11

691 90 20
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

_Gabadaya Shafin yau Sadaukarwa ne gareku Aminiyata Aisha alto(Sisinah) Tare dake D'iyata Rahma Ladingo Diyar kwarai irin albarka Tabbas bani da bakin Mika muku godiyata sai dai nayi amfani da wannan Damar wajen Muku addu"an gamawa da Duniya lafiya Ni nawa rubutun ne kawai Hidiman Labarin da yadasa zuwa inda ya dace wannan Ragamar duka kun Daukemin ita Nagode kwarai da karamcinku Allahu yabar zumunci Ameen_

*Page 11*

Har awajen aiki yau an Fahimci Sunaima bata cikin Walwalarta har sai da abokiyar aikinta Aneesa ta Tambayeta ko Lafiya duk da ba wani Alaqa ce mai karfi a Tsakaninsu ba sai dai tafi Dan Sakewa kadan da Aneesa akan Sauran abokan aikin nata Domin aikinsu yafi Fadowa rana Daya da Aneesan kuma sun fi zama a maternity.
Kowa yasan Halinta da kamewa Daga Shiga Harkan jama"a shiyasa ba wanda ke shige mata banda gaisuwan Mutumci,Ko auranta kowa ya sani Saboda daman ko bata fada ba,Abun Duniya baya Taba Boyuwa kowa yasan ta auri Sulaiman kargi Mijin kanwarta mai rasuwa,ba wanda ya Tusa kansa Tunda ko Tarewar nata bata Fadama kowa ba Shiyasa ba wanda ya Damu da Tusa kansa Inda ba'a Kirasu ba ba wanda ya Damu da ita Tunda bata Bukatar haka ko Lambobinsu bata  kowa take dashi ba Sunaima kamewarta tayi yawan da bata Doguwar Mu"amala da Mutum komai Dadewarsu tare da mutum kuwa..
Duk da Aneesan tasan bazata Fada mata ba sai da ta tambayeta sai tace ba komai kanta ke ciwo ta mata sannu Harda kawo mata panadol tace tasha ta amsatana mata Godiya gabadaya tsausayin yaran yaki barin Ranta barin ma Karamar Wafiyya data fi Sabawa da Babanta gabadaya ta Tsaya Waje Daya akan in ta koma Gida ta Je ta samu Sulaiman da mganar tana Tunanin kamar baisan abubuwan Dake Faruwa bane.
Da wannan Shawaran ta tsaya sai kuma ta fara Tunanin yadda zata Dauko su Wasim Daga makaranta karfe Biyu take tashi aiki su kuma sai 3:30pm na rana suke tashi bata so ta koma Gidanan ta sake Fitowa kuma batasan taje gida Saboda kada Inna ta ga kamar batajin mganarta Ba,Har ta yanke shawaran Kiran Ahmad tace ya Daukosa Daga makaranta yakai mata Gida ita sai ta koma Gida in tatashi aiki sai ta fasa Sanin Surutunsa zai Fadama Inna kuma Zatayi wani Tunani ita kuma bata so Afara Zaton wani abu na Faruwa Tun yanzu da haka sai ta yanke shawaran Jira Har Lokacin tashin nasu sai ta Biya ta Daukosu su koma gida.
Haka kuwa akayi a acikin Asibitin ta zauna har zuwa Lokacin kafin ta Samu Tashar adaidaita zuwa makarantar nasu ta Daukosu Domin kamar yadda tayi Hasashene ba Sani ba Dalilinsa.
Koda suka dawo gidan Yar Mulkin ta ga dama tabada Umarnin Bude Kitchen din har an Dafa Lonching magajiya ce kadai ta mata sannu da zuwa ta karbi Lunch box din yaran zuwa Kitchen domin ta wanke su kuma Sunaima ta jasu Dakinta ta Cire musu kayan makaranta ko hutawa batayi ba sai da tayi musu wanka Lokacin Magajiya ta kawo musu abincu Jallop din Shimkafa da Miya da Nama nata dana yaran Ta mata Sannu da aiki..
Ita ta zauna ta rika basu abincin abaki Har suka Koshi bayan sun gama ta Tattara wajen ta Kwashi kayan makarantarsu ta fita Chan ta bayan Kitchen inda aka Saka injimin wanki nan mai wanki ke zuwa yana wankewa sai ya tafi dasu ya goge kayan yara na makaranta da Sauran abunda ba"a rasa ba ita ke Dawaniyan Wankewa Ranar ma ita ta wanke Tas da kayan Uniform dinta itama ta wankesu duk da wajen kala Uku Gareta Saboda Chanji.
Bata tsaya bi ta kan kowa agidan ba bata ga Laila ba ballatana Sulaiman sai duk a Tunaninta ya tafi wajen aiki ne Dakinta ta koma ta rika jan Hankalin yaran har suka saki suna wasansu Sai ta koma gefe kawai tayi Shuru Tana Tunanun abunda ya Faru jiya wanda ya kasa barin Ranta.
Abunda bata sani ba Kamar Jiya ne Laila bata bar Sulaiman ya Fita ba Duk da suna ganawa ta Biyu da kanfanin Dasuki Ventures.
Lokacin da Saifullahi ya isa kamfani Duk a azatonsa Sulaiman ya iso saboda yasan baya african Time kuma baya da Dabi"ar saba alkawari.
Shiyasa Office dinsa ya wuce kai Tsaye yana karisa wani aiki kafin su kariso bai Farga da Sulaiman bai zo ba sai da Bakin suka iso wannan karon a Hall meeting dinsu zasu yi Zaman yasa bayan ya karbesu abun ya bashi mamaki bai ga Sulaiman ba Office dinsa yaje tun kafin ya shiga Sakatariyarsa ta Fadamasa yau ma Yallabai bai zo Office ba yau sai ya fara Tunanin ba Lafiya yasan Waye Sulaiman da yadda yake bama wannan aikin Muhimmamci yadda yake aiki Tukuri bazaka taba cewa Kamfanin na Mahaifinsa bane sai ka Zata shima kamar Sauran ma"ikatane neman Halalinsa yake.
Kiran wayarsa ya farayi duk da zai iya Attending din Bakin nasu ammh sun Rika sun saba duk wani Kasuwancinsu da kananun Ma"aikatu da Sauran Cinikayarsu tare suke Gudanar dashi da Sulaiman Su kansu sai da suka Tambayesa yasan Lafiya Lafiya bazai Saba wannan alkawarin ba.
Saida yamai kira yafi Goma bai Dauka ba sai ya Kira Sani Direba sai dai ya Shiga Dimuwa da Bayanin da Sani kemai bai ma Tsaya Fahimtarsa ba ganin kamar Sanin yana mai Bayanin da ba haka bane,Sai ya kashe Wayarsa.
Sai ya kara Kiran Wayar Sulaiman wannan karon an Dauka Cikin Sauri yace"Haba Kargi kasan fa yau muna da Appoitment da Kamfanin Dasuki Ventures har sun iso shuru baka zo ba..Meke Faruwa ne..?
Sai dai maimakon yaji Muryan Sulaiman kamar yadda suka saba sai yaji Muryan mace Cikin gadara Tana Fadin"Ni na hana sa Fita aiki yau..!
Cikin mamaki Saifullahi ya Daga wayar yana kara ganin Lambar Daya Kira ko dai ya saba lamba ne sai ya kara Tabbatar da Tabbas Lambar Sulaiman ya Kira wanda yayi Saving da Kargi.
Cikin mamaki ya maida wayar kunnensa yana Fadin"Wacece ke..!?
Juya ido Tayi ta Juya tana kallon Sulaiman Dake gefenta yana kallonta Kamar wanda ya warke makanta kafin tace'"Laila nake..Amaryan Sulaiman Kargi..!
Saifullahi yace"Oh Amarya ce.?don Allah kiyi hakuri ki sakesa yazo yanzu..Wannan Tattaunarwar tana da Muhimmanci shima ya sani..!
Yafada da dan sigan Zoyala Domin shi azatonsa wasa take yi sai yaji tace"Ai tun dazu ya shirya yana son zuwa na Hanasa..bazai Sabu ba Yau kwana na Biyu agidansa ya fara Fita yana Barina Ina Hutun Amarcin da kowani Ango yake yi ma Amaryansa ni Shikenan kamar mara gata bazai min ba Daga kawoni sai ya Fara Fita aiki To na Hana na kuma Fadamai sai yayimin Hutun Wata Daya kafin na barsa ya Fara Fita..!
Saifullahi mamaki ya kamasa Cikin Dan kara Son Fahimtar wani abu yace"Da dai kinyi hakuri...Yanayin aikin namu ne kuma kada ki manta Shine Shugaban wannan kamfanin..!
Laila tace"Ai ba kwadago yake yi a kamfanin ba..Kamfanin Mahaifinsa ne ko Shekara yayi bai leka ba Damuwa Saboda haka kayi duk abunda zai iya yi awajen bazai fara zuwa aiki ba sai nan da wata Daya..!
Saifullahi mamaki ya gama Sandarar dashi yaushe Laila ta fara samun Daman Sulaiman bai Taba ganin Mace taja Ragamansa ba Tsayayyan Namiji ne kuma a kalamanta ba Tauttasawa sam ballatana yace Soyayyace tasa haka Cikin dan kamewarsa yace"Shi Sulaiman din kuma ya amince sai bayan Wata Daya zai dawo Office..?
Karkace kai Tayi tana kallon Sulaiman Daya yake ta kallonta Tun dazu tace"Au baka yarda ba..?Habibina Fadamai kila ya yarda dakai..!
Ta fada tana Hangamai Wayar a kunnensa Saifullahi mamaki ya Cikasa Cikin son Tabbatarwa yace"Sulaiman...!
Sulaiman yaji Zuciyarsa tayi mai Nauyi yana so yacemai yana son Zuwa ammh bazai iya Saba Umarninta ba yasa yace"Saifullahi ka Kula da komai don Allah..!
Cikin karyen Murya yayi mganar wanda Tun bayan Lokacin Da Sunaira ta rasu bai taba jin Sulaiman cikin wannan rauninba sai yau dayasa ya kasa mgana Illah kai daya gyada kawai ya yanke Wayar acikin Ransa yana Tunanin abubuwa na Faruwa ba Daidai ba.
A lokacin shi ya Tattauna da bakin bayan ya Sanar musu wani Uzuri ya rike Mrs Sulaiman Bazai samun Daman zuwa ba basu Damu ba,Sanin shima ai Saifullahi yasan abunda yakeyi kuma Tun Farkon Yarjejeniyar dashi aka Fara komai.
Bayan sun gama Tattaunawar basu Tsaida matsaya ba sai a zama na Uku suka Rabu Cikij jin Dadin hadin kan da wannan Kamfanin ta A.S kargi ta basu Saifullahi Duk ya Damu da Rashin Sulaiman sun saba Gudanar da komai Tare yasa gabadaya yaji sa Ba Daidai ya Fara Tunanin me ya Faru da Sulaiman bayan Rabuwarsu Ranar asabar Tabbas wani abu ya Faru ko yana kan Faruwa yaso ya Dauko Fayel din Tattaunawarsu yaje gidan Sulaiman yaga abunda ke faruwa su kuma Duba Abun atare sai dsi ya kasa Tafiya yabar Kamfanin ba kowa ba Sulaiman bashi sai ya bari sai ya tashi aiki zai Biya Gidan yagani.
To bai tashi aiki da Wuri ba sai Dare Gida ya wuce kawai ammh abun na Ransa da Safe kuma yaso ya Fara Biyowa ta nan sai aka Kirasa kan wasu sun zo nan kamfani suna son ganin sa ko shi ko Mrs Sulaiman yasa ya bar komai ya tafi koda yaje Mutane Daga wani karamin kamfani suna Bukatar Su hada dasu wajen Farfado nasu Ma"aikatan wannan ai ba mganarsa shi kadai bane Dole yaga Sulaiman su Tattauna.
Aranar Daya tashi Daga aiki Gidan ya Sauka sai dai Bai ga Sulaiman ba Sunaima kuma bata gida Ranar aikin Rana Tayi Glow slow ya riketa bata Dawo da wuri ba,yan aiki kadai ya gani suna Hiduma afalo Sulaiman da Laaila suna Sama koda yace ayi mai mgana da Sulaiman Sai ya samu Sakon wai Hajiya Laila ta hana su Haura sama indai ba ita ta Sauko da kanta ba Saifullahi ya shiga mamaki Sosai ya kuma kara Tabbatar ma da kansa wani abu na Faruwa ya Tambayi Sunaima Magajiya ta Fadamai Tana wajen aiki yaga su Wasim da Sunaima ta bar ma Magajiya Ahalin kula dasu Karfe Biyu tafita wajen aiki,Bata da Zabi Ahmad ta Kira yaje ya Dauko mata su zuwa Gida ya Damkama mgajiya,Bata da Mafita ne taso ya kawo mata su asibitin ne sai dai Doka ne yara bashi da kyau ka Rika zuwa dasu asibitin sai su samu wata Cutar yasa kafin ta Fita tabarma Magajiya da itace kadai Daman zata Kula dasu bayan bata nan.
Saifullahi ya tafi da Tarin mamaki da neman karin bayani ya Kira wayar Sulaiman har ya gaji ba"a Daga Kiran ba bai ga Sunaima kuma yaso ya ganta Kila ita in tayimai bayani zai iya Fahimtar abunda ke Faruwa.
Aranar da Sunaima ta Dawo Daga Wajen aiki ta yanke Shawaran yi ma Sulaiman mgana Domin bata Sauya Zani ba Kullum sai dai ta Siyamusu Biscuit da Juice ta saka musu Cikin Lunch Box,sannan basu kara Saka Sulaiman a ido ba Shi din ma in Laila na gabansa mantawa yake da kowa Cikin Harda karan kansa.
Sai da ta bari dadaddare bayan tayi Sallar Isha"i ta bama su Wasim tea sun sha ta musu wanka ta tayasa sun yi Homework kana ta Lallabasu suka kwanta kana ta Fito Daga Dakinta Cikin Shigarta na bakar Abaya Da Farin Hijabinta iya gwiwanta.
Batare da Shawara da kowa ba ta Haura sama Shashen Laila sai dai Da Samira taci karo ita take Fadamata suna Shashen Yallabai mamakin yadda aka narka Dukiya afalon take kafin ta fice zuwa Dakin Sulaiman Wanda bata taba Hawowa sama Ba Tunda Aka kawota gidan a matsayin matar gidan.
Daga Falon ta Dinga Sallama taji Shuru ammh ko"ina kal kal ashare Cikin Tabta ko"ina na tashin kamshi,har ta yanke Shawaran juyawa sai ga Laila ta Fito Daga Bedroom tana Sanye Cikin Fitattun Riga da wando sun kamata kanta ba ko Dankwali ta bazo sumar kanta baya Kallo kallo sukayi ma Juna ita da Sunaima kafin ta Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta Dora Kafa Daya kan Daya tana kallon Sunaima a yangace kafin tace"Lafiya..?bana son Damu ina Hutawa da Mijina..!
Sunaima ta kauda kanta kafin tace"Wajen Sulaiman nazo..Abban su Wasim..!
Laila tayi wani kayattacen Mirmishi kafin tace"MIJIN KANWARKI...!
Sunaima ta kalleta ido Cikin ido kafin Tace"Eh kuma KADDARATA ba..!
Laila ta Dago zatayi mgana Sulaiman ya Fito Daga Cikin Bedroom kamar wanda aka Jeho yana Sanye da Jallabiya Fara yana Fitowa Laila ta Dago Tana kallonsa Kafin tace"Meyasa ka Fito Habibi..?Wacece ita da Zata ganka..?ka koma bazata ganka ba..itama Lokacin dataci nata armarcin ban Takura mata ba..!.
Kamar Uwarsa haka ya juya zai koma Sunaima batabi ta kan Laila ba ta taka gabansa Tana kiran sunansa
"Abban wasim..!
Cak ya tsaya cikin jin yadda Muryanta ke Shiga Ko"ina na Jikinsa Juyowa yayi yana kallonta da lumsassun Idanuwansa Laila ta mike Cikin Daga Murya tana Fadin"Ka koma ciki nace Habibi..!
Sulaiman ya kalleta bai yi mgana ba Sunaima ta kalli Laila Cikin Dakewarta Tace"Bazai koma ba sai ya Saurareni malama..!
Ga mamakinta Sulaiman ya kalleta yace"Ki kyaleta tayi mgana Lailata..Ina so naji abunda tazo dashi ne..!
Laila sai ta Sandare Me hakan ke nufi..?Sunaima ba mallakanta bace kenan bata iya Juyata kamar yadda ta Fara  Juya kowa Dake karkashin Sulaimam.
Mamaki bai gama kamata ba Sai da Sulaiman ya Tsura ma Sunaima ido Lokaci Daya yace"Ina jin ki Sunaima..!
Sunaima ta Rausayar Dakai kafin tace"Kana sane da cewa Sani Baya zuwa kai yara makaranta..!?
Cikin Kallonta Ido na ganin Ido yace"wasu yaran..!?
Sunaima taji gwiwanta yayi sanyi Idanuwanta suka kawo Ruwa Cikin Zamewar Tunani tace"Wasim da Wafiyya..!
Sai alokacin ya Tuna da su Cikin son karin bayani yace"Meyasa..?
Sunaima tace"Bansani ba...Sannan ba"a Bude Kitchen da safe ballatana Magajiya ta Dafa musu Luch din da zasu tafi dashi..nazo na Fadamaka ne in ka sani to ya yakamata kasan me ake Ciki in kuma baka sani ba ka sani..Ka kuma gayama matarka kada ta Saka ya"yanka Cikin Tsarinta Yara ne kanana da basusan komai ba..!
Lokacin Datake mganar Bakimciki ne ya Rufesa kamar yayi Bindiga haka yake ji sai dai yana Juyawa ya kalli Laila sai komai ya Tsaya mai Cak ya kasa mgana Laila kuwa na Gefe tana Mirmishin keta.
Kallon Sunaima tayi kafin tace"Kin gama..?
Sunaima ta kalleta Idanuwanta sun Tara Hawaye kafin tace"Eh na gama..Me kike shirin aikatawa..?zaki Raba Uba da ya"yansa..?
Laila tace"Baki ga alama ba..? Ai yanzu Habibina ko Hajiya Zabba"u tazo gabansa sai da Izinina zai Kalleta..!
Sunaima ta Fara tsorata da Lamarin Laila Cikin Mamakinta tace"Kinsan me kika aikata..?
Laila ta Fara taku zuwa gaban Sulaiman ta Rikess Lokaci Daya tana Dora kanta saman kafadansa tace"Nasani mana..Nasha Wahalan Soyayyar Sulaiman yanzu dana Samesa ai sai abarmin shi kadai ko ba Haka ba Habibina..!?
Kai ya gyada mata kamar wani Wawa Kuka ya kwacema Sunaima Domin alokacin ta rasa Karfin Gwiwanta Cikin kuka tace"To baki isa ba Laila..Zan iya Yin shuru a komai na Gidan nan banda yin shuru kan Raba Sulaiman da ya"yan yar"uwata..In har ke Juranki Sammako ni Sunaima Abdu Datti Atafe na kwana ina Daidai da Duk abunda kika Shirya nayi miki alkawarin indai ina Gidan nan bazaki samu yadda kike so ba Laila..Sai na Zame miki Kaddara acikin wannan Muguwar Hanyar da kika Dauka...!
Daga haka ta juya zata Fita karaf Sulaiman ya Riko hannunta Cikin Zafin Nama Laila ta kallesa Ta kalli Hannunsu Dake Hade Kafin ta ce wani abu Sunaima ta Juyo Idanuwanta sun shige aaboda kuka Cikin Bakin ciki da yadda yake jin Tafasa acikin Ransa yace.
"Kiyi hakuri....!
Yafada yana hada Labbansa Waje Daya Gaban Sunaima yayi Rugu Rugu alokacin wani Abu ya fito Daga Idon Sulaiman ya shiga Idanuwanta wanda ya Gauraye a cikin ajikinta lokaci Daya batare data sani ba.
Laila ta Kwace hannun Sulaiman Tana Fadin"Ki Fita daganan...Ki kuma kula Domin duk wanda yace zai sha Gabana Karshensa Faduwa ne..!
Sunaima bata kara cewa komai ba Illah wani kayattacen Mirmishin Dayafi kuka Ciwo tayi ma Laila kafin ta Fice tanajin Jikinta na kassara da yanayin kallon Sulaiman alokacin Sunaima bata sani ba Kaddaranta ta Fara Domin awannan lokacin Soyayyar Sulaiman tayi mata Shigar da bata taba Tsammani ba
Dakinta ta koma ta Fada Bisa gado Tana ta kuka,kukan Dake Fitowa Daga karkarshin Ranta wazata fadama Damuwarta ya bata Shawara..?bata da kawa ballatana wata abokiyar Shawara Sunaira ce kuma bata agidan Duniyanan ballatana su Tattauna.
Komawa tayi tana toshe bakinta kada kukanta ya bayyana ya Tada yaran Daga Barci.

*****

Acikin wani kyakyawan Lambu mai Cike da korayen ganye shar shar dasu Ta Hango wata mata zaune kan wani kututuran Icce gabanta wani karamim Koramana ne tana ta Daukam kananun Fararan Duwatsun Dake wajen tana Jefawa cikin Ruwan Wanda yake Fallasomata har saman Fuskarta Tana Sanye da Fararan kaya Tun daga sama har kasanta ko Tafin Hannunta ba"a gani.
Sunaima ta samu kanta Cikin Lambun Tana Faman waige waige Da kayan Jikinta Ta ga kanta acikin wannan kayattacen Lambu ba gida gaba ba gida baya sai ta fara tafiya Kafarta ba Takalmi tana waigen bayanta da gabanta.
Acikin hakane ta Hango bayan Sunaira Bata iya ganin Fuskarta ba yasa ta fara takawa zuwa Wajenta Daidai tana zuwa Daidai tana Mikewa tajuyo suna Fuskarta juna ido Cikin Ido da wani Rawan baki dana Jiki tace.
"SUNAIRA...!
lokaci daya ta Nufeta zata Rumgumeta da Sauri ta kauce Daga Rikon Cikin mamaki Sunaima ke kallon yar"uwanta kafin tace"Meyasa kika Hanani Rumgumeki yar"uwata..?
Sunaira takalleta da kyalin Idanuwanta cikin Hasken Farin watan Daya mamaye wajen.
Tace cikin amon muryan ta data Sauya"meyasa zan yadda ki Rikeni SUNAIMA..?
Alhalin bayan Barina Duniya baki Rike Amanar yan"uwantakan mu ba..Baki yadda ni din yar"uwanki bace..!
Da sauri Sunaima tace"Meyasa kikace haka..!ina da yar"uwan data wuceki ne Duk Fadin Duniya..?
Sunaira ta yi Kayattacen Mirmishi Kafin tace" In kin Daukeni yar"uwanki ta Jini meyasa kika ki Rumgumar KADDARANKI...?
SULAIMAN ZAHIRINKI ne Sunaima Shine Duniyarki ayanzu...!
Tafada kafin ta juya mata baya tana Fadin"Ya"yan dana Haifa Duka mallakin ki ne Sunaima...Sulaiman Kaddaranki ce ni aronta na karban miki gashi kuma na Dawo miki dashi ammh baki Rikesa Dakyau ba...To ina so ki sani Sulaiman na Cikin Wani Hali kuma ke kadaice Aduniyarsa da zaki iya Fito dashi daga wannan Halin ke kadaice Duniyarsa yanzu..Kece Kaddaransa..Ki karbesa Hannu Bibbiyu ki gyara Duniyarsa in kina so na kara zuwa Har ki kirani yar"uwanki na amsa..!
Tana gama Fadin haka ta bace bat awajen Sunaima ta Fara Waige waige tana Kiran sunan Sunaira Kamar Zautattaciya.

"Sunaira...Sunaira...Sunaira....!

*****

Afirgice ta Farka kamar Wacce Tayi Gudun Famfalaki gabadaya ta Hada Zufa Har Tsiyaya take Dakin Take kallo Ganin haske ya gauraye ko"ina sannan ta koma tana kallon kanta Kayan Jikinta ne da su taga Sunaira Tun sanda ta Fara kukan nane barci ya kwasheta bata sani ba Shine tayi mafarkin Taga Sunaira..
Jikinta na rawa ta mike Jiri ma Take gani Saboda kanta gabadaya ya Daure Zufa ta kara yankomata Ta sama da kasa ta yarfe,kanta ta Dafe tana Fadin"Innalillahi Sunaira...Sunaira..!
Take Fadi tana kokarin Tuna abubuwan da suka wakana acikin Mafarkinta ta kasa ma Dora mganar akan Mizani Jikinta taja ta Shige Tiolet wanka tayo gabadaya kasala ya Rufeta Alwala ta Dauro Saboda barcin kwata kwata ya Fita Daga Idanuwanta.
Darduma ta Shimfida bayan ta Saka wata Doguwar Rigar barci da katon Hijabinta na Sallah ta Fara sallar Nafila Raka"a shida tayi kana ta Zauna ta Fara karatun Qur"ani sai da asuba ta kawo Jiki Sunaima na Zaune tana karatun Qur"ani tana kuka Gabadaya lamarin ya kasa barin Ranta tana Cikin Wani Halin Datake Bukatar matallati Wazata Tunkara Awannan yanayin Datake ciki bata Tuna Kowa ba awannan yanayin ba Sai INNA..!
UWA domin awannan gabar Uwace kadai Zata iya Tsayawa ta Fahimceta har tatayata samun ma kanta Mafita da wannan Gudurin ta Tashi da Safe sai karfe Biyu take da zuwa Wajen aiki bata Sauya zani ba kamar Kullum ba yau ma ita takai su makaranta Yau ma Din lemo ta siya musu da Biscuit Dakyar ta Lallashi Wasim ya Fara Rigiman kwai zai ci to har alokacin Laila bata bada damar Bude Kitchen din da Wuri ba kamar yadda aka saba ba.
Daman da Shirinta ta Fita Daga makarantar su Wasim Gida ta wuce a kofar gidan taci karo da Baba ya Fito da Mashin zai tafi Wajen aiki Ahmad ma ya Shirya zai tafi makaranta yana Jiran Baba ya Daukesa ganinta da Safe haka Fuska duk ta kode yasa Baba ya kalleta kafin yace"Sunaima Lafiya..!?
Tana Duke tace"Lafiyalau Baba...!
Bai matsanta mata da Tambaya ba Ahmad ne ya isheta da Tadinsa bata Biyemai ba ta Shige Cikin Gida.
Yanayin yadda Inna taga Sunaima sai jikinta ya bata ba Lafiya da Sauri ta Saki Sharan Tsakar gidan datake ta Bi bayan Sunaima data Fada Dakinta.
Tana Shiga ta ganta Tsaye ko zama batayi ba Cikin Damuwa Inna Tace"Lafiya Sunaima..!?
Sai kawai Sunaima ta fashe da kuka ta isa ga Inna ta Rumgumeta Tana Fadin"Inna ya zan yi..?
Wannan Kaddaran ta auran Mijin kanwata tamin girman da bazan iya Dauka ba Inna..ki bani Shawara ya zanyi..!
Tafada Cikin kuka Inna batace komai ba illah Bayanta data Dafa Tana Lallashinta Har ta Tsagaita Kafin taja ta zaunar da ita saman Kujera kwara Daya Dake Cikin Dakin Waje ta Fita Taje Madafi ta Dibo mata ruwan Randa mai Sanyi ta koma dakin ta bata Tana Fadin"Cire Hijabin ki sha ki Samu natsuwa...!
Ba musu ta Cire Hijabin Jikinta Riga da Sikat din Atamfar dake jikinta ta bayyana ruwan ta karba ta kafa kai tasha da yawa kafin ta mikama Inna ta karba Tana Fadin"Kin samu natsuwa yanzu..?
Kai ta gyada mata Kafin ta Sauke Numfashi Gefenta Inna ta Zauna Lokaci Daya tana ijiye kofin Hannunta Cikin Tattara natsuwarta ta maida kanta Tace"Meke Faruwa ne Sunaima...?







*Janafty*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now