BABI NA BAKWAI

92 9 3
                                    



*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_
2023

*بسم الله الرحمن الرحيم*


BY
ZAYNAB BAWA

PAGE 7

FREE PAGE SUN KUSA ƘAREWA KUSHIGO CIKI DAN AFAFATA DAKU."

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

    TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

   WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

  BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝

******

Munata shirye shiryen walima dan haka yau ban fita school saura 2days walimar Sauƙanmu gidanmu da gidansu maryam gabaki ɗaya anata shirye-shirye, Baba ya bugamin Memo masu girma guda ɗari sunana da Maryam ne ajiki domin maryam yanzu tadawo ƴar gida agidanmu kamar yanda nima nadawo agidansu, Mama kuma key holder ta buga mana mai suna ajiki anty tayi mana sticker kowanne guda ɗari ne dan haka na rabasu a tsakiya na 50-50 kowanne natafi dan kaiwa maryam nata, Itama nasamu gidansu anata shirye-shiryen walimar, ganin motar Hamma a harabar gidan ya sanyani sakin murmushi dan nasan yana gida ta iya yiwuwa nayi arba dashi hakan kuma zai samamin sanyi acikin zuciyata.

Part ɗin Umminsu Maryam nafara wucewa na sameta da wasu daga cikin ƴan uwanta suna shirin walima domin ita maryam za'ayi mata walima agida.

Shiga nayi muka gaisa tacemin maryam na ɗaki da ƙawayenta suna aiki, miƙewa nayi nashige ciki. A falonda Hamma yake zama natsaya naketa raba idanuwa na ko zan ganshi amma wayam ina tunanin jama'arda suke gidanne yasa bai zaunaba gabaki ɗaya sai naji babu daɗi nan da nan murmushin dake kan kumatuna ya sauƙa jiki a sanyaye nayi sallama na shiga falon maryam, tana jina ta saki ihu tana faɗin ƴar halak kinƙi ambato wallhy babe yanzu nake zancenki,

Raɓawa ta cikin ƙawayenta nayi bance komaiba na isa kujera ma zauna sannan na taɓe baki nace.

"Toh sai me? Ninace kiyi hira tane da zaki cikamin kunne daga shigowata?" harara ta wurgamin tace.

"keh wallh ba'a abun arziki dake"

"saina tsiya" na ƙarasa maganarta.

Cousin sisters ɗintane a falon da wasu daga cikin ƙawayenmu wanda mukeyin nursing tare su biyu ga dukkan alamu sunzo tayata aikine dan dama tun daga lokacin da suka fuskamci babanta hamshaƙin mai kuɗine suke shige mata.

Souvenir ne agabansu dayawa ga dukkan alamu shiryasu sukeyi, Sannu da aiki kawai nayi musu na dubi maryam nace ga aikanki inji mama da Baba da Anty,

Na miƙa mata ƙatuwar jakar danazo dashi karɓa tayi ta buɗesu taciro tafara karanta ihu tasaka tana faɗin.

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now