BABI NA BIYU

114 13 1
                                    


*BIBIYATA YAKEYI*
_(WAYE SHI?)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


  BY
     ZAYNAB BAWA

Assalamu alaikum
Ina kuke manyan mata?

Matanda suka san kansu, Suka amsa sunansu Mata, Amarya, Uwar gida shin kin taba using kayan *ROYAL EXQUISITE* kuwa??? Idan kin taba to barkanki danna tabbata kin fita daban da sauran mata, idan Baki taba ba kuwa lallai an barki a baya kuma kin dade kina cutar kanki da mijinki, Domin samun kayanmu masu kyau da inganci zaku iya tuntubarmu domin munada Kayan mata masu kyau da inganchi Kamar su
Virgin again
Tightening pills
Turaren ban mamaki
Sweetness agents
Wetness agents
Infection set da sauransu
Domin ƙarin bayani ku tuntubemu ta wannan numbern
08030644073

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝



PAGE 2

     Bayan fitarmu daga ɗakin gabaki ɗaya, Mama ta dubi Anty ganin yanda jikinta yayi sanyi duk sai taji babu dadi, cikin karfafa guiwa Mama tace.

"Kiyi hakuri idan wannan abun ne yaci ace yanzu ya zame miki jiki ya daina damunki gabaki ɗaya. Kuma ina da tabbacin wata rana zai shude ya zama labari kamar hakanma bai taba faruwa ba."

Saida Anty tayi murmushi mai ciwo sannan tace.

"Mama dole na damu domin ba yanzu bane lokacin damuwar, lokacin da abun zai zama wani iri nakeji, ina matukar tausayawa yarana dan sune kananu acikin gidan nan. Kuma sune wanda basu da farin jini, inaji ajikina ba zasu taba son yaran da na haifa ba. Yau idan akace babu ni yarana basu da makama tunda sune manya sune danginsu kadai kuma basa son su, gara ke koda yaranki basu tasa sosai ba amma kina da dangi wanda zasu iya rike miki yaranki kuma basajin haushin naki kamar yanda suke jin haushin nawa yaran, ni ba uwa ko uba gareni ba bare nayi tunanin ko babu ni nabar wanda zasu kulamin dasu." Mama ta katseta da fadin.

"Haba Habiba wai me yasa kike haka ne? Duk me ya kawo wannan zancen? In Allah yayarda Allah zai barmu akan yaran mu har zuwa girman su." Anty ta share kwallar data zubo mata tace,

"Shikenan na daina yanzu kishiga ki fadawa babansu jikin Hussainin danni idan na shiga sai ya zama wani abun daban."

Mama ta mike ta fice daga dakin. Ganin takalma a kofar dakin Baba ya sanya ta tsagaita kamar bazata shigaba sai kuma tayi sallama ta shiga. Dukkan su wanda suke palourn suka amsa mata sallamar,

Kujerar dake kusa da ta Baba ta karasa ta zauna tana karewa yan mata guda biyu dake zaune kasa kan carfet kallo fuskarta dauke da fara'a tace.

"Ikon Allah wa nake gani kamar Fadeelah da Ayusha? Lallai sun girama masha Allah shekaru da yawa ba'a hadu ba." Baba yace.

"Sune kuwa, shekaru dayawa kam, yanzu nake niyyar na aika a kirawoku gabaki daya domin yayansu yazo min da wani zance." Mama tace.

"Toh ai gamu bari nakira Habiban tana tare da Hussaini yanzu Mamee ta dawo dashi daga makaranta zazzabi ya rufe shi."

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Onde as histórias ganham vida. Descobre agora