BABI NA UKU

105 11 1
                                    

*BIBIYATA YAKEYI *
_(WAYE SHI?)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

  BY
       ZAYNAB BAWA

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid book 200
*ƘADDARAR RAYUWA*

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

    TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

   WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

  BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝

    PAGE 3

    Kallon Mama nayi naga tayi shiru tana saurarena ni take jira na bata amsa batareda bata lokaci na nace.

" Tace saboda mahaifiyarsu tabar gidan ta dalilinta." shiru Mama tayi sai can tace.

"Allah ya rufa asiri." Na amsa da

"Amin."

"Gobe idan Allah ya kai mu zaki koma dakin yayyunki da kwana, Saboda bai kyautu ace mu muna kwana da yaran mu daki daya su kuma suna can su kadai ba." Toh kawai na amsa dan nasan dole hakan zata faru. Mama nasake kiranta. Cikin kaguwa da tambayoyina tace.

"Mamee ki kwanta kiyi bacci yanzu dan bazaki fahimci lamuranda suke faruwa agidannan ba amma idan lokaci yayi zaki fahimta"

  "Zan kwanta Amma Mama yakamata izuwa yanzu ace kowa yayi hakuri tunda abun yadauki shekaru" kallona sosai tayi sai can tace.

  "Mahaifinku yana bukatar ganin iyalansa a hade waje daya baida burin daya wuce wannan, ki kasance  mai son yan uwanki kada kitaba kullatar yan uwanki a wani dalili komai girmansa"  Kai kawai na gyada tace.


  Dare yayi ki kwanta na amsa na lumshe idanuwana ina karanto addu'oi ahaka har bacci ya daukeni."

Washe gari na koma dakinsu da kwana, naji dadin zamana a dakin Saboda suna da wayar Android hakan  ya sanya idanna bace cikin dakin ko motsina ba'a jiyowa barin ma idan na samu wayar da data na ringa bin labaran yan wasanni kwallon kafa kenan. Nafi amfani da wayar Fadeela dan tafi saukin kai saboda kwanaki kadan da muka yi da ita har mun saba da ita, kuma itace Babba dama. Zaman mu da ita yasa ta fahimci yanda nake masifar son wasan kwallo hakan yasa take download na wasannin koda na tafi hadda ta ajiye min. Aysha kam yawanci gaisuwa kawai ke shiga tsakanina da ita dan ita sam bama tada sakin fuska ba kamar fadeela ba."

———
Dawowar mu daga sallahr la'asar kenan babu wani malamin daya shiga mana, hakan yasa muka zauna muna ta hira nida kawayena muna dan hirar mu, Maryam ta dubeni tace,

"Mamee an duba miki results kuwa?" Da mamaki na dubeta nace.

"Result ya fito ne? Kai Wallahi ban sani ba."

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now