BABI NA SHIDA

74 9 1
                                    


*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023

*بسم الله الرحمن الرحيم*


BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 6

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

    TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

   WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

  BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝





Dr Salman yaja numfashi Sannan yacigaba da faɗin.

"Jiya Bayan wayarda mukayi dake nasamu saƙo daga baya kira yashigo, anyimin offering kuɗinda hankali bazai iya ɗauka ba akan narabu dake banaji akwai wani mahaluki da zai iya cire wannan kuɗin yabayar kawai saboda soyayya har indai akwaishi toh son dayake yiwa wannan abu duk duniya baza'a samu wanda zaiyi mata kwatankwacinsa ba, da baki sanar dashi ba ni kaɗai kika faɗawa zan fahimta" Da mamaki nake kallonsa nace.

"Amma ni ai malam babu wanda na faɗawa kuma mutumin da kake referring akansa ni banma sanshi ba" Ya kalleni kallo irinnna wanda yakeson gaskata abunda nake faɗa. ya jijjiga kai yace.

"Amma abun da mamaki dan fa har zuwanda kikayi office ɗina jiya yana sane da hakan dan saida yayi maganarsa kuma maganar da mukayi a waya yayimin ita jiya"

"Wallh Malam ni ban faɗawa kowaba ko zuwan office ɗinka danayi ko agidanmu ban faɗa ba"

"Eh toh zan yarda da cewa baki faɗawa kowaba saboda saida nayi tunani nace idan keda kanki kika sanar masa kiranki danayi awaya da zuwa office ɗina hakan yana nufin kina ra'ayinsa kenan idan hakane bayada buƙatar bani kuɗi kafin narabu dake har indai kina ra'ayinsa keda kanki zakice akwai wanda kikeso, tunda bakisan dashi ba tabbas yana BIBIYARKI toh Amma WAYE SHI?" Shiru mu dukanmu mukayi dan bamuda wannan amsar,

"Malam dan Allah zan iya ganin numbern da aka kiraka?" danno kan number ɗin yayi ya mika min yace.

"Gata nan idan kinada bukata zan iya sakawa a Bibiya miki layin"

"kayi hakan dan Allah malam nagode"

"Babu damuwa zuwa gobe duk yanda ake ciki zan sanarda ke. amma sai dai Kiyi Hakuri na janye zancen neman aurena akanki dan wannan ga dukkan alamu zai iya aikata komai akanki bazan ɗauki wannan risk ɗinba dama ace munsan WAYE SHI? toh da zamusan yanda zamu ɓullowa lamarin amma rikici da abunda baka taɓa kallonsanba ai babban kasada ce" Har wani zazzaɓi nakeyi Jin wannan lamari dayake faruwa koma wanene yanzu yaci ace ya bayyana kansa. Malam yace.

"Bani wayarki nagani" na miƙa masa wayar jiki a sanyaye Ya dudduba sannan yace.

"Abunda mamaki da nayi zaton ana sauraron kiranki amma kuma ya nunamin babu mai bibiyar layinki shikenan dai Zaku iya tafiya in sha Allahu idanna sameshi zan sanar dake Godiya nayi masa sannan muka tashi muka fita"

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang