BABI NA DAYA

491 20 3
                                    


*PAID BOOK 300*

*BIBIYATA YAKEYI*
_(WAYE SHI?)_
   

*بسم الله الرحمن الرحيم*

ZAYNAB BAWA

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

    TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

   WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

  BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝


*Allah yabani ikon rubuta muku abu mai amfani kamar yanda nafarashi Lafiya Allah yasa nagamashi lafiya.*

Page 1

Jin alamun za'a shigo ɗakin ya sanya nayi saurin ɗauke idanuwana daga kan madaidaiciyar tv ɗin dake manne ajikin bango nayi saurin maida hankalina ga littafin dake gabana. Da sallama ta buɗe labulan ɗakin ta shigo ta zauna a ɗaya daga cikin  kujerun da suke cikin falon. Matashiyar matace wacce bazata wuce shekara talatin da takwas ba. Kallona tai ta taɓe baki ta zare remote tana faɗin.

"Nida ɗakina amma ban isa abarmin tashar dana keson kalla ba kulllum sai dai wannan tashar kwallon ta jaraba, ke kina mace ni bansan mai ya hadaki da wannan kallan kwallon azabar ba."

Nidai bance komai ba harta canja tashar ta maida zuwa tashar shirye-shiryen Hausa sannan ta ajiye remote din. Mikewa nayi ina zumburo baki nafice daga ɗakin ina jiyota tana faɗin.

"Dama nasani wannan karatun na munafunci ne kallon ball kawai kike yi."

Nidai bance komai ba na wuce zuwa ɗakin matar mahaifina wacce muke kira da Aunty na zauna na cigaba da kallon ball ɗina acan. Sai da aka gama sannan raina yayi sanyi domin tawagar da nake so itace ta lashe wasan kwallon. Raina fess na fito na nufi ɗakin mahaifiyata. A uwar daki na sameta na shiga na zauna tana faɗin.

"Angama kallon ball din kenan?" Batareda ta jira amsata ba ta cigaba da fadin. "To sai amaida hankali maza ayi karatu tunda angama ibadar." Zumburo bakina nayi nace.

"Nifa dama Mama na rigada nagama karatu, kawai bita nake yi."

"Gara dai ki maida hankali kiyiwa kanki faɗa Mamee kitsaya kiyi wannan karatu dakyau ke kanki shaida ce kinga yanda aka samu kika fara wannan karatu, har indai kikaki nutsuwa kici wannan jarabawar kika fadi kinsan yanda mahaifinku zai ji. Idan kuma so kike ki karasashi toh, kina gani dai da ya ya aka yi aka hado har dubu casa'in aka biya miki rijista dan kawai kin nuna kina so, idan kika zuba masa kasa a ido baki yiwa kanki adalci ba. Ki daure kiyi karatu kici weeding ɗin nan in sha Allahu har indai kin wuce zamu san yanda zamuyi mu hada karfi da karfe wajan ganin mun taimaka kinci gaba. Idan kuma kika tsaya wasa kika fadi ko shakka babu nasan cewa aure babanku zai yi miki da karancin shekarunki dan ya samawa kansa saukin rayuwa. Amma idan kinci wannan jarabawar koda ace auren ya yi miki sai mijinki ya karasa daukan nauyin karatun naki ki karasa agidansa." Saurin girgiza kai nayi nace.

"Dan Allah Mama ki daina fadin haka, zanyi karatu kuma in sha Allahu zanci." Sai da ta  kalleni na wani lokaci sannan tace.

"Shikenan Allah yasa." Nace,

"Amin." Saboda yanda nakeso naci jarabawar nan haka na hana idanuwana runtsawa sai da na raba dare sannan na kwanta.

Washe gari kuwa kafin kowa ya tashi na tashi kusan kaff gidan na rigasu tashi ina jiyo mahaifinmu zai fita sallar asubahi yana bubbuga kowa ne ɗaki domin atashi ayi sallah. Ina idar da sallah na shiga wanka  na shirya ban tsaya karyawa ba dan karfe bakwai zan shiga jarabawa mama tabani kudin abun hawa nafito harabar gidan babu kowa haka naabude karamar kofar dake jikin gate dinmu na sanya kaina nafice yar, dakyar  nasamu abun hawa nashiga yawuce dani makarata zuwa 12:00pm nagama duk wani abunda zanyi a makaaranta na nufo gida dan ban fita ta ishesshen kudin da zai isheni nayi karin kumallo ba kuma yunwa nakeji shiyasa ina gama abunda zanyi na nemo hanyar gida dukda kasancewar bawai dama ina tsayawar bane,

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now