13

587 84 8
                                    

*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*Page 13*

Kamar yadda Sunaima tayi alkawari karfe Hudu da yan Mintuna ta Dauki Excuse kafin ta bar wajen aiki zuwa Gida Koda taje inna ce kadai acikin Gidan sai Wafiyya daketa sha"aninta acikin gidan tana ta Wasanta Wasim baya nan Ahmad ya tafi dashi Shagon Dayake Koyon aiki hannu,Baba kuma Ya fita Tun dazu.
Farincikin Inna ya kasa Boyuwa sanda Sunaima ke fadamata ta amince Zata taimaki Sulaiman ammh Saboda ya"yansa ya"yan yar"uwanta ammh ta Boye ma Inna Kudirinta na in ya Dawo Cikin Hayyacinsa sai ya Saketa.
Inna Bakinta yaki Rufuwa ta rike hannun Sunaima tana Fadin"Allah yayi miki albarka..Allah ya baki aljannah..!
Sunaima ta amsa da Ameen kafin ta Kalli Inna Tana Fadin"Na Fadama Abokinsa Saifullahi komai..Domin yayi ta zuwa nema na yau kafin na tafi Wajen aiki na Biya chan ma"aikatansu munyi mgana..!
Nan ta shiga Fadama Inna Duka abunda suka Tattauna Inna ta jinjina kai kafin tace"Ba mtsala Saifullahi ya wuce amini Dan"uwane ga Sulaiman ya kamata yasan komai shima..Sai dai naji Dadi da kika Hanasa Fadama iyayen Sulaiman na Fada muku Fadan ba naku bane..Fadan na Cikin gida ne kuna Zaune in ta kwabe musu zasu nemo Hanyar gyara da kansu..Yanzu dai Gobe asabar zan je Zuntu na Samu kawu Jafaru nayi mai bayani Duk Abunda yace zan Sanar Dake..!
Sunaima tace"A goben zaki dawo Inna..?
Kai ta Kada Kafin tace"Bansani ba..Kinsan Tafiya Allah keda ita..In ta kama sai na kwana in ya Bukaci hakan sai na bari sai Jibi zan dawo..!
Sunaima ta jinjina kai kafin tace"Allah ya kaimu..ya mganar su Wasim Inna kin ji fa Baba nata Fada..?
Inna tace"Kada ki damu na gama da wannan Mtsalan da zarar na Dawo zan Kiraki a waya ki Hada kayansu Waje Daya..Ahmad zai zo ya Dauko mun su su zauna a waje na Har muga yadda Allah zai yi..!
Sunaima Tace"Kina ganin ba matsala..?
Inna Ta Dafa kafadarta Kafin tace"Kada ki damu..da yardan Allah babu Wata mtsala muna gayama Allah kuma bazamu Fasa ba..Kema kada ki Fasa duk da nasanki baki da Wasa..!
Jinjina kai kawai Sunaima tayi batace komai ba,bata yarda takai yammah ba Saboda Baba Karfe 5:30pm na Yammah ta Kira Ahmad tace ya Dawo mata da Wasim zasu tafi gida Ido na ganin Ido Ahmad ya Rakota ta Samu adaidaita zuwa gidan.
Kamar yadda ta Saba Daga ita Har yaran adaki suke Rayuwarsu haka suka Cigaba da gudanar da ita ko suna son Fita sai ta Hanasu,Sai dai ta Zauna dasu adaki tayi ta jan Ra"ayinsu da wasa abinci Magajiya ce ke Shigo musu Dashi shima aboye kada su Samira su gani su Fadama Laaila Domin tace duk wani abu da za"a Gudanar sai da saninta.
Washegari kamar yadda Inna tace Sammako Tayi zuwa Zuntu sun yi mgana da Sunaima da Safen kafin Tatafin,taje chan Babban gidansu Innda Yayenta suke zaune da iyalansu sai da ta Huta kana ta isa gidan kanwarta Tani suka gaisa Duk da kanwartane uwa Daya uba Daya bata gayamata komai ba tadai ce ta Rakata gidan Kawu Jafaru tana san ganinsa Koda sukaje baya nan ya tafi Wani aiki sai suka zauna wajen Goggo Indo mai Dakinsa suna ta Hira sai bayan La"asar ya dawo gidan yaji Dadi sosai na Ganin Inna,Tani ta koma Gida ita ta Dora sanwa..
Dakinsa dayake ganawa da Mutane suka Shiga Tunda Daman sun yi waya da ita da Safe tacemai Zata zo yau Wajensa akwai mganar Dake Tafe da ita.
Bayan gaisuwa da Tambayan yara Inna ta Tankwashe Kafa ta shiga Labartamai Duka abunda ke Tafe da ita kai yake ta Girgizawa kafin ya Dago yana kallon Inna yace"Wato Rukayya...Tabbas Surukin ki ya Hadu da Hatsabibiyar mace..Wannan Sihirin Kamar yadda kikayi Hashashe na mallaka ne..Kuma yana da karfi Sosai Makarin Sihirin an Hadashi da Siddabaru kuma an cikashe Shi wani abu Dake tare da Surukin naku sai dai bansan ko miye ba..!
Inna ta Jinjina kai tana Fadin"Tabbas Kawu..Domin Sunaima ta Tabbatar min da cewa in yana gabanta kamar D'a yana gaban Uwarsa ne.!
Kawu Jafaru yace"Ai Kamar Uwarsa tasa ce..Kamar bawa ne da Uwargijiyanta Duk duniya yanzu bayan ita bazai iya Bin Umarnin kowa ba...Sannan in ya kauce ma mganarta zai ji kamar zai mutu ne Shirin mai karfi ne..Sai dai kada ki Damu Rukayyah da yardan Allah Da kuma Ikonsa Munyi karatu mun kuma san acikin Alqur"ani akwai ayoyin Dake karya Sihiri zan yi mai wadandan addu"o"in acikin Ruwan Sama ki tafi Dashi sai kibama ita Sunaiman ta Tabbatar ta rika basa da Safe da yammah yana sha..Sannan mu Dake da addu"a Baza"a adauki Dogon Lokaci ba komai zai Daidaita Nima ta Bangareena zan Ta sakashi Cikin addu"o'ina Domin Neman masa waraka da Fita Daga Cikin wannan Infitila"in sannan in akwai yadda za"ayi Shima arika sakashi yana Ibada yana Kiran sunan Allah hakan ba karamin Taimakamai zai yi ba..!
Inna tace"Insha Allahu kawu nagode kwarai..!
Kai ya Girgiza kafin yace"Haba bakomai Rukayyah...Kawai dai Kinsan yadda Duniyan ta Sauya ne..Mutane ba Tsoron Allah..Don Allah ki Fadama yarinyar wajenki ta Dake da addu"a Domin sakacin mu kadan ke saka aci Galaba akanmu..Sihiri gaskiya ne Domin mu gasgasta haka anyi ma Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallalahu alaihiwasallam Kuma ya kamasa Kinga kenan kowa ma za"a iyamai Sihiri ya kamasa sai dai an Fadamana Ita addu"a makamin Muminice sannan Ita tana Sauya Kaddara Daga mara kyau zuwa mai kyau..!
Inna ta gyada kai Tana Fadin"Hakane kawu mungode Allah kara girma..Zan koma ne yau da nake so..!
Kawu Jafaru yace"A"a ki bari gobe da Safe yau da Daddare zam kamallah addu"o'in sai na baki ki Tafi dashi..Sannan akwai wasu addu"o'in da zan Rubuta sai ki bama Ita yar wajen naki Da ke matsayin matarsa yanzu ta Rika yi insha Allahu komai Zai Daidaita Da kadan kadan..!
Inna nata godiya kafin ta ijiyemai kudi yaki karba yace ta Dauki Kudinta yana Fadin"Rukayya ai kema Yatace..
Ni bana karban ko sisi Daga hannun Mutane Domin na Taimake su kan sanin da Allah ya bani..Tashi kije inna gama zan Aiko Miki kizo ki Dauka..!
Da haka suka Rabu Inna ta baro Gidansa Tana ta Godiya Gidan Tani ta koma ta kwana Da Safe ta shirya sai da ta Biya gidansu tayi sallama Dasu kafin ta Biya Gidan kawu Jafaru ta Dauki Sakon awata Farar Jakar Cike da Ruwan sama da yayi addu"an aciki Sun Rabu akan in ya kare ba wani Chanji Ta dawo sai ya Sake mata wani yana da Tabbacin in akayi sau uku Komai zai yi Daidai da yardan Allah..!
Da wannan Inna ta kamo Hanyar Kaduna Daga Zuntu da wuri ta iso Tana Dawowa ta Kira Sunaima ta Fadamata tazo gida Tana nemanta ta Dawo.
Haka kuwa akayi Daman Duk zaman Gidan ba Dadi ta Riga ta gama Hada su Wasim yan kayansu Da na makarantarsu da Lunch box dinsu da Schoolbag dinsu Magajiya kadai ta Fadama zata kaisu gidansu ne su kwana biyu kamar ko yaushe ta Hau adaidaita zuwa gidan yaran sai Murna suke Tunda tace musu Gidan Inna Zasu kwana.
Kamar yadda Kawu Jafaru yayi mata Bayani haka ta Juyema Sunaima wacce ta Kifta kananun Idanuwanta kafin tace"Ni kuma Inna..?tayaya zan iya basa har yasha..?kin san fa na Fadamiki bana ganinsu koda yaushe suna Sama shi da laila..!
Inna tace"Kada ki badani mana..Haka Sunai..Kamar ba mace ba ai kinsam Dubaran da zaki yi har ki samu nasaran basa..Kada ki manta Ta wannan Hanyar ne kadai zamu Taimake sa..!
Sunaima ta Jinjina kai ta kasa mgana Tunani take ta ina zata Fara..!
Inna dai sai kara mata karfin Gwiwa take bata yarda takai Dare ba ta Koma Gida bayan Inna ta bata addu"o'in da Kawu Jafaru ya Rubutu cikin Harshen ajami Da zata tafi Wafiyya ce kadai tayi Rigima ammh Inna na Goyata ta Lafe Wasin kuma Harda Bye bye yayi mata da zata tafi bai Damu ba sai Wasansa yake afilin Tsakar gidan ballatana daman Ta jido mai kayan Wasansa wanda zai Dauke mata Hankali gobe zata koma Aikin Dare gabadaya Satin na Dare zatayi Hankalinta ya kwanta Tunda yanzu Inna ta karbam mata Nauyin kula da su Wasim ita sai taji da Sauran yakin Dake gabanta.
Kamar yadda Inna tace bayan ta koma Gida ta Kira Saifullahi tafadamai komai yaji Dadi kwarai har Shima ya Fadamata yadda sukayi da Babansa na Zaria ammh yace duk da Haka shima zai je har gida  yamai Bayani Shima sai ya Tayasu da addu"a har yana Fadama Sunaima yau Abba ya Kirasa yana Tambayansa komai Lafiya kuma hakam bai rasa nasaba da Rashin jin Sulaiman Tun bayan auransa da Laila Tunda wayarsa bata Hannunsa tana Hannunta ko zaka Gaji da Kira sai taga Dama Zata Daga Kiran Duk da Abba bamai Takura bane ammh ka gaida mai gaisheka Lafiya dai Sulaiman bazai kwana Biyu bai Kirasa ba..
Ya Tabbatar ma da Sunaima bai Fadamai komai ba Sunaima tace Shikenan ita dai zata yi iya Kokarinta Saifullahi yace shima bazai kwanta ba Amana Ta hau kansa ga na Kula da kamfani ga Addu"an Allah ya kwato Sulaimam Daga hannun Daya Fada.
Da haka suka Rabu da juna ya Kudirar ma Ransa zai yi iya Kokarinsa Wajen Taimakama Sunaima Sulaiman ya Dawo Cikin Duniyarsa.
Dayake ba wanda yaga Dawowar Sunaima Magajiya da Mariya suna Kitchen su Samira kuma suna Shashen Laila Tunda ita sun tare a barayin Sulaiman din.
Ta shiga Dakinta ta adana Ruwan Addu"an a waje mai kyau yadda bazai Samu wani Tawaya ba, Tunaninta ya Fara kan yadda zata Fara gudanar da aikinta Batare da Laila ta Fahimci wani abu ba sai dai Duk iya Tunaninta ta kasa Domin ta tabbatar ma kanta sai dai in ta Bisa Chan kuma Laila na Tare dashi bazata iya yin komai ba agabanta.
Tana nan Zaune Daga inda Tayi Sallar mangariba bata Jirga ba,Har aka Kira Sallar Isha"i tatashi tayi Gabadaya sai taji kewar yaran ya kamata na Rashinsu Allah Sarki sabo Turken Wawa ba wanda ta saba dasu irin yaran Tana cikin addu"o'inta taji Kiran wayarta Tana Dubawa taga Ahmad ne tana Dauka taji Muryan Wasim yana kiran sunanta Wafiyya ma Tana Hadawa da gaurancinta Ran Sunaima yayi mata Dadi,Ahmad na Fadamata Suna ta Kiran sunanta Shine Baba yace akirata suji Muryanta To waya da yaran ne ma ya Sata Farinciki nan ta biye ma Shirmen yara na dan Lokaci har sai da Kudin Wayar Ahmad suka kare.
Ta mike tana Nannade Darduman kenan taji kamar Hayaniya Daga Falo mamaki ya kamata da Hijabin Jikinta ta Fita zuwa Falon Cikin mamakin Jin Tashin Muryan Namiji.
Ta shigo Falon Daidai Lokacin Daya Mike yana gyara Zaman wasu Takardu Dake hannunsa yana Fadin"Mr Sulaiman Amanar Dukiyarsa ya bani..Kuma dani dashi muke Gudanar da wannan Lissafin Duk Lokacin da hakan ya taso..Bai Taba Sama mana wani Thirth patner ba..Kinga kuwa ba yadda don kina matarsa kice dake zan yi mgana..!
Yafada kai Tsaye yana Karema Laila Kallo Ta Cikin Siririn Gilashin Dake manne a idonsa.
Habib Kenan shine Manajan Dake kula da gidan Madaran Sulaiman na S.A.KARGI FURA AND YOUGHOURT..!
Tun bude wajen shi ya Dauko ya Damkama amanar Komai a Hannunsa Habib Jajirtattace ne kuma mai Amna ne,Yasan abunda yake yi bai da Tsoro sannan a tsaye yake baya Daukan Reni Dan Zaria ne sai dai yanzu yana Zaune a kaduna shi da iyalansa Duk Dalilin Sulaiman.
Yazo Neman Sulaiman ne saboda baya Daukan wayarsa sannan akwai lissafin Watan Daya wuce basu Shigarba Daman Sulaiman din yakan zo ne wani Lokaci ko shi ya sameshi a Kamfaninsu,suyi komai su gama ya Kira Saifullahi shima bai sameshi ba sai ya yanke Shawaran bari yazo Gidan yana Tunanin Amarci ne Bai gama ci ba Tunda ai har Kargi yaje Daurin auran Sulaiman da Laila.
Sanda yazo yasha Zama kafin Laila ta Fito Domin da Farko Tace asallameshi ne Lokacin da Samira ke Fadamata Sulaiman yayi bako jin Sunansa da yarda Sulaiman yayi ne yasa ta Tambayeshi waye ya Fadamata jin Haka yasa tace bari ta Fita ta gansa.
Da farko ya zataama watace Domin bai Dauka matar gidan bane ganinta komayafi bata saka ba Sannan sai Daga baya ya gane bayaninta Tana kallon Cikin Idanuwansa Tana kokarin bashi Umarnin bazai ga Sulaiman ammh Itace Komai na Sulaiman zai iya mgana da ita.
Abun yabashi mamaki ya kuma Shiga Rudani kowa yasan Sulaiman ai ba Lusari bane yasan abunda yake yi Taya zai zauna Wata Sakarar mace na Juya sa macen ma wacce tazo Jiya Tabbas yaji Labarin an bama Sulaiman yayar matarsa bayan Rasuwar Matarsa ta Farko sai dai bata katarin ganinta ba Tunda bai cika zuwa Gidan ba nan ba koma yazo wani Lokacin iyakarsa Haraban Gidan sun gama mganarsu da Sulaiman ya kara gaba.
Shiyasa ya Mike ya Fadamata bazai Tattauna da ita ba tunda ya Lura kamar wannan karon Sulaiman din ya Fada Cikin hannun da bai kamata ba..
Laila Ranta ya baci Saboda agaban Hadimanta ne su Samira Dake Duke awajen Habib ya Kalleta ya gayamata Mgana kamar ita Laila Dake Juya Wanda Taga Dama Sulaiman Data maida shi kamar wani Danta sai abunda tacemai yake yi.
Laila irin jarabbabun matan ne masu Makalema Namiji suyi ta kwashemai albarkatun Jiki Sulaiman ko a baya Ba haka yake ba shi Saffa Saffa ne bai da Jaraba ta sosai haka balle Tunda ya Rasa Sunaira wannan Sha"awar ta fita Daga Ransa ammh Shigowar Laila Rayuwarsa yasa Komai ya Sauya ta maidaahi Sama da Kasa ne,Arana sai tanemesa kusan sau Uku fa Shidai gayinan ne ammh baisan Motsin Zuciyarsa ba in yana Tare da Laila yana jin kamar yagama Dacewa sai dai akan Ransa yana jin Tabbas Sulaiman ya sauya ba Haka ya kamata ya Zama ba..!
Laila ta kalli Habib Daga sama har kasa Shima ya kalleta kafin yace"Ki gayama Mr Sulaiman nazo ina nemansa..In kuma bazan gansa ba Fine zan Tafi..!
Cikin Gadara tace"Baka isa ka gansa ba..bari kaji na Fadamaka..Duk abunda na Zartar agidan nan koda Saninsa ko ba saninsa Daidai ne..!
Bai Damu ba ya Fara Tafiya yana Fadin"Yayi kyau..!
Laila tace"In ka Fita zan koreka Kuma na kawo wani wanda zai Rike mtsayinka..Kila Daga Lokacin zaka ga Ikon Laila..!
Cak ya Tsaya ya Juyo yana kallonta Sunaima da mamaki ya kamata ta kasa Motsi ganin kamar hankalinsu bai kawo kanta ba yasa batare da Shawara da kowa ba ta Fara Haura Stairs,Da sauri Sauri ba wanda ya Lura da ita Shashen Laila ta Leka ba Kowa sai Marliya ita ta Fadamata Sulaiman yana Dakinsa..
Da Sauri ta nufi chan Tana Shiga Falon Sulaiman Dake zaune akan Kujera kamar wani maraya yayi Saurin Mikewa yana kallonta gabansa ta Nufa tana kallonsa ganin yadda Cikin Sati Daya Duk yayi wani Firgai Firgai.
Cikin Sanyin Muryanta Tace"Ga wani chan yazo wajenka..Matarka zata Koresa kai kana nan zaume..Kai kace ta Fita ta gana dashi kai kuma kana Daki a zaune..?
Kallomta yake yi kamar zai yi kuka ba Zato taji ya Rike hannunta Cikin Wata Murya yace"Ina so na je..Habib ne ta Hanani Fita SUNAIMA...!
Yadda ya Kira sunan nata sai da Tsigar Jikinta tatashi ta Dago tana kallon Kwarmin Idanuwansa da Ruwa suka Taru shima kallonta yake gabadaya sai taji kamar Wani abu ya Ruftamata acikin Zuciyarta da gangar Jikinta.
Bata ma gama Tunanin Mafita ba Taji Sulaiman ya jawota Jikinsa akaron Farko ya Rumgumeta Rumgumar datazo mata da wani Bahagon yanayin da bata taba Riskan kanta ba sai yau Tunda Take wani Namiji bai Taba Rumgumeta ba sai yau Gabadaya Tunaninta ya Cak sanda Sulaiman ya manne kansa cikin Dogin Wuyanta yana Fadin"Ki taimakeni..Ya zan yi..?nasan abubuwa suna Faruwa ba Daidai ba..Bani da yadda zan iya in ina gabanta mantawa nake yi da kowa da komai..Ina so na Fita naje wajen aiki Duk ta hanani ni kuma bana iya mata gaddama ki Taimakeni Sumaina In kinsan abunda ke Damuna ki Fadamin in kuma kinsan yadda Zaki Taimakamin ki Taikamanin I need a help plz..!
Yafada ya na kara Riketa acikin Jikinsa Numfashinta taji na neman Daukewa jikinta ya Fara rawan Dayasa da Sauri ta mtsa baya ya kara Biyota zai riketa kawai sai ta Damke Hannunsa Cikin Rawan jiki batare datayimai mgana tajasa Kiii shi kuma ya Biyota suka Fito suna Saukowa Daga Saman Benen ne daidai Sanda Habib ke Fadama Laila
"Bake kika Daukeni aiki ba..Saboda haka baki isa ki Koreni ba..!
Dakatawa Sunaima tayi ta juya tana kallon Sulaiman Daya bada gabadaya Hankalinsa akan Laila iin ta Lura Har Jikinsa ya Fara rawa Tsausayinsa ya kamata sai ta Damke hannunsa kawai ta Juya suka koma Dakin Allah ya Taimaketa ba wanda ya gansu suna Shiga Ta kallesa tace"Kana son na Taimaka maka..?
Kai ya gyadamata da Sauri itama Cikin Hanzarin tace"To ka san duk yadda zakayi ka rika zuwa Dakina da Daaddare..Zan rika baka mgani da in kana sha zaka warke kaji..!
Zura mata ido yayi kafin yace"Laila bazata barni ba Sunaima..!
Yafada kamar Hajiya Zabba"u ce Laila kai Sunaima ta Dafe Cikin Takaici Gefe Daya tana Dauke Hawayenta Kafin Tace"Eh nasani ai bazaka Fadamata ba..in zaka zo kada ka bari kowa ya ganka..Cikin Dare in kowa yayi barci zan rika barin Dakina abude da kazo sai ka shigo kawai kaji..!
Ido ya Kura mata kafin ya Saka Hannu ya Damkwalo Hawayenta Cikin Wani yanayi yace"Meyasa kike kuka..?
Saurin Share Hawayenta tayi kafin tace"Kaji abunda nace ko..?
Ina jiranka Daga yau..Kuma kada ka fadama Laila..Kada kuma ka bari ta ganka kaji ko..?
Bata jira cewarsa ba ta Juya Zata tafi ya kara Riko Hannunta Tana Juyowa ya sakarmata Idanuwansa masu Narkar da Zuciyarta Cikin Wata Murya yace",Don"t Leave me.!
Sunaima tadan Murmusa tana Fadin"Kada kadamu...Insha Allahu!
Da sauri ta Sabule Hannunta ta Fice Tana Waigen kada marliya ta hangota Tana Sauko kasa Lokacin har Habib ya Tafi Laila na Tsaye nata Kumfar baki ta Lallaba ta koma Dakinta ta Fada Kan gado Lokaci Daya ta Fashe da kuka,Gabadaya Sulaiman ya gama Raunana mata zuciya Gabadaya Jikinta ya saki Mganarsa da yanayinsa ya kasa mace mata anya Laila Tana so ta gama da Duniya Lafiya.
Bata da yakinin Sulaiman zai zo ammh Tana da Yadda akansa zai zo kamar yadda ta Fadamai..
Tashi tayi ta Dauro alwala taxo ta Fara Sallah Tana Sallah tana kuka Alokacin ma Farkon Dare ne domin ko 12 batayi na Dare,Ta Daga hannu Sama Tana Kuka tana Fadama Allaah Sai gashi Sunaima na Rokon Allah ya karkato da Hankalinsa Allah ya Fidda shi Daga Sharrin Laila.
Sai da ta gaji barci ya fara Daukanta kana ta kwanta nan saman Darduman tayi Barci sai asuba ta iya tashi.
Haka tatashi Ranta ba Dadi Gabadaya jikinta asanyaye yake ba su Wasim Shiyasa ta koma barci bayan Sallar asuba da Takaochin Rashin zuwan Sulaiman kamar yadda ta saka aranta zai zo.
Ranar ko Kofar Dakinta bata Fita ba sai Da yammah da zata tafi wajen aiki ta Fito Cikin Shirin Tafiya Magajiya kadai ta ma Sallama ta Fice kamar ko yaushe adaidaita ta samu zuwa asibiti acikin Ranta Tana Tunanin kada Sulaiman yazo bata nan tana ji aranta Jiya bai samu Dama bane yau kila yazo bai ganta ba.
Tana aiki ammh Gabadaya Hankalinta na kansa har da Safe ta Dawo Gidan Bata Cikin Hayyacinta ta Shiga Dakinta Tana Dube Duben ko zata ga alamun yazo sai dai bata gani ba Kusan kwana Uku Tana Hashashen zuwansa bata gansa ba Sai ta Fidda Rai ta kuma yardan ma kanta bazata iya Taimakon Sulaiman ba Domin bata da wata Hanyar da zata Taimakamai bayan wannan Hanyar.




*Janafty*

MIJIN KANWATA(K'ADDARATA)Where stories live. Discover now