EPISODE 1

55 4 0
                                    

MAGANA TA ƘARE

  True Life Story

 Zm-Chubaɗo✍️

*Bismillahirrahmanurrahim*

Garin Kano Unguwar Zage da misalin ƙarfe 1:pm na rana. Gidane mai ɗan girma wanda da ga kallon farko zaka fahimci cewar gidan gandune, ma'ana (Gidan Yawa) ɗakunan dake cikin gidan guda huɗu ne kuma ko wanne ɗaki ciki da falo ne, babban abinda ze baka mamaki shine kowa harkan gabashi kawai yakeyi bame shiga harkan kowa, ma'ana duk abinda kaga dama shi kawai zakayi babu me taka maka birki. kaf cikin matan dake gidan duk yaran mata ne ma'ana duk matasa ne, mutum ɗayace mai shekaru da yawa ita ce Atinan ɓula wadda ba zata wuce shekaru sittin a du iya ba. Kowa hada-hadar gabansa kawai yakeyi masu yin wanke-wanke nayi hakama masu yin saƙar hannu sunayi, kamar daga sama suka fara jiyo hayaniya da kuwar jama'a daga ƙofar gida, malam Bello Mijin Sahura ne kawai a gidan Amma Mijin Bintalo da Abuwa duk sun fita neman sisin kwabonsu, Taɓe baki Bintalo wadda ke zaune akan kujera ƴar tsuguno tayi sannan ta kalli Abuwa dake saƙa a ƙofar ɗakinta tace "Kai Allah Madai ya sauwaƙe wllh nidai kam da haihuwar mutumin banza irin wannan yaron wllh gwara na koma ga Allah ban haihu, wannan masifa har ina yaro yazo ya zame mana bala'i a cikin Gida." dariya Abuwa ta saki tareda Ajiya zaren saƙar dake hannunta a ƙasa tace "wllh kamar kin shiga raina kin leƙa, ke nifa na gama gajiya da bala'in da wannan ɗan iskan yaron ke ƙoƙarin jefa mu" ta faɗa tana riƙe haɓa tana kallon Bintalo wadda ke ƙoƙarin juye taliyar hausan dataɗora a wuta,  tsaki Bitalo ta saki tareda ɗibar ruwa a farin bokitin dake ƙofar ɗakinta tace "don bala'i da masifa kullum gidan mu a zagaye yake da ƴan-sanda sekace gidan Ɓarayi ni dama wataran su kashe ɗan iska a karanbatta kowama ya hut......"  "hmmm Bintalo kenan to don Allah meye marabarsa Ɗan Daba da ɓarawo?" Abuwa ta jefa mata tambayar yayinda take kallon tsakiyar idanunta. "af hakane kuma wllh babu wata maraba a tsakaninsu duk kanwar ja ce" cewar Bintalo. "Ke Bintalo wai meyasa bakinku baya faɗar alkhairi ne?" Atinan ɓula ta faɗi hakan yayinda take yaye labulan ƙofar ɗakinta ta fito tana kallonsu, sannan tacigaba da cewa "wllh kuna bani mamaki kubiyun nan idan kuna aikata wani abin, har indingajin cewar kamar bakusan zafin haihuwa ba" kallon galala kawai suke binta dashi ba tareda sunyi magana ba. murmushi kawai Atinan tayi tacigabada cewa "da alama gabaɗayan ku baku san ita haihuwa ba'ai mata zaɓe shiyasa duk kuke faɗin hakan, Allah dai ya bamu raida lfy ko banza mayi kallo a nan gaba."   shiru Sukai mata babu wanda ya tanka ta sam bata damu da shirunsu ba taci gabada cewa "wllh inajiye muku tsoron abinda zezo muku nan gaba a sanadin jaye-jayen bala'inku da kukeyi da bakunanku, ƴaƴan nanfa kuma kun haifa kuma na tabbata kaf cikin ku babu wadda tasan me nata ɗan ze zama se Alla....."a'a malama Atine karki mana mugun baki akan ƴaƴan mu dan kawai kinji mun maki shiru" Abuwa ta katseta ta hanyar faɗar hakan. Murmushi tayi kawai batace komai ba hakama Hadiza wadda ke wanke kwanikan da sukaci abincin Rana, tunda suka fara magana take hawaye sabida jin irin alkaba'in dasuke janyo ɗanta guda ɗaya tilo a duniya, share hawayen fuskarta tayi da bayan hannunta sannan ta miƙe zata shiga ɗaki. hakanne yayi dedai da shigowar ƴan sandan cikin gidan da ankwa ɗaure a hannun Ibrahim wanda akewa laƙabi da Wajagal. Salati Su Abuwa da Bintalo suka saki lokaci guda kuma suka dafe ƙirji idanunsu duk a waje, gabaɗayan su kasa magana sukai amma a ransu sun tabbatar cewa yau Wajagal Masifar daya jawo me lasisi ce. Hadiza kasa magana tayi sabida tsabar tashin hankalin datake ciki tunda ta tsuguna ta haifi Wajagal bakinta be taɓa hutawa da magana ba tunda ya fara girma, shiyasa gabaɗaya ta ɗaura da sintirin zuwa police station  a halin yanzu tana kyatata zaton cewar babu station ɗinda basu san kallar fuskarta ba, ɗaya daga cikin ƴan-sandar da suka ɗauroshi da sarƙa ne ya dakawa  Su Bintalo tsawa yace "ina Uwar wannan yaron?" da sauri Suka Nuna Hadiza dake tsaye tana hawaye, kallon tsaf ya dinga binta dashi har seda taji ta muzanta a gurin sannan ya bude baki da nufin ya daka mata wata tsawar kamar yanda yaywa su Bintalo Wajagal yay saurin tarar numfashinsa yace "na rantse da buwayar Lamyalid walam yulad idan kayi ganganci yiwa uwata tsawa sena fafema ciki da ƙarfe" yay maganar cikeda dabanci gamida taurin zuciya. Kasa magana ɗan sandan yayi dukda irin zafinda maganganun wajagal ɗin sukai masa, sabida yasan halinsa sarai tabbas ze aikata abinda ya faɗaɗin don ba ƙaramin aikinsa bane ..... Muryarsa yaɗan saisaita sannan ya kalleta yana binta da wani ɗan iskan kallo yace "ina fatan kun tara kuɗin dazaku ɗauki lauya a kotu don wannan karan shaiɗanin ɗanki baze tsira ba" share hawayen daya zubo mata tayi sannan ta ɗaga kai ta kalli Ibrahim ɗin a karon farko tun shigowarsu dashi gidan sannan ta ɗauke kanta tace "Zanyi farin ciki idan har akan laifinda ya aikata hukumar zatai masa hukunci, idan har Ibrahim ya aikata abinda kuke zarginsa akai ina roƙonku dan Allah kada ku saurara masa, haka kuma idan har be aikata abinda kuke zarginsa dashi ba to kada ku zalinceshi!!" tana kaiwa nan ta juya da sauri ta shige ɗaki sukuma ƴan Sandan sukai waje dashi, a haka suka ratso dashi ta tsakiyar Mabugar zage a ɗaɗɗaure suka sashi a mota sukai police station ɗin ƙofar wambai dashi a ƙarƙashin jagorancin Aminu Bala. Suna isa dashi aka jefashi a bayan kanta aka naɗa masa duka tareda sagar masa da duk wata gaɓa dake jikinsa, gefan bakinsa kuwa banda jini babu abnda yakeyi  sannan suka fita suka barshi a kwance yana maida numfashi, se yamma liƙis dabda ketowar Almuru (Magariba) sannan D.p.o ya ƙaraso Seda sukai sallar Magariba sannan D.p.o Ali musa yasa aka fito dashi zuwa ofishin sa se faman cijewa yake kamar bashi aka gama jibga ba, Ali musa ya kalleshi kimanin tsayin minti 2 sannan yace " Ya sunan ka?" banza yay masa kamar baze amsa ba hakan yasa wanda ke bayansa ya tokareshi da ƙafa yace "bada kai ake magana bane ?." bakinsa ya goge da hannunsa wanda suke ɗaure cikin ankwa sannan ya kalleshi yace "ai bansan magana akemin ba seda naji ka mai-mai tamin ɗan kanzagi kawai" ɗan sandan zeyi magana kenan Ali musa ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu.  "inajinka ya sunan ka?" a taƙaice yace "Wajagal" sunanka na gaskia nake nufi bana banza ba" cewar Ali musa. "Ibrahim" ya faɗa a takaice, ɗan rubutu Ali musa yayi kaɗan a wata farar takarta sannan ya sake kallonsa yace "meyasa kuka shiga gidan  Alhaji Tajo mai gwanjo kukai masa Sata harda yunƙurin yin fyaɗewa ɗiyarsa?" wani ɗan iskan kallo ya watsawa D.p.o ɗin sannan yay wani gajeran murmushi yace "ni idan zanyi ɓarna banabin dare rana nakebi, sannan kuma ni bana buƙatar zuga nikaɗai ma gaiyane sannan a lamari na babu keta alfarmar mace, don haka bani bane na shigar mas gida ba" "ok" konsabil maidashi sel sannan make sure kun sanya ido akansa sosai." Cikeda girmamawa suka amsa da "ok sir" hannunsa Aminu bala ya kama da sauri ya fusge yace "kai naga kanata wani zaƙewa to wllh kasa a ranka cewar  daga yau kullum a fargaba zaka dinga kwana sabida ba wani ɗan lawaha dazewa uwata tsawa na ƙyaleshi!"  ya faɗ yayinda yake takawa cikin irin takunsu na ƴan daban da sukaci dubu se ceto ya coma sell ɗin Ya zauna, kallonsu kawai yake ɗaiɗai har duhu ya raba a ransa kuwa Allah kaɗai yasan mugun abinda yake shiryawa akan Alhaji Tajo mai gwanjo idan yabar sel ɗin....... Har dare ya fara tsalawa idonsa biyu be rintsa ba kuma da Alama bashida niyar Rintsawar, abu ɗayane ke masa yawo a saman zuciyarsa wanda har yanzu sam ya kasa mantawa shine kamashin da Alhaji Tajo Mai Gwanjo yasa akayi, wata zazzafar iska ya fesar daga bakinsa sabida ɓacin rai Still idanunsa a soye babu alamar jin Bacci a cikinsu.   kamar wanda aka tsikara ya miƙe da sauri tareda kallon gefan hannunsa wanda ya fara kumbura sabida duka dayasha ɗazun Murmushi yayi wanda ya bawa yankan gefan kumatunsa damar tattarewa, guri yaɗan shafa da ɗaya hannun nasa sannan yace "wllh sena rama wannan dukan akanka Alhaji tajo yau ɗinnan base gobe ba!" taune leɓansa nanƙasa yayi da haƙoransa lokacin guda kuma ya fara laluba gefan wandonsa ya zaro mukullin daya sata ɗazu a ƙugun Aminu Bala, sarƙar Hannunsa ya fara kwancewa da bakinsa sannan ya nufi ƙofar sell ɗin itama ya buɗe yay waje abinsa, a can gefe ya hangi Su Aminu Bala da tawagarsa se sharar bacci suke sedai dukda hakan Haske ya gama gauraye ko ina kamar Rana. A dabarance ya silale ya gudu ba tareda yayi kuskuren yin motsin da wani mahaluƙi ze ganshi ba, be ɗauki wani lokaci me tsaho ba ya shigo Unguwar zage kasancewar babu tazara sosai a tsakanin station ɗin da kuma gidansu, kasancewar lokacin zafine duk yawanci matasan unguwar na fitowa ƙofar gida su shimfiɗa tabarma su kwanta sabida zafi, tsaki ya saki a ransa yace "wato ni inacan an kameni su suna nan suna kwanciyar zafi, tona rantse da Allah bzan barku kiyi bacci cikin salama ba bari na shiga gida na fito ku gani" kai tsaye ɗakin Ummansa ya nufa tareda Tura ƙofar ɗakin ko Sallama beyi ba dan duk a zatonsa tayi bacci a wannan lokacin, ja yay da baya kamar wanda ke cikin maye yace "Kai wai Umma har yanzu idonki biyu bakiyi bacci ba?" ya faɗa se wani ƙyalla ido yake kamar mara gaskiya. umma dake zaune bisa Sallayar data idar da sallah ta ɗaga kanta ta kalli ƙaramin agogon bangon dake manne a ɗakin wanda ya nuna ƙarfe biyun dare dai-dai sannan tace "Ibrahim meyasa ka gudo?" ɗan turo baki yayi kaɗan yace "Umma to meyasa zan zauna a can bayan ni banyi laifin komai ba?" zatayi magana kenan tayi saurin dakatawa sabida zafinda ƙirjinta ya farai mata, da sauri ya ƙaraso kusada ita cikeda tashin Hankali yace "don buwayar ubangiji Umma kiyi haƙuri karkiyi fushi kinji? Wllh ban aikata komai kema kinsan da hakan ai tunda jiyama a gida na kwana ban fita ko ina ba" janye jikinta tayi daga nasa jikin sabida warin tabar wiwin dake tashi a jikinsa wadda yasha tun kafin ƴan sanda su kamashi da Rana, hawayen daya ƙarasa zubo mata tasa hannu ta share sannan ta maida kallonta sosai gareshi batareda tayi magana ba, gabaɗaya duk ya Rame yayi wani irin duhu kamar ba Ibrahim ɗinta mejin magana ba a shekarun baya. Ɗan jim tayi kaɗan still tana hawaye sannan ta buɗe bakinta wanda taji yay mata wani irin nauyi sabida ciwon abinda yake aikatawa tace "Ibrahim har zuwa wani lokaci za'a ɗauka kana wannan dabar da bazata kaika ko ina ba? Shin kai baka jiyewa kanka tsoron abinda zeje ya dawo maka a nan gaba ne? Dududu gabaɗayanka shekarunka nawa ne a Duniya Ibrahim?" shafa kansa kawai yayi batareda ya kalleta ba yace "Ashirin da biyar ne" girgiza kai kawai tayi tareda sakin wani ɗan guntun Murmushi wanda yafi mata kuka ciwo tana kallonsa,  hawaye ne suka shiga zubo mata a nan inda take zaune ta ɗaga hannunta tana kallon Sama tace "ya ubangiji kaikaɗai ne sheda akan irin zafinda zuciyata keyi bisa jarrabawar danake ciki akan wannan Yaron! Ya Allah ina roƙonka da sunayenka mafiya kyawu ka bani ikon cin wannan jarrabawar." " hmmm wllh Umma kekike ɗorawa kanki damuwarsa da har yake ƙoƙarin kasheki da baƙin cikinsa, meyasa bazaki cireshi a ranki ki sallamashi ba tunda haka yakeso" Zainab ƙanwarsa wadda ta farka daga bacci tun shigowarsa ta faɗi hakan sabida ciwonda ɗabi'un yayan nata suke mata ciwo a ranta itama. Kafeta kawai yay da ido yana kallonta, daga irin kallonda yake mata ne yasa ta shiga taitayinta sabida tasn halinsa sarai bashida yawan magana sabida miskilancinsa ammafa idan ya damƙeta tofa seta yabawa aya zaƙinta. Murmushin ƙarfin Hali Umma tayi sannan ta kalli Zainab dake tsaye jikin ƙofar shiga can uwar ɗakan su tace "har yanzu ke yarinya ce Zainab bazaki taɓa fahimtar Fa'idar haƙurin uwa akan ɗanta ba senan gaba!"  sosai kalaman Umma sukasa Jikin zainab yin sanyi don haka ta sunkuyar da kanta ƙasa tace "don Allah Umma kiyi haƙuri!" Miƙewa yayi ba tareda yayi magana ba ya shiga uwar ɗakinsu ya kai tsaye cikin jakar kayansa ya buɗe ya ɗakko wata baƙar Hula irinta masu farauta ya saka a kansa ya fito, daka kallon farko da Umma tai msa tasan ransa a mugun ɓace yake tunda taga ya sako wannan hular kuma idanunsa sun fara sauya launi shinfiɗarsa dake gefan Umma ya ɗaga ya zaro wata zabgegiyar wuƙa wadda ke cikin kufenta a rufe Ƙofar fita ya nufa batareda yayi mgana ba, kai tsaye ƙofar fita ya nufa da sauri Umma ta rigo rigarsa ta baya ta jawoshi ya dawo cikin ɗakin ɗaga hannu tai zata zabga masa mari se kuma ta fasa aikata hakan, sabida tasan muddin ta mareshi to al'amarin ƙara tsamari zeyi a zuciyarsa wanda takeda tabbacin cewar akan Alhaji Tajo Mai-Gwanjo ze sauke komai. Hannunsa ta kama tareda zare wuƙar tana kallonsa tace "idan har hannunka ya zubar da jinin wani a yau wllh Ibrahim sedai ka nemi wata Uwar bani ba!!!!" da sauri ya ɗago manyan idanunsa da suka rine sabida fishi yana kallonta, nan da nan jikinsa ya ɗauki rawa kamar mazari kai kace gangi ake kaɗa masa sabida tsabar yanda jikinsa ke rawa.  

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now