EPISODE 3

9 1 0
                                    


MAGANA TA ƘARE
true life story

Mallakar: chubaɗo✍️

Banyi editing ba 🙅‍♀️

03

___✍️Wannan shine kuskure mafi girma data aikata a rayiwarta na Taimakon Wajagal, jawota Nura yayi lokaci guda kuma ya wanka mata wani lafiyayyen mari yace "shikenan gashinan kinjanyo mana bala'i Hajjo taya kike tunanin zamu iya tserewa waƴan nan gungun ƴan daban?" Fashewa tayi da wani irin kuka sannan ta kalleshi jikinta na wani irin Rawa tace "yaya na shiga uku yanzu ya zanyi kenan ? Wllh nasan idan suka kamani kasheni kawai zasuyi!!!" Zarya Nura ya farayi zuciyarsa kamar zata faso qirjinsa sabida tsoro

Buga ƙofar gidan suka shigari inda wasunsu kuma ke karta makamansu a jikin dandamalin simintin dake ƙofar gidan, ganin da sukia wankin hula na ƙoƙarin kaisu ga dare ne yasa Suka shiga ƙoƙarin ɓalle ƙofar daga Nura har Hajjo jikinsu rawa yake sabida tsabar tsoro batama san ta saki fitsari ba, da gudu Hajjo ta shiga Ɗakinsu tareda bushe fitilar ƙwan da Innarta ta kunna sannan ta nemi lingun gadon ƙarfamsu ta shige tana maida numfashi

Hayaniya ce ta kaure kafin kace me Samba da Ɗan-calangi sun kwaso zugar su don kawoma Wajagal ɗauki, nanfa aka kacame tsakanin ƴan-Daban ƙofar wambai da kuma na Unguwar Zage ganin da sukai bazasuyi riba bane yasa suka gudu se'a lokacin suka ankara da babu Wajagal a gurin nanfa gabaɗayansu hankalinsu yay mugun tashi, Ɗan-calangi ne ya kalli sauran yace "nifa ina tunanin wancan gidan ya shiga shiyasa harsu Tagarai suke ƙoƙarin ɓalla ƙofa, kawai musa kai mu duba" Samba ne ya shiga gidan yana ƙwala masa kira amma kuma ɗib babu motsin kowa, wata cocilan ya zaro daga aljihun gajeran wandonsa me bala'in haske ya kunna

Idansa ne ya sauka akan Nura wanda ya tura kansa cikin tukwanan dake jere a kicin ɗinsu, takawa yay har inda yake sannan ya dafashi wata Uwar ƙara ya saki tareda faɗin "don Manzon Allah kuyi haƙuri wllh bani bane Hajjo ce ta ɓoyeshi!" ya faɗi hakan jikinsa na ɓari kamar mazari. Fizgoshi yayi zuwa waje tareda haske masa idanu da fitilar dake hannunsa yace "dilla wace wata Hajjo? Zaka fito da itane kosena tsarge ma ciki da wuƙa?" da sauri ya miƙe dukya gama kiɗimewa ya shiga ɗakin yana ƙwalawa Hajjo wadda ke maƙale a bayan gado kira, tana jinsa amma taƙi fitowa sanadin hargowar kiran dayake mata ne ya farkar da Inno daga nannauyan baccin daya ɗauketa, yatsina Fuska tayi tareda zaro ƙaramar cocilan ɗinta datake ɓoyewa a ƙasan filo ta kunna cikeda faɗa ta kalli Nura tace "Nura me kake har yanzu baka kwanta ba da tsohon daran nan?" kallonta kawai yake amma ya kasa magana sabida tsabar yanda yake a tsorace, ba abinda ke karyo masa illa gumi hakan yasa Inno ta tashi daga kwancen datake ta tsira masa ido tace " lafiya kuwa Nura ina hajjo take?" hajjo wadda ke maƙale a bayan gado se'a lokacin ta fito, janta Nura ya farayi tana tirjewa batareda ya bawa inno Amsa ba yay waje yana zuwa ya hankaɗo ta gaba yace "itace ta ɓoyeshi ku tambayeta tasan komai" Fashewa da kuka Hajjo tayi tareda durƙusawa a kan ƙafafuwanta jikinta se ɓari yake tace "wllh bansan komai ba nifa kawai tausayinsa naji shiyasa nayi hakan amma don Allah kuyi haƙuri wll....... "Dalla rufe mana baki muje ki nuna mana inda yake!" Samba yadaka mata wata uwar tsawa wadda tasa Inno dake ɗaki ta fito a kiɗime da ƴar cocilan ɗinta a hannu.

Tsayawa tayi a baki ƙofa tareda dafe ƙirji tace "innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!" da sauri ta koma ɗaki ta ɗakko zani ta nufi inda Hajjo ke tsugune tana kuka ta miƙa mata tace "haba bayin Allah meya kawoku gidan Mu da wannan daren sabida Allah? Sannan kuma me ƴata tai muku dazaku sata gaba a irin wannan halin tana Mace?" rasa wanda ze bata amsa akai a cikinsu illa kallonta kawai da sukeyi tamkar waƴanda suka warke makanta, ɗago Hajjo dake kuka tayi tace "Hajjo meya haɗaki da waƴannan bayin Allah?" tsagaita kukan datakeyi Hajjo tayi sannan ta kalli Inno tace "damafa uhmm Wajagal ne na gani ya baɗi dabda bakin bola, wasu zugar ƴan-daba sun taho daga hanyar ƙofar wambai suna nemansa zasu kasheshi shine fa na kwance zani na na rufa masa kuma na juye masa bolar gidan nan akansa, to Ashe waƴannan sun ganni shine sukazo kamani!!" Hajjo ta faɗi hakan tana rushewa da kuka.

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now