EPISODE 5

23 2 0
                                    

MAGANA TA ƘARE
     true life story

Mallakar: chubaɗo✍️

           05

___Ƙanƙame jikinta tai guri ɗaya idaunta na siyayar da hawaye, cikin kakkausar muryarsa me ɗauke da Amo a cikinta yace "ke wa kikewa dariya ɗazu?" Ya ƙare maganar yana kafeta da rikitattun idanunsa da har wani limshewa suke kamar mejin bacci, numfashi ta fara saukewa akai-akai tamkar wadda ke shirin shiɗewa tace "nifa bakai nakema dariya ba wllh, damafa uhmm wannan me awarar Ummi ce take bani wani labari  shiyasa ni kuma na kalleka nayi dariya" ta ƙare maganar tana ƙara fashe masa da kuka marar Sauti se faman Ambaliyar hawaye take.

Kallonta kawai yake se faman yarfe hannu take kamar wadda aka zane sannan ya wani taɓe baki yace "Wllh idan baki dena kukan nan kin mini bayani ba sena Bajeki a  nan gurin." yay maganar yana ƙara tsareta da idanunsa da suka ƙara saukar mata da tsoransa, hannunta tasa duka biyu ta rufe bakinta still jikinta na rawa kallonta kawai yakeyi from head to toe cikeda ƙosawa Samba ne ya ƙaraso gurin yana jan Sigari yace "ya akai ne oga na ganka a nan?" yayi maganar  yana leƙa fuskar Hajjo wadda duk tabi ta tsure sabida tsoron Wajagal ɗin.

Jan sigarinsa kawai yaci gaba dayi ita kuma Hajjo daƙyar ta iya saita kanta tace "nifa wllh ba ruwana, wllh ummi ce ta gayamin wai tayi mafarki dakai kuna soyayya wai bakason ɓacin ranta itama bata son naka, tofa shine abin ya bani dariya kawai seka taho kai kuma." Hajjo tai maganar tana kallonsa, wani ƙayataccen murmushi ne yay escaping lips ɗinshi wanda shi kansa besan a lokacin da murmushin ya wanzu kan fuskar tasa ba, tsabar yanda maganar nata ya bashi dariya  dukda yanda fuskarta ya caɓe da hawaye sam hakan be hanata zaro manyan fararen idanunta ba sabida mamakin ganin yayi murmushi, washe ƙananun Haƙoranta tayi tana dariya ba tareda ta goge hawayen daya caɓe mata fuska ba tace "Lah dama kanada wannan abun kalan nawa?" Tai maganar tana ƙoƙarin kai hannunta gefan fuskarsa inda beuty point ɗinsa daya lotsa sosai sanadin Murmushin dayayi,  wani kallo ya watsa mata ba shiri tai saurin sauke hannunta ƙasa ta fara murza hannun jakarta, juyawa yay batareda ya ƙara ce mata ƙala ba yay gaba binsa  juyawa tayi tareda gyara zaman farin ɗan-madinan dake afarta sannan ta ɗaga muryarta sosai  ta yanda zeji ta tace "kanayin kyau sosai idan kayi murmushi, dama zaka dinga ƙawata fuskarka dashi tabbas da kaf Unguwar zage babu wanda ze ƙara kallonka da fuskar wajagal, sabida sam batai maka kyau ko kaɗan!" ta ƙare maganar tana falfalawa da wani uban gudu tayi gida, dagashi har Samba dariya sukayi abinda wajagal be taɓayi ga wani ba indai ba ummansa ko ƙanwarsa zainab ba.

Kallonsa Samba yayi yace "oga wannan fa itace yarinyar dana baka labari kwanaki wadda ta kaimaka ɗauki ranar da aka samu ɓacin Ranar nan, ɗan taɓe baki yayi tareda jefa tabar wiwinsa a baki ya kunna yana busa hayaƙi yace "tome zan mata inma itance ?" yay tambayar yana kallonsa, basarwa Samba yay sukai gaba Karnukansa na take masa baya.

             **

Juyi kawai take a saman Gadon gabaki ɗaya duniyar jinta take duk babu daɗi, a hankali ta miƙe jiki babu ƙwari ta isa ƙofar toilet ɗinta aɗan hanzarce ta ƙarasa jiki kafin kace me ta fara kwarara uban Amai, tun tana iya tsaiwa akan ƙafarta har hakan ya fara gagaranta ko gurin bata iya gyrawa ba ta lallaɓa ta fito daga Banɗakin tana fitarda nishin Wahala, Momy ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da trey wanda aka jera bread da duk wasu nau'ikan abubuwan haɗa tea irin na gidan ƴan gayu ajiyewa tai da sauri sannan ta nufi inda Zahra ke kwance duk ta galabaita

Kuka momy tasa a lokacin data isa ga ɗiyar tata taga kamar bata numfashi, da sauri ta sungumeta kasancewar ba wani nauyin kirki gareta ba tai waje da ita ko mayafi babu, motar dake fake a farfajiyan gida ta buɗe  sannan ta shimfiɗeta a bayan motar ta koma cikin gidan da gudu, mukullin motar ta ɗakko tareda wayarta tai saurin shiga tama Motan key se Asibitin Murtala  cikin sa'a kuwa tana isa aka kawo musu ɗaukin gaggawa kasancewar Emergency ne, bayan an shiga da ita wayarta ta lalubo ta shiga kiran Mahaifin Zahra wato Alhaji Tajo seda ta kira kusan so 3 sannan ya ɗaga, ƙara fashe masa tai da kuka nan ta fara zaiyana masa duk abinda ke Faruwa.

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now