EPISODE 7

6 3 0
                                    

MAGANA TA ƘARE...!
  
   True life story

Mallakar: Chubaɗo✍️

             07

Banyi Editing ba🙅‍♀️

____Ba ƙaramar girgiza Momy tayi ba dajin wanda ɗiyar nata kewa mahaukacin so, wani uban dogon Fasali taja wanda ya haifar mata da sauke wata nannauyar Ajiyar zuciya sannan tace "Haƙiƙa al'amarin da kika ɗaukoma kanki me girma ne Zahra, Amma inaso ki sani cewar abu ne mawuyaci mahaifinki ya amince da wannan al'amarin naki domin kuwa dedai yake da kin ɗakkoma kanki Dala babu gammo."  ta ƙare maganar cikin yanayin tsare gida

Murmushi kawai Zahra tayi bata ƙara cewa komai ba ta maida bayanta jikin filo tareda kwantar da kanta, ta jima idanunta a lumshe sannan ta buɗesu a hankali akan mahaifiyar nata tace "Momy babu abinda ya gagaru Ubangiji a rayuwa, haka kuma duk wanda ya dogara a gareshi babu shakka shiɗin ya isar masa  bazan ce komai ba akan jarrabawar da Mahaliccina ya min  ba, domin kuwa  nasan MAGANA TA  ƘARE!!!."  zahra ta ƙare maganar tana me gyara kwanciyarta sosai a saman Gadon se faman cije baki takeyi.   Kallonta kawai Momy keyi zuciyarta na wani irin Bugawa da mugun ƙarfi, fatanta ɗaya ne Allah ya canzawa Ƴarta ra'ayi akan wannan yaron sabida sam basu dace da juna ba. In bnda al'amari na ƙaddara ina zahra ina faɗawa son yaron daya gagari kowa?   Tabbas dole ne su ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan shasha-shar buƙatar ta Zahra!!!

         ****
PLATEAU STATE (Jos)

Ammi ce zaune hannunta ɗauke da wayarta ƙirar Samsung, ɗan danne-danne tayi kaɗan sannan ta kara a kunnanta tareda ƙudurtama zuciyarta cewar yau ɗin nan base anjima ba zata kira Abdulsamad da Abdulrahman  suzo nigeria suga Halinda Mahaifinsu ke ciki, koda kuwa hakan yana nufin samun matsalarya da Mano ne. Abdul dake kwance Saman makeken Gadon dake ɗakin baccinsu matarsa Samirah na kwance saman ƙirjinsa tana wasa da sumar dataima faffaɗan ƙirjinsa ƙawanya suka jiyo ƙarar Wayarshi dake ajiye saman bedsit drower, Siririn tsaki yaja wanda tareda janyo Samirah jikinsa yay hugging ɗinta sosai kamar ze shige jikinta kallonta yay a kasalance cikin harshen faransanci yace "har zuwa shekaru nawa Yaya Mano ze ɗauka yana gina katanga a tsakanin mu da Mahaifin mu?" yay maganar aɗan zafafe sabida dama Abdul badai zuciya ba, sassauta Muryarta Samirah tayi cikin sigar Rarrashi tace "kayi Haƙuri Abou Aisha na tabbata haka kawai yaya Mano baze taɓa aikata hakan da mummunar manufa fa, yaufa kimanin tsahon shekaru kenan Rabonsa da ƙasarsa ta haihuwa  haka duk bama wannan ba ka duba irin Sonda yakewa Aunty Maryam amma sam hakan be hanashi  tsallake ta ya barta da tsohon cikin ɗansa ba haihuwa ko yau ko gobe, ni ina ganin dole Yaya manu yanada dalilinsa na gina wannan babban shamakin a tsakaninsa daku da kuma matar dayafi ƙauna a Rayuwarsa idan ka cire mahaifiyarku."  samirah ta ƙare maganar tana kallon Idanun mijin nata daya fara sauya launi sabida kewar Mahaifinsu Wato Alhaji Ibrahim Buzu. Iska me zafi ya firzar daga bakinsa sannan ya ƙara janyota zuwa jikinsa yace " nafi kowa Sanin Halaiyar ɗan uwana Mano  amma kuma se gashi akan wannan al'amarin sam na kasa fahimtarsa." yay maganar Hawaye na zubowa daga cikin fararen idanunsa masu haske, ƙara riƙeshi tayi itama idanunta nakansa tace " ina ganin a kan wannan murɗaɗɗen al'amarin ƙarfin addu'a ne kawai ze warware mana komai."  ɗaga mata kai yayi Alamar gamsuwa da bayaninta yace "ubangiji yay miki Albarka Samirah" da Amin kawai ta Amsa masa tareda ƙara lafewa a cikin jikinsa tana me ƙara Tausaya musu bisa halinda suka samu kansu a ciki.

Ƙarar wayanshi ce ta fara tashi a karona biyu, ɗan ɗaga kansa yay kaɗan yace "
ɗakko min wayana pls" miƙewa Samirah tai a nitse ta ɗakko mishi wayan tareda miƙa masa.

Ɗan buɗa manyan idanunsa yay a lokacin dayay arba da sunan Ammi dake yawo bisa saman screen ɗin wayar, damuwan dake kwance saman fuskarsa ce ta ƙara yawaita fiyeda ta farko cikin nitsuwa da farin ciki ya ɗaga wayar tareda karata  jikin kunnansa

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now