EPISODE 8

10 1 0
                                    

MAGANA TA ƘARE...!!

    True life story

             08

Banyi editing ba🙅‍♀️

___Koda inno ta shiga ɗakin seta samu kanta da tausayawa Rayuwar da Wajagal ɗin ya samu kansa a ciki, haka nan kuma setaji zuciyarta gabaɗaya ta gama karkata ga sanin dalilin daya jefashi cikin wannan hali marar amfani Wanda idan yazo masa da sanadi tsaf ze iya rasa Rayuwarsa ta wannan hanyar.

Wani dogon Fasali ta sauke tareda maida kallonta ga Hajjo wadda ke sauke numfashin wahala, batareda ta ankare ba sejin wata siririyar ƙwallah Tayi tanabin gefan fuskarta wadda takeda tabbacin cewar na tausayin mahaifiyar Wajagal  ne, zuwa yanzu zata iya kwatanta Irin  ciwon da ko wace uwa takeji  Da zarar Rayuwar ɗanta ta samu tawaya, koda ƴaƴa dubu Mace ta tsuguna ta haifa bazata so ace yau ga gudaɗaya daga cikin ƴaƴan ya samu tawaya ta Ɓangareɓ ɗabi'a ba, zatafi so a ranta cewar dukkan  gabaɗaya su su zama mutanan kirki Kuka abin Alfahari ga kowa.

Kallonta ta kuma mayarwa Ga Hajjo wadda ta juya kanta gefe  guda sannan tai murmushi tace "ubangiji kai kaɗai ne gatan kowa, ya Allah ka shirya mana zuri'a don Arziƙin mahaifin Nana" ta shafa addu'ar tana ficewa daga ɗakin don ta ƙarasa gyaran gidan datakeyi sabida ta tsani ƙazanta a Rayuwarta.

           **

Ɓan garen Zahra kuwa cikin ikon Allah ta fara jin sauƙin jikinta sedao har lokacin bata ƙara cewa mahaifiyarta komai akan abin ƙaunar nata ba, sedai a wannan karon ta gama ƙudurtawa kanta cewar da kanta zatai yaƙin samo soyayyar wanda takeji a ranta cewar shine cikamakin Rayuwar ta.  Seda ta shafe wata 2 cif tana jinya sannan aka sallamesu zuwa gida duk tabi ta rame se uban dogon hanci da idanu kawai a farar fuskarta, Dadynta ne ya ɗakkosu da kanshi se faman lallaɓata yake kamar kwai dama can zahra shalelen Abbanta ce balle kuma yanzu da yake ganin yana dabda ya rasata  sabida ciwon zuciyan daya mata sallama tunda ƙuruciyan ta, wannan dalilin yasa yakejin tausayin yarinyar sosai a ransa hakakuma duk wani motsi nata seya jishi har cikin ransa, Allah-Allah yake su ƙarasa gida ya zauna da Zahra yaji menene matsalar ta da har take ƙoƙarin Rasa ranta akan ta!!!

***

NIGER 🇳🇪

Tun da sanyi Safiya Abdul ya gama kammala shirinsa shida matarsa Samirah sannan ya ɗaga waya ya kira Abdulrahman wanda yake binsa yace Shima ya shirya akwai inda yakeso suje, ba musu shima ya shirya Tsaf kamar yanda yanda Abdul ɗin ya buƙata matarsa Su'adatu ya kalla yace "ki shirya  Sadiq Sannan kisa  Araifah Itama ta shiyar nasanta da shegen nauyin shiri kamar wata babbar mace, se kije part ɗin Aunty Maryamu kice ta shiya da ita da Aman zamuje Nigeria." batareda ta kalleshi ba ta miƙe zuwa aiken daya mata , a Zaune ta Samu Aunty Maryam a katafaren Falonta na alfarma Aman ya ɗora kansa a saman cinyarta ya lumshe manyan idanunsa  Kamar me bacci, Sallamar datai ne yaja hankalinsu gabaɗaya zuwa gareta

Hararan Aman tayi cikin sigar wasa tace "wai kai bakasan ka wuce wannan minzalin bane? Don Allah jibeka fa duk ka wani danne mata ƙafa kaman wani yaro" murmushi Aman yayi cikin salonsa irin na Mahaifinsa wato miskilanci yace " Aunty Sa'ada Har yanzu I'm still a baby" yay maganar yana kallon Mahaifiyarsa wadda keta faman murmushi tana jinsu.  A kowani lokaci ta ɗaga kanta ta kalli Aman Mano ne kawai yake faɗo mata a rai, tund Tana ɗauke da tsohon cikin Aman Mano Yay bar ƙasarsa ta haihuwa shida Mahaifinsa ba tareda kowa ya sani ba In banda saƙonsa data gani a rubuce da tuni ta ɗauki haƙƙi Wasu ta hanyar cewa Kurciya aka masa.

Batareda ta sani ba tuni hawaye sun fara wanke mata fuska A sanadin begen mijinta abin ƙauna a gareta, da sauri tasa hannunta ta Share hawayen tana shafa fuskar Aman wanda ya kafeta da fararen idanunsa, a gefanta Aunty Sa'ada ta zauna fuskarta ɗaukeda Alhini tace "nasan Dalilin zubar hawayenki Aunty Maryam don haka sam be kamata in dakatar dake ba, wani abun zafinsa baya taɓa gushewa indai ba hawaye muka zubar ba"  hannunta ta kamo cikin nata sannan Ta saƙi wani ƙayataccen murmushi tace "inada Labari me daɗi a gareki wanda nakeda tabbacin sekinfi kowa farin ciki dajin sa" ƙuri Aunty maryam tai mata da idanu batareda tayi magana ba.

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now