiyya tasha kasa Wata Rigiman ya tashi.
Shima Sai gashi ya Ruke hannayenta Duka Biyu atare suka Kalli juna jin yadda Dumin hannunsu ya Hadu waje Daya yadda hannunsu suka Hadu sai sukaji kamar daman chan Allah ne ya Hadasu waje Daya Sulaiman ji yake wata natsuwa tana Saukarsa kamar ya Rike hannun Sunaira haka yake ji Sunaima ce ta Fara janye hannunta Shikuma yayi saurin rike Wafiyya Dakyau ta fara Motswwa sai ya Fara Lallashinta har ta koma ya isa kan gadon ya kwantar da ita kafin ya Juyi Sunaima ta Rarumi Hijabi ta saka Ta Rufe Jikinta..
Bai damu ba Ledan daya ijiye ya Duka ya Dauka yana Fadin"Sai da safe..!
Asaman lebe ta amsa mai har ya Fice ta Rakasa da Harara,yana Fita taje ta Rufe Kofarta Wasim taga yana ta Zufa ta kara karfin Ac,tunanin tatashe shi tayi mai wanka take yi sai ta fasa ta Ciremai Riga saboda yasha iska.
Bata jin barci kwata kwata yasa data Hau saman gadon Dake chan geefe ta kare Filo Saboda kada Wasim ya Fadi ta Dauki karamin Qur"aninta ta Fara Karatu Cikin Suratul Khafi.
Direct Dakinsa ya wuce bayan ya wuce Dakin Amarya Laila sai da yayi wanka ya natsa ya sanya Jallabiya Mai Ruwan Toka,ya Dauki Ledan hannunsa zuwa Dakin Laila Saboda Tuna Nasihar Abba da Sauran iyayan nashi,In har yaci Amanar hakan kamar yaci Amanar yardansu ne zai je ya kaimata wannan kazan Saboda ta samu abunda zataci Duk da yasan bazata Fito yau daga kawota taci Abinci ba.
Inda ace sulaiman yasan abunda zai kai kansa da bazai taba Tunkaran Dakin Laila ba wacce daman tasan da Shigowarsa gidan,Yana shiga Dakin Sunaima Samira ta Haura sama ta fadama marliya Dayar Hadiman Laila wacce tasata ta Fadamaata da Zarar Sulaiman ya shigo ita kuma ta saka Samira daman kawaye ne tun Farko sun zauna waje daya a gidan Sarki.

Ya shiga Shashen Falon shuru kamar ba kowa ko"ina Tsab yana tashin kamshi kai tsaye yake karema Falon kallo lalle an narka Dukiya anan wajen,Baisan ta ina ta Fito ba kawai ganinta yayi a gabansa ta Zube tana kwasan gaisuwa Cikin mamaki yake kallonta Fahimtar haka yasa Cikin Ladabi tace"Ranka ya Dade..Sunana Marliya ina Daga Cikin Hadiman da Maimartaba adalin Sarkin kargi ya bama Gimbiya Laila..!
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ina Lailan..!
Kanta na kasa ta numamai Dakin Dake kallonsa tace"Tana ciki Ranka ya Dade..!
Tafada Cikin biyayya daman ai Uwargiyan nata ne ta sakata da ya Shigo ta tsaidashi da Gaisuwan da zataji hakan ita kuma sai ta Shirya to hakan ce ta Faru tana jin mganar marliya ta Mike Jikinta na rawa ta Kwabe alkyabban Dake jikinta Tayi wanka yanzu bada dadewa ba ta sauya kaya Kwallin ta Farara Zirara sannan ta Dankwali Turaren ta shafe shi a hannunta na Hagu,Kafin ta Tattara komai ta maida Cikin ledan ta Bude makeken Wardrope din ta Tura Cikin kayanta.
A Jikin gadonta ta Tsaya bayan ta maida akkyabban nata ta juya baya asaitin Kofar shigowa bata Dadewa da Tsayuwa ba taji Knooking dinsa Lokaci Daya da shigowa Hajiya Zaliha ta Fadamata kada ta bari yayi mata sallama zai kira aminci kuma hakan zai iya bata aikinsu dataji Shigowarsa ta Bayyana yadda zasu hada Ido Cikin Ido alokaci Daya.
Ya turo kofar da Karamar sallamarsa wacce bata kaiga Cika ba Laila tayi Saurin Juyowa Lokaci Daya tana Yaye Hular alkayyaban Dake kanta Lokaci Daya Tana kallon Sulaiman din wanda suka Hada ido Hudu alokaci Daya gabansa yayanke ya Fadi Kamar acikin magaji ko Shirin wasan Hausa Yaga Laila Tsaye tana mai Mirmishi kamar yaaga wata hallita mai Daraja da Kima awajensa haka yaji Hatta Ledan hannunsa sai da ta subuce Kamar wani Gaula haka ya Washe mata Fararan Hakoransa yana Jifanta da Mirmishin Datake jifansa.
Ganin haka yasa ta fara takowa gabansa cikin Takunta na Takama da Isa Tana zuwa gabansa ta kuresa da Kallon Kauna da soyayya da Muradi mai Girma shima kallonta yake kamar an mai gafara yana ji in ya Daina ganinta kamar zai iya Mutuwa in ta Mtsa Daga gabansa.
Cikin Laushin Murya tace.
"SARAKINA.!
kamar tana Sarrafa Bakin nashi haka yaji yace
"LAILA TA.."
jin haka yasa batayi wata wata ba ta Rungumesa Lokaci Daya tana Riko Hannunsa na Hagu ta Mulkemai Turaran Dake hannunta kamar Wani Abu ya Giftamai haka yaji acikin Kirjinsa Duk nan Duniya Lailace Duniyarsa ita yake ji kuma yake gani ba Gaddama shima ya Kamkameta Cikin Fitan Hayyaci yana Fadin"Lailata kada ki Rabu dani..In kika barni zan iya Mutuwa..!
Laila Dadi kamar zai kasheta tana kamkame da hannunsa tana kara Gogamai Turaran nan tana Fadin"Bazan taba barinka ba Har Abada Sarakina..Indai zaka Rika jin mganata kana bin Duk abunda nace..!
DaSauri ya Dagota Daga Jikinsa bata ankaraba ya Zube agabanta yana Fadin"Ki isar da Umarninki..Ni Sulaiman kamar bawanki ne unarninki kadai nake jira..!
Tana Kayattacen Mirmishi ta Dagosa tana Fadin"Ka Ciyar dani Daga hanunka mai albarka..!
Jikinsa na rawa ya Dauko Ledan da yar akasa Gabadayanta da Ledan da komai ya Hada ya Dauka sai saman Gadon suka yada Zango
Akan Cinyarsa ya zaunar da ita yana Cire Salan salan kaza yana bata baki sai da ta Koshi ya Dauramata da madara kana itama ta Shiga basa yana ci yana kallonta kamar acikin kallonta me zai samu Sukuni Zuciyarsa Zafi take yana ji ajikinsa kamar in ya Daina ganinta ko Dariya Mutuwa zai yi yana jin inhar ya bata mata kamar zai Sare naman Jikinsa ne Bin Umarninta kamar shine abu mafi Salama da zai yi awannan Duniyan
Kamar Rakumi da alaqa ba Kunya ba Komai Laila ta Tube Zingir agaban Sulaiman shima tasakashi ya Tube Zindir agabanta wanda inda yana Cikin Hayyacinsa bata isa taga Saraki Cikim yanayin da Sunaira kadai tataba ganinsa haka ba,
Laila ita tagudanar da wasan ba Sallah ba Salati ba addu"a ba Komai suka Fara sarrafa juna Sulaiman ya Zama Duk abunda Laaila tace kafin ma tace yayi mata sai da tafiya tayi tafiya ta Raina kanta Sulaiman baya Cikin Hayyacinsa shiyasa ya shiga Laila yadda tazomai budurwace sai dai Budurcin nata ya samu Rauni yasa ta Jigata ammh ba yadda Kuke Tsammani ba.
Saduwa da ita kamar Cikashe makarim aikin Bokansu ne Shiyasa alokacin da Maniyinta ya Hade da maniyinta sai da Sunaima taji acikin Jikinta lokacin ta gama karatun alqur"ani kenan tayi addu"a ta kwanta kafin barci ya kwasheta taji gabanta yayanke ya Fadi da sai da ta Furta"
Hasbunallahi wani"imal wakeel..!
Lokacin datafadi haka Sihirin Dazai yi aiki,Tsakaninta da Sulaiman ya Kuskure ita kadai ce aduniyar nan Laila bazata iya Mallaka ba sannan in tana gaban Sulaimam Laila bata isa ta Mulkesa ba Ita din kamar Makullin Warwaren matsalansa ne ita din kamar Zanen KADDARANSA NE...!


*Kuyi hakuri ku kara Hakuri Sabgogi ne suka min yawa..Afuwan..!*


*Janafty*
















MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now