Babi Na Uku

4.7K 334 48
                                    

“Assalamu Alaikum.”
Sassanyar murya game da mutumin da ya shiga falon suka zuciyr ta sandarewa. Dogon mutum ne, ya na da haske amma ba can ba. Ya na sanye cikin kwat baki da farar shat a ciki. Kamshin turaren sa ya naushi hancin ta, a yayin da hadiye yawun da ke bakin ta, wanda ba ta san da shi ba.

Yanzu ne ta ke ganin dalilin da ya sa Mariya fada wa kogin son sa, har ma da na yarda da shi kamar yadda ta yi.

Ya dace da mafarkin ‘yan mata. Ko da ya saki murmushi, za ta iya rantsewa zai iya narka dutse ya zama gari. Duk da cewa ma ba wa ita yayi ba.

Bayan ya gai da Ummar sa, sai ta gabatar ma sa dalilin kiran da ta yi ma sa. Ya mayar da hankalin sa kan Asiya. Ba tare da bata lokaci ba, ya tambaye ta dalilin neman ganin sa.

Makogwaron ta ya bushe, sannan ta gyada kanta, ta kuma girgiza a lokaci guda. Ba ta san dalilin rudewar da tayi ba. Watakila ko don Umma ta na zaune ne a wajen. Ko kuma don wannan ne karo na farko da take fuskantar sa.

Ya zauna kan kujerar da ke fuskantar ta, kamar yadda Ummarsa tayi zato ne, shi ma hakan yayi, “Ke ce marar lafiyar ko wani?”

Muryar sa cikin natsuwa, wanda wata kila likitoci ke amfani da su wajen jan hankalin marasa lafiya. Ko kuma wanda mayaudari ke amfani da ita wajen jan hankalin ‘yan mata masu rauni, irin su Mariya.

Nan take ta ji bacin ran da yake ran ta ya taso. Mariya! Mariya!! Ta amsa da, “Na bar wacce ke da matsalar a can gida. Na zo ganin ka ne dangane da matsalar ta.”

Kallo ya ma ta, irin na marasa tunani, kauyawan nan. Ya ce, “I am sorry, ki gafarce ni, ba zan iya yi mi ki komai a kai ba muddin babu marar lafiyar. Baya ga haka, ni ba wata mu’ujiza ce gare ni da zan warkar da marar lafiya ba tare da ganin ta ba. Don haka idan kin shirya sai ki kai ta can asibiti ku same ni. Don ban cika son a na zuwa gida a kawo hidimar asibiti ba. Yau don albarkacin Umma ne ya sa na saurare ki.”

Iye! Ga mutum da gadara da ji ji da kan tsiya. Ya kuwa san da wacce ya ke magana? Har ya mike zai bar wajen, irin ya gama yanke hukunci din nan, ta tsayar da shi, “Na zo ne don na yi ma ka bayanin halin da Mariya ta shiga ciki.”

Ya kalle ta, “Mariya?”

Haushin sa ya kara kama ta. Ya ma ta tambaya kamar bai san Mariya ba? Dan rainin hankali kai. Ta yanke shawarar yi ma sa bayani dalla-dalla. Tun da abin da ya ke so ke nan.

“Eh, Mariya. Wacce ka jefa cikin halin da ke neman jefa gidan mu cikin jafa’i.”

Idanun ta suka ciko da kwalla, zuciyar ta ta fara ci da wuta don jin zafin halin da suka tsinci kan su. Shi waye ne da zai jefa su cikin ukuba da tashin hankali, alhali shi kuma ya zauna cikin sukuni? Wannan ai zalunci ne da son kai.

“Wace ce Mariya?” Ya kara tambayar, muryar sa ta na nuna rashin fahimtar sa karara.

Cikin gifcewar dakika daya, Asiya za ta iya yardar cewa wannan likitan bai san Mariya ba da gaske. Amma kuma hakan salon ‘yan yaudara ya ke. Kamar sari-kutuf ne, su sare mutum su noke. Balle ma ya na gaban mahaifiyar sa ne, tilas zai yi taka-tsan-tsan.

“Mariya Sabo Ali. Har ka mance da ita? Ko da yake ba abin mamaki ba ne. Mutum irin ka zai dauke ta tamkar tsummar goge takalmi, ka yaudare ta ka jefar. Amma na sha alwashin cewa ba zan kyale ka ka huta ko ka kasance cikin sukuni ba har sai na samar ma ta adalci daga gare ka.”

Har wani haki take yi, tsabar takaici ya rufe mata ido. Ba ta ko iya ganin girman mahaifiyar sa balle ta yi ma sa sassauci. Musamman ta fito domin sa, ta kuma samu damar fuskantar sa tare da fada ma sa abin da yayi mu su. Ba ta san abin da zai iya yi ma ta ba, tun da mai dukiya ne. Ba ta damu ba kuma.

Nan ta ga ya tsuke fuska, kyaun fuskar sa bai gushe ba. Ya kalle ta da kyau, “Who are you? Ke wace ce? Daga ina ki ka zo haka har za ki nemi yi min isgili a cikin gidana?”

KudiriWhere stories live. Discover now