Babi Na Sha Uku

4.7K 384 63
                                    

Assalamu alaikum. Thank you for being patient with me. Sorry for the delay, it wasn't intentional.  Weekends are normally busiest for me. Bit thanks for your support and keep the votes coming and the comments flowing. 😘😘




“Ya ya kika ganni?”
Asiya ta daga kan juz’i Amman da take karantawa ta kalli Muhibbat daga sama zuwa kasa, sannan kasan zuwa sama. Ta cancada kwalliya, ta saka leshi mai launin tsanwa mai ratsin ruwan gwal. Kamar kullum, dinkin ya karbeta zanzan don Allah Ya yi mata baiwar kyaun sura da diri. Kitson da tayi sun kwanta daidai kafadunta, gami da daurin dankwalin ‘maintain’ a kan su.

“Kin yi kyau, sai ka ce wata amarya.” Asiya ta furta cikin murmushi. Da gaske ne ta yi kyau. Don ta na da aji, duk da a kauye suke. Idan Muhi ta yi kwalliya ta yi dauri, ba kowane namiji ba ne ya kan tunkare ta. Sai irin wanda ya yarda da kan sa sosai.

Muhibbat ta bata fuskarta, “Ke kuma dube ki, kamar ba amarya ba.”

Asiya ta kalli kan ta. Duk da cewa ba ta yi kwalliyar amaren bana ba, ba za a ce ta yi rashin kyau ba.  Atamfa ta saka mai dinkin loose-fitted, launin shudi a gauraye da ruwan kasa da ja. Sabon dinki ne da Umma ta aika mata a cikin wannan satin, don kasancewar ta amarya. A cewar ta, ta san lokacin yin shirye-shirye ya kure musu baki daya, don haka ta aika mata dinkuna uku kala kala.

“Ai baki isa ba. Ko da cewa daga kauye mu ke, ba za mu nuna karanta ba.” Muhibbat ta fice ta bar Asiya ta na murmushi.

Muhibbat kawar Maree ce, kuma a kalla ta ba wa Asiya shekara biyu a haife. Amma jinin kawancen su ya fi karfi saboda yadda Muhibbat ta fi Maree jan ta a jiki. Sau da dama, kowa kan dauka Asiya ce kawar Muhibbat, ba Maree ba.

Jim kadan Muhibbat ta koma dakin, tana rike da yadin material mai launin ja da ruwan gwal, sai sheki yake. Ga shi da sulbi kamar siliki. Dinkin riga da siket ne mai shef na yayi.

“Ga wannan. Tashi ki saka yanzu. Na fi son idan mijin ki ya shigo ya ga kin gwangwaje ma sa.”

Kalmar ‘miji’ ta kara sa zuciyar ta tsalle, kamar yadda ta yi a dazu bayan sun karya da soyayyen dankali da miyar hanta da koda hade ruwan shayi mai kauri.

A wancan lokacin Sara ce ta sanar mu su cewa Yusuf ya na tafe da abokan sa. Gwaggo Tambai an mayar da su Dagauda. Ta roki Muhibbat ta zauna ne don ta samu kwarin gwiwar fuskantar sa.

“Atamfar ta fi kyau Muhi.”

“Kin fara ko? Tashi ki je, don kin san ba kyale ki zan yi ba har sai kin canja.”

A dolen ta ta shiga bandaki ta canja, don ta san Muhibbat za ta tara mata jama’a idan ta cije. Ko da ta koma, ta samu tana jiranta da kayan kwalliya. Rabon ta da shafa hoda a fuskar ta har ta manta. Watakila tun zuwan ta Bauchi na farko.

Tun can da ma Maree ce mai damuwa da kwalliya. Idan ta sayi kayan kwalliyar sai ta boye ta hana ta. Wasu lokuta Asiya ta kan sayi nata, amma ko Maree ta shafe su kare da wuri, ko ma ta je ta zuba cikin salga a boye. Idan fa har Muhibbat ta dage kan sai ta yi kwalliya, Maree kan kushe ta, ta nun aba ta yi kyau ko fasali ba sam.

“Kin hadu fa Minde. Yanzu kika fara kama da amarya.” Muhibbat ta furta. “Zo nan ki zauna don sai na sumar da angon ki yau idan ya kalle ki.”

Abin ya so ya bata dariya, amma sai ta ga ba amfanin sace gwiwa wa wanda ke mafarki irin na Muhibbat. Don haka ta zauna ta ba da fuskar ta.

Wani abin ma ba ta san sunan sa ba, amma an mulka ma ta. Ta na gamawa ta ce da Asiya, “Yauwa, nan ya kammala, yanzu tashi za ki yi don na ga yadda za ki yi tafiya idan ya shigo?”

Asiya ta tura bakin ta tare da harara, “Ni yarinya ce a ka gaya miki?”

“Ke din ce ai. Na ga sai na dage a kan ki.”
Tun daren jiya ta ishe ta da ta yi wannan ta yi wancan. Kunnuwan ta sun gaji da ji. “Muhi, wani abin sirri ne, sai tsakanina da shi zan yi shi.”

KudiriWhere stories live. Discover now