EPISODE 9

6 2 0
                                    

MAGANA TA ƘARE
    True life story

Chubaɗo✍️

             09

Banyi Editing ba🙅‍♀️

"Kin gansu ummah"

Ɗaga idanunta Ummah tayi da sauri tana kallonsa ba tareda ta iya haɗiye naman dake  bakinta ba ta ce "i..b..rahim!! wannan kuɗin  daga ina ka Samo su?" tai maganar tana ƙara fito da manyan idanunta waje alamar kaɗuwa.

Sauke kansa ƙasa yay hannunsa riƙeda zaren Tabarman dake shimfiɗe a tsakar ɗakin yace "Umma wllh wni Buzu ne ya bani kyautar su ɗazu a cikin nasarawa don kawai na taimaka masa" zatai magana kenan yay saurin katseta ta hanyar zaiyane mata kaf abinda ya faru tsakaninsa da wannan Bawan Allah.  Harya gama maganar bata dena kallonsa ba amma kuma har cikin zuciyarta taji daɗin cewar ɗanta yayi abin kirki, murmushi Umma tayi sannan ta kalleshi tace "Amma ibrahim meze Hana tunda Allah ya taimakeka kaci jarrabawarka ta kammala sakandire meze hana ka koma makaranta da wannan kuɗin?, tunda naga sunada yawa sosai inyaso sauran seka nemi wata sana'ar ka dingayi wadda kuɗi baze yanke maka ba"  murmushinsa dake wahalar gani ya saki har seda kumatunsa suka lotsa sannan ya kalli Umma yace "shikenan zanyi yanda kikace  umma amma sedai ba yanzu ba tukunna, idan nace zan koma makaranta yanzu shigata makarantar zata iya janyoma wasu ɗaliban biyan bashin da basu sukaci ba, ni kuma sam banaso in zama silar da wani ze cutu." yana gama maganar ya kwanta  batareda ya ƙara cewa komai ba, sosai umma ta fahimci inda maganrsa ta dosa don haka itama bata ƙara magana ba taci gabada cin naman dake gabanta, kallon Umma zainab tayi kamar zatayi kuka tace "umma don Allah ki ƙara tsananta yiwa yaya Addu'a wllh inaji a jikina kamar wani abu mara daɗi yana shirin faruwa dash...." kuka ne ya taso mata lokaci guda kuma ta faɗa jikin Umma tana rera kukan,  Wajagal dake kwance saman shimfiɗanshi shiru yay bece komai ba amma har cikin ransa yakejin kukan ƙanwar tasa wadda duk duniya shi kaɗai ne gatan ta bayan ubangijin daya halicceta se kuma Umma.

Haka dai umma ta dinga lallaminta harta samu tai bacci a jikinta. Ita kuma ta afka cikin duniyar tunani da zancen zuci.

Nura na shiga tsakar gidan ya saka sakatar jikin ƙofar gidan nasu sannan ya dawo kusa da keken nasa ya ɗau ledar da Wajagal ya bashi wadda ke ɗauke da lafiyayyiyan gasashshen kazar yay ɗakin inno da sallama, a zaune ya samu inno tana cin tuwon shinkafa miyar taushe  Hajjo kuma na saman Gado se tura baki take wai ita bazata iya cin tuwo ba bakinta babu daɗi, kasancewar  sunada wutar nepa ne yasa hasken ƙwan lantarkin dake ɗakin ya game ko ina, jin Sallamar Nura Yasa Hajjo ta saki murmushi tace "yauwa yaya sannuda zuwa Allah dai yasa ka tahomin da soyayyen kifin dana ce?"  ta ƙare maganar tana tsareshi da manyan idanunta.

Be kulata ba ya tsallake ya zauna kusa da Inno wadda kecin tuwanta hankali kwance ya ajiye mata ledar a gabanta, kallonsa Inno tayi sannan ta kalli ledar tace "meye kuma wannan ɗin daka turo min gaba na?"  ajiyar zuciya nura ya saki yace "duba ki gani mana wllh ni kaina bansan meye a cikin ledar ba, Wajagal ne yace na kawowa Hajjo" ba iya hajjo ba ita kanta inno abin ya girgiza ta, daƙyar ta iya haɗiye lomar tuwon dake bakinta  sannan ta kai dubanta ga Hajjo wadda idanunta suka fito waje sabida mamakin abinda Nuran Ya faɗa, sakkowa tai daga saman Gadon a hankali ta zauna a ƙasa kusada inno batareda tayi magana ba.

Buɗe ledar inno tayi nanda nan ƙamshin Kazar ya bugi hancinan su,  washe baki Nura yay yace "kai Amma Allah ya sakama Wajagal da alkhairi wllh, kinsan Allah dama tun satin daya wuce nake son cin kaza se gashi Allah ya kawo mana ita ta hanyar mutumin da ban taɓa zato ba." ya ƙare maganar yana kai naman bakinsa.

Ita dai inno kallon naman kawai takeyi zuciyarta na aiyana mata wani abin daban  hakama Hajjo wadda tsoro ya fara shigar ta tace "inno kuma ci zamuyi?" tai maganar tana kallon Inno wadda itama ɗin kallonta take sannan ta ɗaga mata kai alamar Ae, ɗaya ledar ta buɗe Hollandia milk ce a ciki guda biyu masu ɗan iskan sanyi se kuma locuzad shima guda biyu masu Sanyi, murmushi inno tayi don babu shakka kam tasan sabida Hajjon yayi hakan Amma kuma a zahiri se tace "to Allah ya saka mishi da alkgairi ya kuma shiryar dashi bisa tafarkin Addini" da Amin suka amsa sannan inno ta rarraba musu tabama kowa nashi naman ragowar kuma ta Ajoyema Hajjo zuwa da safe,  a  Wannan daran Abubuwa biyu ne suka dinga yawo a zuciyar Hajjo tambayar datafi addabar zuciyarta itace "meyasa wajagal ya aiko mata da nama me yawa irin wannan bayan kuma basu da wta alaƙa da juna?" a haka dai taita faman juyi ba treda bacci ya ɗauke ta ba, se can wajen 1am na dare sannan ta samu matsaya a ranta wadda take ganin ita kaɗai ce mafita a gareta da kuma danginta gabaɗaya.

    ****

A wannan daran Sam Mano be iya Rintsawa ba sabida yanda jikin Ibrahim Buzu ya rikice, zuwa yanzu kam mano ya gama sarewa don haka ya fashe da kuka cikin Sujjadarsa cikin harshen france ya fara faɗin "ya ubangijin sammai bakwai ubangijij Al'arshi mai girma, ya Allah kaine mafi sani akan jarrabawar da kaiwa mahaifina Allah kaikaɗai kasan irin Azabar dayake ji a duk wata daƙiƙa ta Rayuwarsa, ya Ubngiji ka bamu mafita da waraka cikin hikimar ka da sassaucinka!!" a haka Mano ya kwana yana Abu ɗaya har lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallar farko na Asubahi, miƙewa yay zuwa gefan gadon ya kalli fuskar mahaifin nasu wadda ta faɗa sosai sabida halin jinya, Addu'a yay tai masa yana tofa mishi sannan ya fice zuwa masallacin dake cikin Hotel ɗin

Bayan ya idar ne ya zaro wayarsa ƙirar samsung yq shiga kiran wani abokinsa da suka zauna tare a jos tsahon shekaru 5, dama tun kafin ya baro joss ya kirashi kan cewar ya sama mishi gidan me kyau ze siya a nan cikin nasarawan.

Dailing number ɗin daya rubuta Nurudden a jiki yay , daga ɓangaren Nurudden yana ganin kiran Mano ya amsa tareda  faɗaɗa fuskarsa da  wani ƙayataccen Murmushi cikin harshen turanci yace "wlcm to Kano state Sulaiman Ibrahim Buzu" gajeran murmushi Mano ya saki tareda shafa baƙar ƙasumbar dake ƙarama kyakkyawan fuskarshi haiba yace "thank you Nurudden, I just call you to ask you about what we talk last 2weeks ago hop you remember" yay maganar yana korar murmushin dake saman fuskarsa gabaɗaya.

Daga ɓangaren Nurudden yay murmushi cikin harshen france yace " ban manta ba don har nasa an nemo maka kuma na tabbata idan kaga gidan zeyi daidai da ra'ayin ka." murmushi jin Daɗi Mano ya saki tareda cewa "thank you very Much Nuru i really appreciate this favour and I will never forget it in my life!." Nuru yay murmushi me sauti yace "you deserve it friend" kafin hanging call ɗin yay saurin cewa cikin harshen france "anjima by 11sekazo kai paying kuɗin gidan", cikeda jin daɗi Mano yace "insha Allah I will be come on time" sannan yay hanging call ɗin zuciyarsa fess da farin cikin samun gidan.

Tunda sanyin safiya Umma ta kammala dama musu kunun dazasu karya dashi, ragowar naman kazar da sukaci jiya ta ɗakko ta juyeshi a farantin silver sannan ta ɗebo ragowar dankalin turawar daya rage musu ta ferayeshi tsaf sannan ta wanke ta yayyanka manyan ta taceshi a kwando, duk abinda takeyi babu wanda ya fito sabida safiyace sosai, seda ta kammala jajjaga kayan miyanta tsaf sannan ta soyesu ta tsaida ruwanta, dankalin ta zuba ta rufe sannan ta fara gyara gurin

Ƙarfe bakwai dedai ta kammala dafa fatan dankalin dayay shar dashi a ido se baza uban ƙamshi yakeyi, wata ƙaramar kwanon silver ta ɗauka ta cika da fatan dankalin sannan ta ɗauka ta nufi ɗakin Atine dashi, a bakin ƙofar tai Sallama sannan ta shiga ɗakin  a zaune ta sameta tana karanta alqur'ani mai girma. Seda takai aya sannan ta ɗago da fara'a tana kallon umma tace "Hadiza kedai sam bakya gajiya da Hidima kokaɗan, jiya me sunan Ubana ya kawo min abin Arziƙi to ubangiji yay musu albarka ya kuma ƙara shirya mana zuriya gabaɗaya" da amin Umma ta amsa sannan ta miƙe tace "bari in koma ɗaki Baba" "to Hadiza Ngde sosai" fita umma tayi zuwa inda tukunyar Dankalin take, faranti Guda ta ɗauka ta zuba musu Abincin itada Wajagal faranti guda sannan ta zubawa zainan nata itama, ta ɗauka tai ciki dashi

A zaune ta sameshi harya tashi da brush a hannunsa, zainab dake tsaye tana matsa makilin a jikin brush ɗinta tana gamawa ta miƙa masa shima ya matsa sannan yay waje, kusan a tare suka gama goge bakin shida Zainab ɗin ɗakin ya shigo da sallama sannan ya gaida Umma ya zauna daga gefanta se faman murmushi yakeyi, kallonsa umma tayi itama ta i murmushin tace "Ibrahim duk wannan murmushin na fatan dankalin ne kenan?" ɗan waya manyan idanunsa yayi wanda suke kamada Umman sosai yace "hmmm bari kawai Umma wllh inason abin ne over"  a haka safiyar ranar ta kasance musu Cikin nishaɗi da kwanciyan hankali.

Se wajen 10 sannan yay wanka ya shirya cikin wata   brown ɗin jallabiya wadda ta baiyana lr da hasken fatarsa sosai, kansa sanye cikin farar hular tashi kafiye naci,  ya kalli umma daketa faman kallonsa harya gama sa hular yace "umma zan tafi gurin Mutumin jiya dayace na koma jiya" murmushi umma tayi sannan tace "to Ubangiji ya bada sa'a ibrahim Allah yasa kai katari da babban alkhairi musamman yanda kai kyau ɗinnan kamar bakai ba" dariya yay har seda kumatunsa duka suka lotsa yace "Amin Umma na" yay maganar yana fita daga ɗakin, Da kallo Sahura ta bishi hakama Bintalo da Abuwa dukkansu baki buɗe

Wllh in banda sunsan tafiyarsa sosai sesu rantse ba Wajagal bane sabida wani maifan  kyau da sukaga ya musu kaman ba shi ba.

A kwarin zage ya samu Ɗan-adaidaita sahu ya hau tareda gayamasa inda ze kaishi, shiga yay ya zauna sannan me mashin ɗin yaja suka tafi se faman kare Fuskarsa yake sabida kar ƴan Daban  ƙofar wamban su shaidashi, sabida sam yau be shiryawa hakan ba sam bayason duk wani abinda ze zama katanga a gareshi ga cimma muradinsa ko kaɗan..............


Comment
And
Share

Chubaɗo✍️


MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now